← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 184

Sashe 13

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da dare lokacin Manar tana parlor tare da Ameerah suna kallo Amaar ya shigo fuskarsa babu fara'a,a tare suka masa sannu da zuwa,bai kallesu ba ya amsa ya ciro wayarsa ya fara making call,wayar yana shiga aka katse aka kirasa video call,d'auka yayi saurin yi yayi sallama,muryar mace ce ta amsa shi,da sauri Manar ta kalli direction d'insa,idanunsa akanta shima yana kallonta har suka gama gaisawa,tana jin sanda matar tace "kana tare da su ne yanzun?" Ya gyad'a kai yace "sure!" Tace "where's my kid? Ba ni ita!" Kallon Manar yayi kafin yace "she's right here tana jinki ma" Da hannu ya yiwa Manar alama tazo,ta taso da sauri ta k'araso inda yake,ya mik'a mata wayar yace "Ga Mommella za kuyi magana" murmushi tayi cikin zumud'i ta karb'i wayar ta tashi daga kusa da shi,hak'oranta a waje tsabar murna tayi sallama,kyakykyawar matar da ta bayyana screen d'in wayar k'irar Apple (IPhone 11 Pro) sai murmushi take yi ta amsa sallamar da tayi mata,bayan sun gaisa cikin tsananin farin ciki tana kallon Manar tace "Baby! Haka kika zama? Me kike ci? Me Hjy take ba-ki kika yi girma haka sosai?" Dariya tayi cike da jin kunya ta b'oye fuskarta tace "Mommella! Yaushe za kuzo?" Wani murmushi Mommella tayi tace "muna nan a hanya in sha Allah" ta gyad'a kai tace "Allah kawo ku lafiya.." Mommella dai sai kallonta take yi cike da mamakin girman da ta k'ara yi cikin y'an shekarun da basa k'asar tace "baki tambayi bhai d'inki ba?" Murmushi tayi tak'i cewa komai,Mommella ta zaro idanu tace "Ohh! Baki damu da tambayarsa ba ko? Shi kenan zan fad'a masa nace ko tambayarsa baki yi ba" saurin girgiza kai tayi tana dariya tace "a'a Mommella!" Mommella tace "haka ne mana" girgiza kai ta sake yi za tayi magana ta jiyo wani sanyayyan murya yana fad'in "nima na yi fushi.. Mommella ki fad'a mata ko na je Nigeria ba zan kulata ba!" Dariya ta fara tace "a'a kayi hak'uri!" Tana jiyosa yace "na k'i wayon" dariya ta dunga yi,yace "u see dariya ma kike yi? Kinga baki damu ba kenan ko?" Tana dariya tace "a'a na damu mana!" Yace "baki damu ba baby.." tace "da gaske na damu" yace "ban yarda ba,da kin damu da tuni kin kira kiji lafiya na ko ki tambayi Mommella ina nake" wani irin b'ata rai tayi kamar za ta fashe da kuka a shagwab'e tace "ai to ba ni da waya ni" yace "u most be jocking.. Kamar ki ace ba-ki da waya?" Tace "da gaske fa nake yi,ka tambayi Mommella ma kaji" saurin bayyana kansa yayi a fuskar wayar,kyakykyawan matashi ajin farko,fuskarsa tana bayyanar da wani sihirtaccen murmushi yana kallonta yace "ya akayi babu phone a hannunki?" Tana tab'e baki tace "nima ban sani ba" shiru ya d'an yi kamar yana tunani then yace "any ways.. Amma dai kin ganki fa kin zama k'atuwa,yanzu ai ke za kina goyani ki ramamin goya kin da nayi sanda muke 9ja ko?" Wani kunya taji da sauri ta b'oye fuskarta ta kyalkyale da dariya tace "ai ka fini girma,ni bazan iya goya ka ba" murmushi yayi yace "raguwa kawai,ni zan goyaki idan na zo" gwalo idanu tayi tace "ina da