← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 184

Sashe 67

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

za ku tashi ko sai rai ya b'aci?" Boss yayi magana it was there suka ajiye kan game d'in suka fara shirin tafiya,ya juya zai fita yace "ku jira na fito mu wuce" suka amsa masa,ko da ya fita bai ganta ba he thought ta gaji ta koma ne,ya tab'e baki ya wuce part d'in Dadda yana bud'e k'ofar ya ganta zaune kan kujera ita kad'ai kamar mayya,ya k'arasa bai ce mata komai ba ya wuce hanyar d'akin Dadda yayi knocking,yaji shiru ba'a amsa shi ba,ya kalli d'akin da su Manar suke yace ma Afiyah "babu mutane a gidan ne?" Tana danna wayarta tace "i don't know" ya wuce yayi knocking kafin ya tura k'ofar,Manar dake kwance kan gado da waya a hannunta tana chat da Azaan tana dariya ta waiga da sauri suka had'a ido ta d'auke kanta tana zumb'uro baki,yace "Hjy ba ta nan ne?" Tace "ehh" ba tare da ta kallesa ba,yace "ina taje?" A tak'aice tace "ta je masjeed!" Kallonta ya dunga yi kafin yace "masjeed?" Tace "ehh!" Yace "yaushe ta fara zuwa?" Tace "dama tana zuwa ai" ya gyad'a kai ya juya yana cewa "alright! Idan ta dawo kice mun shigo gaisheta" tace "toh" har zai fita ya sake kallonta yace "kun gaisa ne ke?" Bata d'ago kanta ba tace "a'a" yace "saboda me?" Tace "haka kawai" yace "taso ku gaisa" saurin d'agowa tayi ta kalleshi,taga ita yake kallo shima ta d'auke kanta tana tab'e baki tace "wa zan gaisar?" Yace "baki san wanda za ki gaisar ba?" Tace "ehh!" Tana d'aure fuskarta,yace "kada ki bari na maimaita" wani haushin da ya ciyota ta kalleshi eye to eye tace "ni bazan gaisheta ba fa!" Yace "saboda me?" Tace "i just don't like her" wani kallo ya dunga binta da shi,dai² lokacin Ameerah tana fitowa toilet,tana ganinsa tsaye ta wuce ta d'auki hijab d'inta tace "sis barin je gida na dawo" Manar ta amsa mata ta fita,ta juya masa baya da sauri ta goge idonta saboda ba ta son yaga hawayen da suka fara taho mata,Waleed dake kallonta har sannan ya rufe k'ofar d'akin,fuskarsa a d'aure yace "she is my wife Manar,aside that kuma ta girme ki sosai,kada ki sake ganinta ki k'i gaisheta,that's very disrespectful of u.." Juyowa tayi tana kallonsa da wani expression,ya k'arasa kusa da ita kafin yace komai cike da masifa tace "ni dai wallahi bazan gaisheta ba d'in,da ta girmeni sai kuma akace ta haifeni? Ni ina ruwana da ita da zaka ce min she is ur wife ko da na ce maka ban sani bane? What's my business with that?" Sai kuma ta fashe da kukan da dama k'iris take jira ta tashi za ta shige bathroom,da sauri ya rik'ota yace "No! I'm only reminding u Manar,i knew ba irin tarbiyan da mother ta maki ba kenan k'in gaida na gaba dake,kinga bazan ji dad'i ba idan baki gaisheta ba" fad'awa jikinsa tayi tana kuka sosai tace "ni dai wallahi Yaya bana son ganinta,i don't want her to stay here,kace mata ta tafi,i don't like her.." Bubbuga bayanta yayi yace "it's ok.. Za ta tafi yanzun shi kenan?" Ta gyad'a masa kai da sauri,kamar daga sama suka ji an banko k'ofar suka juya a tare suka kalli gurin,Afiyah dake tsaye sai kallonsu take cikin tsananin b'acin rai tace "dama iskanci kuke shi ne har da kulle k'ofa?" Waleed dake rik'e da Manar har sannan ya mata tsawa yace "watch ur tongue Afiyah.." Cikin tsawar itama tace "bazan yi ba d'in,munafikin Allah ta'ala,ka shigo ka ruk'unk'umeta kana lalubeta,kai yanzu Waleed baka ji kunya ba,ka rasa wanda zaka k'wak'wule sai wannan yarinyar,mene ne ma yake da akwai a jikinta?" Ta juya kan Manar data wani sake rirrik'esa tace "sure! Biri ya yi kama da mutum,ai tunda na samu labarin zaman Saudiyyan da kuka je ba na Allah bane,na san dole ma kiyi maitar maza,kin gama bin mazan ki a can shi ne za ki lik'ema mijina.. Ina so ki bud'e kunnenki da kyau ki saurare ni,wallahi ko kina tafiya da ubanki mijina sai dai ki gansa ki kyalemin abuna,ya fi k'arfin ki ke da shi sai dai kallo" wani tsawa Waleed ya sake mata yace "ya isheki Afiyah ki wuce ki bar nan" tace "baza'a bari ba d'in munafiki algungunmi.. Tunda muka yi aure ina ce ko hannuna baka tab'a tab'awa ba,i thought ko ba ka da lafiya ma ashe lafiyarka lau iskancinsa sai a wani gurin yake motsawa,ka dai ji kunya wallahi da ka rasa macen da za ta gusar maka da sha'awarka sai yarinya wadda bata gama mallakar komai ba" Manar dake jikinsa har sannan ta dunga kallon Afiyah,sosai kalamanta suka mata zafi cikin masifa ta bud'e baki tace "ba dai ubana ba sai dai in naki nake tafiya da shi.." Da sauri Waleed ya rufe mata baki,yace "shhhh! Kyaleta