← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 184

Sashe 55

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"za ki raka ni unguwa" ta zaro idanunta tace ''Yaya ina?" Yace "gidansu" kallonsa ta dunga yi kafin tace "Yaya ka fara sonta?" Wani kallon da ya d'ago ya ba-ta ta kawar da kanta tana zumb'uro baki tace "to kuma sai kana min irin kallon nan,nifa tambayarka kawai nayi" lumshe idanunsa yayi a hankali yace "Mama ta takura sai na je munyi magana da ita" ta tab'e baki tace "to kuma ni sai kace na raka ka?" Ya d'an marairaice yace "please mana kinga fa kece babban k'awar ango idan munje yau shi kenan" ta washe baki tace "to kuma Yaya ai baka mana d'inkin biki ba ma" ya kalleta yace "anya akwai ankon da za'ayi a bikin?" Tace "to ba na ga su Deejah sun turama k'awayen su ba a group d'in class" ya gyad'a kai yace "alright! Ki tambayi kud'in kafin anjima" da murnanta sosai ta amsa,ya d'an kulle idanunsa kad'an yana tunanin yadda za su k'are da yarinyar dan shi kawai zai je ne ba wai dan yana ra'ayi shi a karan kansa ba. Da yamma ya fito cikin shirinsa,d'anyen shadda ne sanye jikinsa arsh colour,yadda take maik'o da kyalli kad'ai ya isa fayyace adadin tsababan kud'in da aka narka wajen siyanta,rigarsa iya guiwa an mata hannun links d'inkin dai² zamani,banda kamshi babu abunda yake beard d'insa da baida duhu kana iya hango asalin skin d'insa mai haske sai kyalli yake fiddawa,ya murza hula akansa,hannunsa d'aure da wani black ion-plated multi functional chronograph na company Skmei,yana fitowa bedroom d'insa suka had'u da Mama dake haurowa saman,ta kalleshi ta k'ara tana washe baki tace "tafiyan ne ya tashi?" Ya gyad'a mata kai yace "sure!" Cikin nuna tsantsar farin ciki tace "to Allah tsare hanya a gaishe su.." Ya amsata yana sauka k'asa,a mota ya kira Manar ta d'auka tace "hello Yaya!" Fuskarsa babu alamun farin ciki irin na mutumin dake shirin aure yace "ke nake jira ki same ni a mota" ta amsa da sauri tace "ga mu nan fitowa" ta katse kiran,shiru ya d'anyi yana kallon part d'in ta mirror ya ga sun fito ita da Ameerah cikin kaya iri d'aya,d'an ubansun lace ne a jikinsu royal blue da crystals fari a jiki,sun saka mayafi da takalmi iri d'aya duk farare sun rik'e da wayoyinsu a hannu,tafiya suke suna hira suna darawa gwanin kyau da burgewa,da yake kuma they're look alike sai kayi zaton tagwaye ne,ya shagala wajen kallonta har suka k'araso bai sani ba sai da ta bud'e motar ta shiga,k'aran rufe k'ofar yasa shi saurin kallonta,kyakykyawan murmushinta tayi masa tayi fari da idonta tace "Yaya na yi kyau?" Ya d'an yi murmushin da baiyi niyya ba yace "u look gorgeous" tayi dariya tace "Yaya bari muyi photo" yace "alright!" Tace "Yaya muyi da naka ya fi camera" ta kai hannu ta d'auki wayarsa dake gefenta,shi dai bai ce mata komai ba ta d'aga musu selfie yana wannan tsadadden murmushin nasa,after sun gama ya tada motar suka tafi,sanda suka je gidan yayi parking ya kira Afiyah a waya,ta d'auka cikin yauk'i tace "Hello D ka shigo mana sai kace dai gidan bak'on ka ne?" Yace "nope! Ki fito we are outside" tace "please ka shigo kawai Mummy ba ta nan fa idan ma ita kake jin kunya" wani haushi yaji a fusace yace "idan baza ki fito ba mu koma inda muka fito" da sauri tace "alright! Ga ni nan zuwa to" ta ajiye wayar tana tab'e baki tace "d'an bala'i ka gama duk wulak'ancin ka kafin ka shigo hannu na ne" ta d'auki siririn mayafinta ta d'ora kan shoulder d'aya taja flat shoe d'inta ta sakko k'asan,a hankali take tafiya kamar tana k'irgen steps d'inta,ta rage girman idanunta saboda haske ta hangosa can wajejen get tayi siririn tsaki tana mitar "ji d'an walak'aci dole sai ya sa ni dogon tafiya" a haka dai ta wuce tana jin b'acin rai saboda Afiyah irin mutanen nan ne da abu kad'an yake b'ata musu rai,kafin ta k'arasa inda motar yake ta saki fuskarta tana murmushi,da yake glasses d'in motar da suka zo masu duhu ne and duka kuma a rufe suke bata fahimci tare suke da su Manar ba tana shirin zagayawa side d'in mai zaman banza ta shiga ya sauke glass d'insa yace "there's someone a front seat ki shiga baya" wani b'acin rai ne ya tunkud'o mata but ta danne ta sake yin murmushin yak'e ta bud'e back seat d'in ta shiga tayi musu sallama,ta kallo side d'insa taga wace ce a kusa da shi Manar ta waigo tace "amaryar mu ina wuni?" D'an dariyan yak'e Afiyah tayi tace "how are u?" Manar tayi murmushi tace "fine!" Da wani iyayi saboda yanzun an fara gane yes da no,wani kallonta Waleed yayi bai san sanda