nauyi fa" yace "duk nauyin ki zan goya ki,kin manta lokacin da muke nan?" Rufe fuskarta ta sake yi tana dariya tace "kai dai Yaa *AZAAN* ba ka mantuwa" yace "ya za'ayi na manta? Bayan ba wasu shekaru ne da yawa ba" sun jima suna hira kafin suka yi sallama,za ta katse kiran Azaan yace "but ban tambayeki ba?" Tace "me za ka tambaya?" Yace "phone d'in waye wannan?" Tayi squeezing fuskarta tace "a ina?" Yace "i mean wanda yake hannunki" d'an murmushi tayi tace "na Yaa Amaar ne" murmushi yayi shima yace "yana ina?" D'agowa tayi ta kallesa kafin tace "gashi a zaune" da sauri Azaan yace "ba-ni shi muyi magana" gyad'a kai tayi ta tashi ta kaiwa Amaar wayar,yana karb'a ya mik'e ya nufi hanyar fita. Almost one week da zuwansu tun ranar da suka yi fad'a da su Deejah Manar bata sake sa Waleed a idanunta ba,ko apartment d'insu taje ba ta ganinsa,Dadda kanta tun ranar bata kuma ganin ya shigo mata ba,da farko ta yi tunanin ko ba ya nan ma,sanda ta tambayi Amaar ko Waleed ya yi tafiya ne bai mata sallama ba? Ya kalleta yace "yana nan babu inda yaje" mamaki yasa Dadda tace "yana gari amma ba ya zuwa gaishe ni?" Amaar yace "a'a! Kefa kika koresa kika ce ya daina zuwa" gwalo idanu tayi tace "ni azumi? Kada ka min sharri da raina,ta ina zance ya daina zuwa bayan duk cikin jikokinta na fi sonsa" wani kallo Amaar ya mata yace "to ni dai ya fad'a min ke kika ce ya daina zuwa.." Rau² tayi kamar za tayi kuka tace "Wane irin laifi na masa ni kuwa da zamu kwana gida d'aya mu tashi bai zai zo ya gaishe ni ba,sai kace muna gab da juna?" Amaar ya dunga kallonta kamar zai yi dariya,ya mik'e da sauri yace "a'a nima dai ban sani ba,sai dai kije kiyi bikonsa kyaji daga bakinsa" yana fad'a ya kama hanyar fita zai bar apartment d'in,Dadda tayi shiru ta kasa masa magana har ya fita,har dare maganar bai bar damunta ba,lokacin Manar ta shigo daga apartment d'in mother ta d'ago ta bita da kallo har ta zauna kan kujera,kamar ance ta kalli Dadda taga ta yi fuskar kuka,dariya ta fara yi k'asa²,Dadda ta kasa daurewa ta mik'e da sauri Manar tace "ina kuma za ki?" Juyowa tayi tace "ke ni rabu da ni,wancan mutumin zanje nema,yau sati d'aya kenan ban sashi a idanuna ba" yamutsa fuska tayi tace "wane mutumi?" Dadda tace "Waleed mana.. Ko kin gane min shi?" Girgiza kai tayi saurin yi tace "a'a! Nima rabona da shi tun ranar da ya shigo kika samesa kitchen" Dadda dai kamar za ta fashe da kuka tace "to wai ni me na masa da zafi da zai d'auki gaba da ni,ya daina shigowa?" Manar tace "to ba ke kika koresa ba?" Zaro idanu tayi tace "yau naji jaraba.. Ya za kuna cewa ni nace ya daina zuwa,fisabilillahi Yaro yaji ai ba zai ji dad'i ba,ta ina ma zance ya daina zuwa?" Manar tace "to ba ke bace dai kika faffad'a masa magana,ai dole ya daina zuwa,kuma yanzu sai ki zo kina neman sa?" A fusace Dadda tace "ni dai yau na shiga uku,wane magana zan fad'a masa ni kuwa? Bayan duk cikin jikokina na fi sonsa!" Wani had'e rai Manar tayi ta harareta cike da jin haushi tace "to tunda kinfi sonsa ba sai ki tafi ki nemosa ba da kanki ki daina tambayar mu" Dadda tace "yanzu kuwa y'ar nan.. Bari