Sashe 37
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
ne" ta juyo a fusace tana maka masa harara tace "yo ko bai yafe bama ai dole ya yafe,tunda dai ba zai yanki namana a matsayin kud'insa ba ko?" Hannunsa ya wanke ya fito da ruwa a hannunsa na roba,sanda ya koma ya zauna yana bud'e ruwan yace "kyaleta dan ta samu na ce na yafe mata ne,sai ma nace na fasa sai kin biya ni" mik'ewa tayi da sauri ta kama waistband tace "yo Allah na tuba sai dai mu dambatu mai k'arfi ya k'wata" yayi murmushin da ya bayyana hak'oransa yace "yanzu ko cewa aka yi ni dake muyi dambe,ai kya gudu kice a'a" tace "Iiiiiihhh! Saboda me?" Yace "haba Hjy ki kalle ni fa,ko wani namijin zai ji tsoron mu had'a jiki bare ke" harararsa tayi tace "ehh! Namijin ma sai dai idan sauna ne zai k'i" dariya sosai Amaar ya dunga Ameerah tana tayasa,Dadda ta wuce kitchen tana mita,Waleed yayi murmushi ya kalli Ameerah yana d'aure fuska yace "ke je ki d'auke wancan kayan" da sauri ta shiga taitayinta ta tashi ta d'auke plate d'in,ta kai hannu za ta d'auki robar ice creams d'in yace "banda wannan" ta wuce kitchen ta kai,da ta dawo ta wuce hanyar d'aki because ta san zama kusa da shi baka isa kayi kwakwkwaran motsi ba yanzun nan sai rai yazo yana b'aci,har ta kai kusa da k'ofa yace "su wannan d'in kina jira sai na ce ki d'auke?" Ta dawo da sauri ta d'auka a hankali gabanta yana fad'uwa tsabar tsoronsa tace "Yaya ina zan kai maka?" Wani kallo ya maka mata yace "kin tab'a ganin ina shan ice cream?" Ta girgiza kai da sauri yace "kin b'ace min daga gani ko sai na zane ki?" Da sauri ta wuce za ta sa a fridge ya mata tsawa yace "idan kika bari na ganshi da safe jikinki sai ya fada miki" cak ta tsaya idanunta suna kawo ruwan hawaye ta juya tana kallonsa tace "Yaya to ni ban san na waye ba" ya maka mata harara yace "ki jira na fad'a miki" daga haka ya d'auke kai ya ci gaba da kallon sport da ake haskawa,tsaiwa tayi a gurin ta kasa tafiya sai da ya d'ago ya kalleta ta shige d'aki da sauri,ta tarar da Manar a kwance ta k'arasa tana sauke ajiyar zuciya tace "shi wallahi Yayan nan ya cika takura" Manar tayi dariya tace "ki fad'a ya ji" a tsorace ta zaro idanu tace "Tabbb' so kike ya karairaya ni?" Tace "ashe kina tsoron yaji?" Zama Ameerah tayi kusa da ita tace "ga shi" Manar tayi saurin kallonta tace "mene ne?" Ameerah tace "ice cream" saurin tashi tayi ta zauna,ta d'auki d'aya ta bud'e Ameerah ma ta d'auki d'ayan suka fara sha suna hira. Ranar monday 7am ya shigo part d'in cikin k'ananun k'aya da suka amshesa yayi sallama,a zaune yaga Dadda kan darduma tana gyangyad'i bai yi magana ba ya kalleta ya wuce hanyar bedroom,ya tura k'ofar ya shiga,ya hangota kwance a saman gado tana bacci ya k'arasa ya kai hannunsa ya yaye duvet d'in da ta rufa,tayi juyi ta kai hannunta tana laluben bargon,ya tsaya ya zuba mata ido sanda taji ta kasa kamo bargon ta bud'e idanunta a hankali,a kansa idanunta suka sauka tayi sauri ta tashi ta zauna tana murza idanunta,ya maka mata mugun kallo yace "get up Malama ki shirya kada ki b'atan lokaci" ta dunga kallonsa kafin ta daure tace "ina za mu Yaya?" Yace "ban sani ba" ya juya zai fita,har ya kai bakin k'ofa yace "mintuna goma ki shirya ki fito ina jiranki a parlor" ta zumb'uro masa baki tana k'unk'uni,ya juya yace "me kika ce?" Da sauri ta sauka daga gadon ta wuce bathroom tace "nifa ban ce komai ba" ya gyad'a kai ya koma parlor ya zauna,kusan mintinsa biyar a gurin yana danna wayarsa yaga Dadda ba ta da niyyar kwanciya,yayi murmushi ya tashi ya matsa kusa da ita,shoulders