← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 184

Sashe 11

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

miki bai isheki ba?" A tsiwace Deejah tace "to ko za ki k'ara dukana ne?" Manar tace "kiyi min abunda zan dakeki kiga idan ban fasa miki jiki ba" matsowa gaban Manar ta fara tana rik'e waistband d'inta,a tsiwace tace "ga ni ai ki dake ni kiga idan zan kyaleki" da sauri Diyanah ta rik'o hannunta k'asa² tace "muje Yaya yana kallonki" saurin waigawa tayi ta hangosa zaune cikin mota ya zubo musu idanunsa,da sauri ta juya tayi k'wafa k'asa² tace "next time,we'll meet!" Suka shige ciki da sauri,tab'e baki Ameerah tayi ta juyo ta kalli Manar tace "let's go sis! Ai ko yanzu jikinsu ya fad'a musu" wani murmushi Manar tayi suka shiga gidan tare. After an sakko masjeed motar Waleed ya shigo gidan,tun daga nesa ya hangosu a gurin su uku suna kneel down ya gyad'a kai ya samu guri yayi parking ya fito ya rufe motar,yana k'arasowa gurin ya kalli Ameerah yace "where's *MANAR?"* In'ina ta fara tana son kare Manar,da sauri Deejah tayi zaraf tace "Yaya! Bata zo ba mu kad'ai muke yi tun d'azun" wani kallo ya aika mata yace "who asked u?" Sauke kanta k'asa tayi tace "i'm sorry" ya aika mata wani kallo yace "idan na sake magana ba dake nake ba kika sa min baki saina fasa miki jiki.. Stupid girl" ya juya yana k'ok'arin barin gurin yace "je ki kiramin ita" Ameerah ta tashi da kyar k'afafunta duk sunyi tsami ta nufi hanyar part d'in Dadda,a parlor ta tarar da Dadda zaune ta zubawa TV idanu ba ta ko gane me ake cewa,ta shiga tana tambayarta Manar,Dadda ta juyo ta kalleta ta d'auke kai tace "tana mad'bak!" Da sauri Ameerah ta nufi hanyar kitchen d'in,a door way ta tsaya tana kallonta tace "Sis ki zo inji Yaya" juyowa Manar tayi saurin yi ta kalleta,tana squeezing fuskarta tace "me zan masa kuma?" Ameerah tace "ya dawo bai ganki ba a gurin shi ne yace na kira ki" rau² idanunta suka yi,da muryar kuka tace "kiyi tafiyarki dama ni kada ki tsaya jira na" Ameerah ta bud'a idanu tace "Yaya ne fa yake kiranki" Manar tace "ni dai bazan je ba,dama kice baki ganni ba" Ameerah tace "kizo muje kada ki k'arawa kanki laifi please" a fusace Manar ta juyo hawaye kwance cikin idanunta tace "na ce miki ki tafi ko?" Dadda ta jiyo su tace "me yake faruwa?" Manar ta lek'o daga kitchen tana share hawaye tace "wai Yaya ne yace ta kira ni" Dadda tace "akan wane dalilin zaisa a kira ki?" Ameerah tace "d'azu ne ya ganmu muna kokawa da su Deejah shi ne yace muyi kneel down kafin ya dawo daga masjeed" tab'e baki Dadda tayi tace "meye kuma nil doo?" Ameerah ta fashe da dariya tace "kneel down fa aka ce" Dadda tayi mitsi² da ido tana kallonta tace "ohoo! Muku ku kuka san shi,ni da ban yi boko ba,ai ba rubutawa aka yi dole sai na fad'a dai² ba" Ameerah ta dunga dariya,Dadda ta d'auke kai ta ci gaba da kallonta,sanda tayi mai isarta tana kallon Manar dake b'are garlic za tasa a farfesun da ta d'ora tace "ni dai Allah da za ki ji ki zo muje kawai" tsuke fuska Dadda tayi a fusace ta juyo tace "kije kice masa na hanata zuwa" Ameerah ta gwalo ido tace "Dadda ki bari mu tafi,Allah idan ya kamata ko?" A fusace Dadda tace "idan ya kamata ya zare mata rai,kije ki ce masa ni na hanata zuwa,na ce baza ta zo ba d'in" jikin Ameerah a sanyaye ta juya ta fita daga part d'in,a hanya suka had'u da Waleed,tun daga nesa ta hango irin kallon da yake mata,tayi saurin sunkuyar da kanta k'asa bakinta har b'ari yake tana fad'a masa sak'on Dadda,k'ala bai ce mata ba ya wuce ta,yana shiga yaga Dadda ita kad'ai ya had'e rai yace "ina wannan yarinyar take?" Dadda tayi kamar bata jisa ba ta kafe TV da ido,gyad'a kai yayi har ya juya zai fita ya jiyo motsi a kitchen,fasawa yayi ya nufi hanyar da yake jin motsinta,cikin d'aga murya Dadda tace "me za kaje yi nan kuma?" Bai tankata ba ya shige,Manar dake tsaye wajen sink tana wanke naman da za ta d'ora a wuta ta juyo da sauri jin k'amshin scent's d'insa yana kusantota,ido biyu suka yi da shi yana shigowa,ya mayar da k'ofar ga rufe saboda Dadda da ta biyosa fuskarsa a d'aure yana aika mata wani kallo yace "har ni zan aiko kiranki kik'i zuwa? Ke har kin isa? Nawa kike?" Baya tayi da sauri ta jingina da cabinet idanunta sunyi rau² tace "Yaya ni fa ban ce mata bazan zo ba" wani tsawa ya mata,Dadda dake waje ta fara buga k'ofar tana kiransa "Mamman! Yalla iftahal baab" banza da