ki gani" ta mik'e da hanzarinta,har ta yi gaba ta waigo tace "ko za ki zo muje tare? Kinga dare ne bana fita ni kad'ai ba" Manar dai bata kalleta ba tace "tsoro kike ji ne?" Da sauri Dadda tace "haba dai.. Wane mutum,me jiya tayi ma balle yau? Muda muke keta daji da talatainin dare" Wani dariya Manar ta saki babu shiri tace "ke dai Dadda idan tsoro kike ji ki fad'a sai na taso na raka ki" harara ta maka mata ta yi gaba tana mita "kuji min yarinya,Allah na tuba sanda muke k'auye muke gane² bamu ji tsoron komai ba sai yanzu da duniyar tayi lafiya,su kansu jinnun ba ganinsu aka cika yi ba saboda addu'ah da ilimin da ya ratsa mutane.." Dariya Manar ta dunga yi har da fad'owa k'asa bayan data tabbatar Dadda ta fita,ta tashi ta biyota lokacin har ta yi nisa,Dadda tana zuwa ta dunga bubbuga k'ofar apartment d'in da k'arfi,Mama tasa Deejah taje ta ga waye a gurin,tana bud'ewa taga Dadda ta bita da kallo bata yi magana ba,Dadda ta wuceta ko kallo bata isheta ba,tab'e baki Deejah tayi ta biyo bayanta,tun kafin ta k'arasa inda Mama take ta fara magana "Asama'u! Ni kam ina Muhammadu ya shiga duk kwanakin nan ban sashi a idanuna ba?" Waigawa Mama tayi da sauri,ganin Dadda yasa ta fad'in "sannu da zuwa Hjy" Dadda ta saki baki tana mata wani kallo kafin ta kyab'e baki tace "yau kuma ni kike ma sannu da zuwa?" Mama ta sunkuyar da kai ba don ta-ji kunyar abunda Dadda ta ce ba,Dadda ta tab'e baki tace "ni dai in dan ganin idona ne yasa kika ce min sannu da zuwa dama ki rik'e abunki,ni ba sannu da zuwanki na zo amsawa ba,tambaya ce dai na zo yi dama ina Mamman ya shiga?" Mama bata d'ago ba tana b'ata rai tace "bai dawo ba" Dadda ta k'ureta da ido tace "yana garin ne?" Mama tace "ehh yana gurin aiki" hangame baki Dadda tayi tace "Auuu! Da gasken dai ba k'arya aka masa ba yana nan,amma dan iya shege shi ne ba ya zuwa inda nake? Ince dai ke kika masa khud'ubar tsiya kika ce masa ya daina zuwa gaishe ni?" Saurin d'ago kai Mama tayi za tayi magana ta hango Abba yana sakkowa shi da Aunty dake bin bayansa,ba dan ta shirya had'iye maganar ba tayi shiru tak'i cewa komai,k'asan ranta sai suya yake mata,ta so ace Abba bai fito ba ta kwab'awa Dadda maganganu,Abba ya k'araso cikin parlon yana kallonsu d'aya bayan d'aya,yace "wani abu yake faruwa?" Da sauri Dadda ta kallesa tace "yawwa! Yaro gwanda da Allah ya kawoka,gara ayi komai akan idanunka" kallonta Abba ya ci gaba da yi bai yi magana ba,Dadda tace "ka ga wannan k'atuwar matar taka,wallahi ba ta da tsoron Allah ko kad'an" Abba ya kasa daurewa yace "me ya faru Hjy?" Dadda tace "idan banda rashin tsoron Allah ni ba ni na haifeka ba?" Abba ya gyad'a kai yace "ke ce Hjy" tace "to ita matar ta-ka bata san da haka bane ko dai mancewa tayi?" Abba ya kalli Mama da ta had'e rai yace "ta sani Hjy" Dadda tace "a'a bata sani ba" Abba dai ya kasa gane me Dadda take nufi sai kallon Mama yake yace "i made sure ta sani Hjy,ta san matsayinki a gurina" girgiza kai Dadda tayi da sauri tace "a'a Yaro kada ma mu fara jayayya da kai,da ta san irin matsayin da nake da shi a gurinka da
Chapter 13 · 0% Book details