d'inta ya kama zai kwantar da ita ta bud'e idanu a firgice suka had'a ido dashi tace "A'uzhubillahi minashshaid'anir rajiim" wani kallo ya mata ya saketa ya koma inda ya taso,ta gyara zamanta tana hamma,ya tab'e baki yace "ki kwanta mana" da sauri tace "na kwanta a wannan lokacin?" Yace "mene ne idan kin kwanta yanzun?" Ta girgiza kai ta d'auki carbinta tana ja,tace "banji shigowarka ba yaushe ka shigo?" Bai kalleta ba yace "kina gyangyad'i ya za'ayi kisan na shigo dama" suna zaunen Manar ta fito sanye da dogon wando da t-shirt kanta babu hula sai kamshi take bakin nan bad'au da chapstick,tun kafin ta k'arasa turaren da ta sa ya sanar masa,ya d'aga kansa ya kalleta ya girgiza kai cike da takaici ya mik'e tsaye yace "d'auko hijab muje" kallon Dadda ta tsaya tana yi tana jira taji ko za tayi magana taga bata ko kallesu ba,shi kam tuni har ya nufi k'ofar fita ta juya ta d'auko ta kalli Dadda ranta a b'ace tace "mun tafi" Dadda ta d'auke kai tace "Allah tsare hanya" daga haka ta mik'e ta fara karkad'e kura,tana fita ta hangoshi a parking space ta k'arasa a hankali,ya bud'e front seat ya shiga ba tare da ya ce mata komai ba,ganin ta tsaya ya lek'o fuskarsa a d'aure yace "za ki shigo mu tafi ko tsaiwar za ki ci gaba da yi?" Ta tab'e baki ta bud'e ta shiga ta rufe,ya kalleta kafin ya fara warming motar then yayi zooming off suka bar gidan,suna isa makarantar yayi parking a inda aka tanada,science academy ne mai kyau da yake had'e boys and girls,yayi parking ya fita yayi gaba,ita kam tana ciki sai zare ido take sai da ya juya yaga bata fito ba ya mata tsawa yace "get down Malama" ganin yanayin fuskarsa yasa ta bud'e ta sakko ya wuce forefront ta dunga binsa a baya har suka k'arasa office d'in principal,cike da girmamawa matar tayi welcoming d'insu dan tsaf ta shaida Waleed ta nuna musu guri suka zauna,after sun gaisa da Waleed Manar ta gaisheta,matar ta kalleshi tace "Mr Maji dad'i! Meke tafe da ku?" Waleed ya gyara zama yana kallon Manar ya mata bayanin abunda ya kawo su,ta gyad'a kai ta kalli Manar tace "ya sunanki y'an mata?" Manar dake b'ata rai tace "Manar Muh'd Maji dad'i" cikin barkwanci matar tace "wow! Triple M ko?" A hankali Manar ta d'aga kai ta kalleshi,yadda taga ya had'e rai ta sunkyar da kanta tana wasa da fimgers d'inta,Waleed da ya zuba mata ido ya juya ya kalli matar yace "Zainab Muh'd Maji dad'i shi ne sunanta" principal ta gyad'a kai tace "wane class ta gama can makarantar da ta baro?" Wani murmushi Waleed yayi ya kalli Manar cike da takaici yace "madam a tunaninki wane class ne ya dace da kamarta?" Principal tayi murmushi tace "think s.s one ko j.s.s three?" Waleed ya sake yin murmushi yace "ku kaita j.s.s one.." Matar ta kalleshi cikin mamaki tace "j.s.s one?" Waleed ya gyad'a kai,principal tace "amma ba ka ganin shekarunta da girman jikinta ya wuce na y'an j.s.s one?" yace "wane aji kike ganin ya dace da ita idan ba can ba?" Principal tace "j.s.s one duk k'ananun yara ne babu sa'anninta a can,ina laifin ma a kaita ko j.s.s 3 d'in" waleed yace "Ko kin san iya karta primary daga nan bata ci gaba ba?" Matar tace "wannan ai ba wani abun damuwa bane" yayi wani murmushi mai had'e da k'wafa yace "please madam ku kaita j.s.s one" sheshshek'ar kuka Manar ta fara,ya waigo da sauri ya kalleta,babu shiri ta rufe baki,ya sauke numfashi ya mayar da hankalinsa kan principal yace "madam she deserved nowhere than j.s one" principal tace "why not baza'a a had'a ta da y'an uwanta ba,idan yaso sai ku nema mata lesson teacher da zai na guiding dinta a gida.."