Sashe 3
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tace "ke ni ban ce miki shi ba,amma dai uwarsa da k'annensa babu ruwanki da su duka kinji na gaya miki dama" gyad'a kai tayi saurin yi suka k'arasa apartment d'in k'arshe,Dadda ta d'auko mukulli daga jakarta da take rataye da shi irin na zamani ta bud'e,Manar tayi sauri ta shige tana kalle²,Dadda ta saka k'afarta cikin parlon tana washe bakinta da yasha hakor'in makkah har hud'u,biyu sama biyu k'asa tana lumshe idanu ta furta "O'ohhh! Gida kenan.. Malam bahaushe yayi gaskiya da yace kowa ya bar gida,gida ya barshi.." Fitowarsa kenan ya hango mutum tsaye gurin,matashi ne kyakykyawa dogo kamarsu da Waleed har ya b'aci sai dai shi skin d'insa ya d'an yi duhu,Waleed kuma ya girme sa da 2yrs,idan ba wanda ya sansu ba sai yayi zaton they're twins,bud'a idanu yayi ya dunga kallonta sanda ya kusa k'arasowa gurin da murnarsa yace "Dadda!" Waigawa tayi saurin yi ta kalleshi tayi mitsi² da idanu tace "waye wannan kuma?" Wani murmushi ya saki yace "Haba matar *AMAAR* ne fa,ya idon na ki?" Washe baki tayi tace "A'ahh! Kace min d'an Fodiyo ne,mai gidana na kaina,ai da farko na d'auka wancan mutumin ne ya sake dawowa nayi masa fata²" murmushi yayi yace "Waleed wai?" Tsuke fuska tayi tace "waye kuma Waleed?" Yayi dariya yace "haba Dadda *MUHAMMAD* d'in ne baki sani ba?" Tace "to ni ka ce min wani Waleed? Waleed ai ba suna bane" dariya yayi because ya san halinta haka take cewa idan suka samu matsala,yace "kun had'u da shi kenan?" Tace "ai tunda kaji ina wannan maganar kaima ka sani" yayi murmushi yana gyad'a kai yace "yanzu kuke tafe?" Tace "wallahi fa.." Da wani murya tace "Afff! Yi sauri d'an albarka kaje waje ka kalle min mai motar can kada ya sace mana kaya" wani kallo ya fara mata kafin yace "sata kuma Dadda?" Tace "yo to idan yaga babu idanun mu a kansa ai sai ya sace su,ka san mutane ba gaskiya suka cika ba" Manar dake tsaye cikin parlor tana jin zancen da Dadda keyi ta tab'e baki bata ce komai ba,Amaar yace "a'a Dadda ba zai sace ba,ba shi ya kawo ku ba?" Tsuke fuska tayi tace "yo dan shi ya kawomu,rubutawa akayi a goshinsa bazai sace ba?" Amaar ya fara dariya,tace "Ai ka ji matsalarka,sai ana magana ka farawa mutum dariya,kana nan ma ai tuni sai ya gudu da su" juyawa yayi saurin yi ya ci gaba da dariya ya nufi hanyar get yana fad'in "bari dai naje na gani" tace "yawwa! Hanzarta kaje dan Allah kada ya b'ace mu shiga uku.. Uban dukiyar mu kad'ai ya gudu da shi ai ya cuce mu.." Ta shiga parlon tana ci gaba da mita "wallahi kuwa da sai na sa Yaro yasa an nemosa duk inda ya shiga ya biya mu dukiyar mu,idan yak'i kuwa dama cewa zanyi da alk'ali ya d'auresa kawai har sai ya fito mana da dukiyar mu,ina dalili? Zan zauna na zuba ido mutumi ya gudu da dukiya ya barni na shiga uku?" Haushi ne ya ciko Manar ta d'ago tana had'e rai tace "dan Allah Dadda kiyi shiru,tunda ba'a ce miki ya gudu ba,mitar me kike yi kuma?" Wani kallo ta wurga mata tace "kuji min mata kamar na kasa da ita! Ai kiji in gaya miki idan ba cewa akayi mutumin yana nan ba,idan kinji na yi shiru Allah tsinemin,uban dukiyar nan da muka zo da shi,banda nawa ko iya naki