ya saki lallausam murmushi ba jin mutuniyar an yi turanci an wani basar,Ameerah ma ta gaisheta ta amsa,ta d'an kalli Waleed tace "D duka k'annenka ne?" Yace "baki gane su bane?" Ta gitgiza masa kai tace "yeah! That's it" wani kallo ya mata ta mirror yace "wait..! K'annena kika ce? Ke ba k'annen ki bane?" Tayi dariya tace "nope na yi maka yadda za ka fi ganewa ne dai" ya tab'e baki cikin k'osawa da magana yace "Uhn! Mama tace kina son ganina,ya akayi?" Kallon su Manar tayi kafin ta kalleshi tace "D mu shiga parlor please ka ga ai baza muyi magana gaban k'anne ba ko?" Directly yace "no just say it out.. I'm in hurry" tace "but how are going to talk in front of everyone?" A fusace yace "su waye everyone? K'annen nawa kike cema haka?" Kallonsa ta dunga yi ta kasa masa magana gaba d'aya ya sanyaya mata jiki ta gyad'a kai cike da b'acin rai tace "alright! To mu bar maganar kawai kwayi da Hjy" yace "wace Hjyn?" Tace "ur Mom" wani juyowa yayi ya zuba mata kaifafan idanunsa tace "think kamar hakan zai fi ko?" Even though she was reluctant to tell him,ya gyad'a kai yace "alright! U can go" haushin maganarsa ya tunzurota tace "Waleed me yasa kake min haka wai? Kamar dai ba aure muke shirin yi ba?" Yace "if u're done get down please,i don't like noise" nan da nan hawaye suka kawo idanunta tace "u are chasing me all because of na ce ina son ka,and kuma a kan idon k'annenka?" Zuciya ta tunzurosa yace "watch ur tong girl,kin san ba ni nake k'asanki ba ko?" Tace "i know but u are showing me that ba ni da muhimmanci a rayuwarka,a haka za mu gina gidan auren mu?" Tsaki yayi ya d'auke kansa zuciyarsa sai tafasa yake,seeing that he refused to take care of her condition ta bud'e motar hawaye suna zubowa idanunta tace "thank u" ta juya ta wuce gidan da sassarfa. Jikin Manar ya yi sanyi a hankali ta kalleshi tace "Yaya me yasa za ka sata kuka?" A fusace yace "keep ur mouth shut.. Kada ki dame ni da surutun banza da wofi." Ya tada motar ba tare da ya kalleta ba yayi horn get keeper ya bud'e musu suka fice da mugun gudu a hanya motar ya yi shiru Manar dai bata daddara ba tace "Yaya! Ni dai gaskiya ban ji dad'i ba" without ya kalleta yace "baza kiji ba kuma" ta kalleshi fuskarta a had'e tace "to kai wai Yaya a haka ma za kayi auren kana sa ta kuka?" Tsaki yayi yace "ki rufe min baki kafin na bigeki" ta kallesa tace "dan na ce haka shi ne za ka doke ni?" Ya d'auke kansa bai k'ara kulata ba,ganin ya mata shiru itama sai bata sake ce masa komai ba tayi fushi ta juyar da kanta,suna shiga gidan yayi parking ta bud'e motar ta fita cike da haushi ta wuce part d'in Dadda,ya bud'e motar yana kallonta har ta kusa shigewa yana niyyar fita ya rufe motar wayarsa ta fara ring,ya juya ya d'auka yaga Mama ke kiransa,ya d'auka ya kai wayar kunnensa,cike da bariki Mama tace "Waleed kana ina?" Yace "ga ni parking space wani abu ne?" Tace "har ka dawo ne?" Yace "ehh!" Gyad'a kai tayi tace "ya kuka yi da Afiyah?" Shiru ya d'anyi though jikinsa ya bashi ta san wani abu game da yadda suka yi da ita yace "Mama ta ce miki wani abu ne?" A fusace tace "wane irin magana kenan? Ina tambayarka kana tambayata?" Yayi ajiyar zuciya yace "mun gama magana da ita" Mama tace "ya kuka yi? Nawa ka tura mata kud'in gyaran jiki da k'unshi?" Yayi shiru yace "she didn't told me" tace "saboda me? Ko dai baka je ba?" Yace "not at all Mama yanzun fa na shigo gidan" gyad'a kai tayi tace "kada ka min k'arya yallab'ai,yanzun muka gama waya da ita tace min baka je ba,so kafin ka b'ata min rai maza ka juya kaje ka sameta" yace "amma fa Mama" a fusace tace "but what? Me za ka fad'a min? Halinka yanzu wanne ne bak'o a gurina?" Yana ji yana gani haka Mama ta masa tass a waya,kan dole kuma ba don yana so ba ta sa shi komawa,yana shiga compound d'in gidan ya fito ya jingina da motarsa fuskarnan tamkar hadari,Afiyah da tasa a mata observing idan ya dawo tana jin ance ga shi can tsaye ta buga tsalle taja gyalenta ta fita,tana masa murmushin mugunta ta k'arasa cike da kissa tace "Welcome back D" ya sake d'aure fuskarsa bai tankata ba,ta matso kusa da shi ta tsaya kamar za su manne da juna tace "muje ko?" Ya d'auke kansa yace "fad'i abunda kike son cewa ba ni da lokacin b'atawa" wani dariya tayi tace "no problem! Tunda ka dawo ai bazan ji haushi ba ko me za kayi min" ajiyar numfashi yayi yace "idan ba ki da abun fad'a zan tafi" tayi dariya tace "yadda ka tafima haka za ka sake dawowa" murmushin takaici yayi ya d'auke kansa..
Chapter 55 · 0% Book details