ita yayi kamar bai san me take cewa ba,ya zuba idanunsa da suka yi jaa akan Manar dake zumb'uro baki yace "idan baki ce baza ki ba,ai kina da wanda za ta hana ki zuwa right?" Shiru tayi bata ce komai ba,Dadda sai buga k'ofa take tana kiransa ya k'i bud'ewa,cikin jin haushi tace "idan baka bud'e ba billahillaziiy zan kira ubanka na sanar masa,ni ban san wane irin jaraba ne yake damunka ba da ranar Allah ka shige ka kulle k'ofa me za ka yiwa y'ar mutane? Ni dai gaskiya ka fito kafin na tara maka jama'ah,tun wuri ka bud'e min k'ofar nan na shigo kada ka cuceni ina tsaye sake da baki a nan" wani b'acin rai Waleed ya dunga jin kalaman Dadda suna saukar masa,a mugun fusace ya dunga kallon Manar bai iya ce mata komai ba ya bud'e k'ofar da sauri Dadda ta fad'o kitchen d'in kamar an cillota,k'arasawa inda Manar take tayi da sauri ta rik'o hannunta tana dudduba jikinta tana tambayarta "babu dai abunda ya miki ko?" Manar ta d'ago ta kalleshi bata ce komai ba,Dadda ta ci gaba da duba jikinta tana sake tambayarta "ince dai bai miki komai ba da ya rufe k'ofar ko?" Nan ma shiru tayi babu amsa,jan hannunta Dadda tayi za su fita,Waleed yayi saurin fizgo Manar a tsorace ta fasa k'ara,Dadda ta juyo a fusace tana fad'in "ni dai yau na shiga uku da wannan mutumi,kai wai dan Allah ba ka da aikin yi sai na zuwa ka sani magana ne?" Idanunsa sun k'ank'ance yana mata wani kallo cike da b'acin rai yace "me kike nufi? Me maganganunki suke nufin zanyi mata?" Mitsi² tayi da idanu tace "kaga Mamman ka fita idona na rufe,zan maka wulak'anci a gidan nan" gyad'a kai yayi yace "tambayar ki nake me kike nufi da maganganun da kika fad'a?" A fusace tace "ban sani ba ubana,sai ka matse baki na sai na fad'a maka" wani yawun b'acin rai ya dunga had'iyewa ya kalleta ya kalli Manar ya kasa sake cewa komai da sauri ya juya zai fita,Dadda cikin d'aga murya tace "kuma dama zan sanar da uban naka abunda ya faru,idan ma baza su d'auki mataki ba ni zan d'auka.. Ni tun kana tsummanka na san ba k'aramin jarababbe za'ayi ba,yadda kake rik'e jelarka kana soshe²,banda kukan tsiya da kake damun mutane da shi,ai ko yanzun ma Allah ne ya rufa mana asiri na shiga na fita sai da na samo maka maganin k'aik'ayin nan sannan muka huta da masifar kukanka,yanzun ka zama mutum shi ne za ka saka min da rashin kunya da d'iban albarka.." Yana jinta bai tsaya mata magana ba ya fice daga part d'in gaba d'aya,zuciyarsa banda tafasa babu abunda take,ko ganin inda yake sa k'afarsa baya yi,daf zai shiga part d'in suka bangaji juna da Amaar,ya wuce bai ce masa k'ala ba,Amaar ya bisa da kallo har ya shige mamakin abunda yake faruwa da Waleed yasa kai tsaye daga nan bai zarce ko ina ba sai part d'in Dadda,a yadda yaga fuskarsa ya san b'acin ransa bazai rasa nasaba da can ba,tun daga bakin k'ofar shiga part d'in ya fara jiyo fad'anta cikin hayaniya,ya k'arasa da sallama still bata fasa masifa ba a hakan kuma ta amsa sallamar ta ci gaba da fad'anta,Manar dake kitchen har sannan ta fito tana b'ata rai tace "dan Allah mu dai kin ishemu haka nan,sai mita kike tayi bayan shi ya ma tafi" kallonta Amaar yayi saurin yi yace "me yake faruwa?" Kai tayi saurin girgiza masa alamun bata sani ba za ta juya,yace "k'arya kike" ta zumb'uro masa baki da sauri ta shige kitchen d'in,wucewa yayi zai bita kitchen d'in cikin sauri Dadda ta katse mitar da take tace "ina za ka kai kuma?" Amaar ya tsaya yana kallonta yace "dalilin fad'an ki nake son sani,and na ga Waleed yanzu a hanya ransa kamar a b'ace" kyab'e baki tayi tace "ai bama kamar,ni ce nan na b'ato masa rai" Amaar ya bud'a idanu yace "akan me? Wani abu yayi miki?" Tsaf ta kwashe komai ta sanar masa,shi kansa kallonta kawai ya dunga yi cike da takaici ya kasa cewa komai,kalmomin da ta sanar masa ta fad'awa Waleed babu wanda ya dace ace ita ta fad'a,idan akwai mutum d'aya da zai fara fad'an halayen Waleed tabbas zai kasance ita ce,saboda ta fi kowa sanin wane ne Waleed a duka gidan kasancewarsa rainonta,shi kansa da ba shi ta fad'awa maganar ba,abun ya mugun tab'asa bare Waleed,da ya sansa da bak'ar zuciya,abu kad'an yake fusatasa,ba wai dan Waleed yana stepbrother d'insa ba but kyawawan halayensa kad'ai sun wuce a jefesa da irin maganar,ba tare da ya iya ce mata komai ba ya juya ya fita daga part d'in dan bai ga amfanin zamansa ba ko sake yin magana da grandma d'in nasu..
Chapter 11 · 0% Book details