kad'ai ya gudu da shi,danginsa kaf birni da k'auye sunyi hannun riga da talauci bare ya sace duka.. Kuji min mahaukaciyar yarinya wai na bar magana" hararta Manar tayi tace "ai sai kiyi ke kad'ai" ta tashi a fusace za ta fita,Dadda ta rakata da mugun kallo tace "a gaida na gaba.." Bata kulata ba ta fita,a hankali take tafiya kamar mai counting steps d'inta sanda taje k'ofar gidan ta tsaya balcony,kusan mintunanta biyar tana ta tsaye a gurin ta kasa shiga,Amaar dake shigowa da almajirai yana nuna musu inda za su kai kaya ya hangota tsaye yace da d'aya a cikin su "idan kun gama ku jira ni" yace "toh" ya k'arasa gurin yana kallonta yace "K'anwata me kike yi a nan?" Juyawa tayi da sauri ta kallesa tayi masa murmushi tace "Yaah Amaar!" Yayi mata murmushi shima yace "ai na d'auka Dadda ita kad'ai ta zo,ashe tare kuke?" Ta gyad'a masa kai tace "ehh" yace "ya hanya?" Ta fara gaisheshi kafin ta amsa,yace "ba shiga za kiyi ba kika tsaya a nan?" Ta gyad'a masa kai tace "laa! Wajen aunty fa zanje" gyad'a kai yayi ya bud'e k'ofar yace "muje tou" ta fara wucewa,a dining ta hangosa zaune shi kad'ai yana cin abinci,ta bisa da kallo kamar mai jin tsoro,suna had'a ido ya d'aure fuskarsa,Amaar ya kalleshi yayi murmushi cike da tsokana yace "brother! Dadda tana nemanka" bai kalli direction d'insu ba yace "me zan mata?" Amaar yace "i don't know,sai dai kaje kaji" tab'e baki yayi bai sake magana ba yaci gaba da cin abincinsa,Manar ta kalleshi ganin sai had'e rai yake ta kasa masa magana a sanyaye idanunta suna kawo k'walla ta wuce hanyar stairs,ganin Amaar ya tsaya gefe ta d'aga kai da sauri ta kalli dalilin tsaiwarsa,bin matar dake sakkowa da kallo tayi wacce baza ta haura 52yrs ba har ta gama sakkowa,satan kallon Manar da ta k'i kallonta ta dunga yi ta tab'e baki ta wuce,a hankali Manar ta d'aga kai ta d'an kalleta da wani murya tace "ina yini?" Cikin izza matar tana kallonta tace "lafiya" haushin amsar yasa Manar ta d'ago da sauri ta kalleta tayi k'wafa a ciki tace "idan na sake gaisheki ki amsa duk yadda kika ga dama" idanunta akansa sanda ta k'arasa cikin parlon tana masa wani kallo tace "Waleed! Me nake gani?" D'ago kansa yayi saurin yi ya kalleta yak'i cewa komai,ta had'e rai tace "am i not talking to Waleed? Ko ni sa'ar wasan ka ce da za kamin shiru kana kallo na ina magana?" Sunkuyar da kai yayi a hankali yace "i'm sorry" tana ci gaba da kallonsa tace "d'azu dana sa a tambayeka me kace min?" Saurin d'agowa yayi zai yi magana ta d'aga masa hannu tace "iskanci ne yasa kace ma Diyanah azumi kake?" Yace "ba haka bane Mama,ciwon ciki ne yasa ni sauke azumin,amma banyi miki k'arya ba" idanu ta zuba masa tana masa wani kallo cike da tuhuma tace "wane irin ciwon ciki ne haka lokaci d'aya har ya tafi?" A dake yace "kawai zuwa yayi" numfashi ta sauke ta gyad'a kai tace "Allah sawak'e" ba dan ta yarda da abunda yace ba ta nemi guri cikin parlon ta zauna ta d'auki remote tayi powering TV,juyawa yayi ya kalli direction d'in da Manar take tsaye har sannan ya aika mata mugun kallo kafin ya d'auke kai,Amaar da ya kula bata biyoshi ba ya waiwayo,tsaye a k'asa ya hangota ba ta da niyyar tahowa ya girgiza kai yace "Manar! Me kika tsaya kallo?" Saurin juyawa tayi ta bi bayansa,yayi knocking k'ofar bedroom d'in,daga ciki aka basu izinin shiga,tura k'ofar yayi ya shiga da sallama,ta bisa a baya suka shiga tare,y'ar kyakykyawar budurwar dake tsaye wacce baza ta wuce sa'ar Manar ba tana nad'e kayan dake zube saman gado ta waigo ta amsa,tayi masa murmushi tana ci gaba da nad'e kayan tace "Yaa Amaar aunty tana nemanka" yace "where's she?" Tace "tana toilet" Manar ta lek'o daga bayansa tana sakin murmushi tace "Marhaba uktiiy!" Saurin waigowa ta yi jin magana kuma,she thought shi kad'ai ne ya shigo da farkon,dai² lokacin Amaar ya wuce gaban mudubi yana shirin janyo kujera ya zauna,idanunta suka sauka kan Manar dake tsaye tana kallonta sai murmushi take mata,wani ihu ta fasa ta saki kayan hannunta da gudu ta taho suka rungume juna,daga toilet Aunty da ta jiyo ihunta tayi magana "Ameerah! Kin samu tab'in hankali ne kike min ihu?" Cikin farin ciki tana rik'e da hannun Manar tace "Aunty u know what?" Aunty tace "sai kin fad'a" tayi murmushi tace "surprise! Fito kiga" tsaki Aunty tayi saboda sanin shirmen Ameerah,ta gama d'aura alwala ta bud'e k'ofar ta fito,tsaye tayi a door way ta dunga kallon Manar da mamaki tace "daughter! Ke ce da gaske?" Tashi Manar tayi da sauri ta k'arasa ta shige jikinta,Aunty ta rungumeta back tana sakin murmushi tace "saukar yaushe?" Manar tace "yanzu!" Gyad'a kai Aunty tayi ta fara amsa gaisuwar da take mata tana shafa kanta,suka k'arasa bakin gado tana rik'e da hannunta suka zauna,Amaar dake zaune yana danna waya ya d'ago ya kallesu,kafin yayi magana aka turo k'ofar,duka suka juya suka kalli gurin,Dadda ta tsaya gurin fuskarta babu fara'a tana kallon Manar tace "yanzu idan ba iya shege ba,daga zuwa har kin taho gantali,ni kike nufin zan gyara miki gidan?" Tsuke fuska Manar tayi ta d'auke kai tak'i cewa komai,Aunty tayi murmushi tace "sannu da zuwa Hjy" wani kallo Dadda tayi mata kafin tace "yawwa" fuska babu wadataccen fara'a ta ci gaba da mita "ka ga yarinya kamar ba da ita nake magana ba ta manna min hauka.. To kin yiwa uwarki shiru.." Dariya Ameerah ta fara tace "sannu da zuwa Dadda" ko tankata bata yi ba,ta zubawa Manar ido da tak'i kallonta,a fusace tace "wai ba dake nake ba kika k'i kula ni?" Manar ta juyo ta kalleta tace "me zan miki tou?" Dadda tace "da kika taho kika barni ni baiwar uwarki ce ko ta ubanki?" Kicin-kicin Manar tayi ta tsuke fuska itama tana yiwa Dadda wani kallo ta gyad'a kai tak'i cewa komai,a fusace Dadda tace "wallahi tunda kika min haka sai dai ki tafi gurin uwarki dama,baza ki kwanar min a gida ba" murmushi Aunty tayi tace "kiyi hak'uri Hjy bari a tura maids su gyara" saurin washe baki Dadda tayi hakor'in makkan ta suka bayyana tace "to babu laifi,dan dai ni kam dama bazan iya wannan aiki ba daga zuwa na" Aunty tayi murmushi tace "ki shigo ciki Hjy kafin a gyara muku part d'in" saurin girgiza kai tayi tace "a'a a'a! Barni a nan ma tafiya zanyi nasa musu ido,na baro kaya uban dukiyarmu idan ba na gurin ai sai su samu damar sacewa" tagumi Amaar yayi ya zuba mata ido,Aunty tayi murmushi tace "baza su sace ba Hjy ki shigo har su gama" juyawa Dadda