kada kice komai" ta gyad'a masa kai idanunta sunyi ja tace "Allah to ka mata magana kada ta sake zagina" magana ya rad'a mata a kunne ta kalleshi tana b'ata rai,ya lumshe mata idanunsa,ya juya ya kalli Afiyah dake tsaye tana kallonsu ranta a mugun b'ace,ya zabga mata mugun kallo bai ce mata komai ba ya kama hannun Manar yace "muje" ta gyad'a masa kai suka wuce za su fita,da k'arfi Afiyah ta fizgota,Manar ta fasa k'ara ta sake rik'e shi gam,Waleed ya juyo da sauri ya d'auke Afiyah da mari,ta dafe cheek d'inta tana kallonsa tace "akan wannan y'ar iskar yarinyar za ka fidda hannu ka mare ni?" Ransa a mugun b'ace yace "ko yanzun kika sake tab'ata zan miki abunda yafi wannan.. Stupid" ya wuce ransa a b'ace yaja hannun Manar suka fita,suna zuwa daf da balcony d'in mother ta k'wace hannunta ta shige ta barsa tsaye,binta da kallo ya yi kafin ya biyota,ta zauna saman kujera tana zumb'uro baki ya shigo,da sauri ta tashi za ta shige d'aki ya rik'ota yace "kiyi zamanki masjeed zan wuce" dai² yana sakin hannunta mother ta fito ta gansa tsaye ta kalleshi tace "baku tafi ba?" Ya sosa backhead d'insa yace "yanzu dai za mu tafi,ina su Asad?" Tana kallon Manar dake b'ata rai tace "ai sun fita tun d'azun" yace "okay! Bari naje maybe can suka tafi" tace "alright" ya juya yana satan kallon Manar ya fita,mother dake mata kallon tuhuma tace "ke kuma fa?" Manar ta d'ago tana kallon mother tace "babu komai" mother tace "babu komai kike b'ata rai?" Tace "ehh" tab'e baki mother tayi tace "na bar shinkafa a wuta idan ya k'arasa ki kwashe,saura ki bari ya k'one" ta wuce ta barta a nan. Waleed yana fitowa yaga Afiyah ta fito gidan Dadda tana share k'walla ya d'auke kai fuskarsa a d'aure ya wuce ya nufi gidansu,ta biyosa a baya tana matse idanu,yana shiga bai zauna ba yama Asad magana yace "kuzo mu wuce lokaci na k'urewa" yaran su biyar duka suka biyosa,Afiyah ta bud'e k'ofa ta shiga lokacin shi kuma yama fita,Mama ta d'ago tana kallonta tace "har kun dawo?" Afiyah ta kece da wani kuka,hankali tashe Mama ta rik'ota tana tambayarta "lafiya Afiyah? Me ya faru?" Afiyah cikin kuka ta fara bawa Mama labarin abunda ya faru tsakaninta da Manar,ran Mama a b'ace tace "dan ubansa shi Waleed d'in Mahaukacin inane da zai mareki? Kuma k'arya aka mata ba karuwanci aka kaita ba? Barni da shi zai dawo ya same ni,wallahi yau saina ci mutuncinsa" haka ta dunga fad'a kamar za ta ari baki,lokaci d'aya hawaye ya kawo idon Afiyah sai kuma ta fashe da kuka tace "is this the real him dama Hjy? me yasa tun farko baki yi encourage d'ina wajen ganin na hak'ura da shi ba,u always telling me i shouldn't worry zai koyi sona idan munyi aure,dama ya aureni ne to make life a living hell for me,kin san irin mutanen da na k'i amincewa da su nace sai d'anki? Na watsa ma idona k'asa na nace sai shi,son mutum da zuciya d'aya yana iya zama laifi dama? Tunda aka kai ni gidansa ko zaman minti biyar bai tab'a yi tare da ni ba bare ya kwana d'akina,wallahi ina sonsa Mama,ban auresa saboda komai ba sai saboda ina son kasancewa da shi,kin san irin gidan da na fito balle ace saboda wani abu na auresa" d'auke kai Mama tayi zuciyarta na bugawa ba ta son ace maganar ya yi nisa har ya kai kunnen Hjy Sahiba,sosai ta zage tana lallashin Afiyah tace "yi shirun ki daughter,in dai ni na haifesa dolensa ya zauna da ke ko da bai so,he won't make ur home a living hell for u,but u've to respect this family,duk abunda yace baya so kuma please try to avoid that ko dan ku zauna lafiya,kin san shi yak'i d'an yaudara ne ko ba haka ba?" Lamo tayi jikinta ta gyad'a kai tana imagining yanda rayuwarsu zai koma nan gaba,a hankali tace "kuma yana ganin yarinyar fa bata gaisheni ba ma ta wuce yak'i ce mata komai" Mama tace "bar shegiya mai bak'in ido,nima ba gaisheni take ba" Afiyah tana kallon Mama tace "dama ba ta da kunya?" Mama tace "dama kin tab'a ganin inda barewa ba tayi gudu d'anta yayi rarrafe? Ai like mother like her child.." Wuni guda hiran da suka dunga yi kenan,ko da aka taso masjeed Waleed kam bai dawo gidan ba,ya sauke su Mu'awiyah bakin get ya juya kan motarsa,sai dare sannan ya shigo yayi parking ya fito ya nufi b'angaren Dadda,a kan carpet ya sameta zaune ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya ta tasa plate a gaba,yayi sallama kafin ya shiga Dadda tayi saurin b'oye plate d'in a bayanta ta d'ago tayi mitsi² da ido tana kallonsa tace "wa nake gani kuma haka?" Ya kalleta ya d'auke kansa yace "wa kike zato?" Ta d'aure fuska tace "to me kuma ya kawoka da wannan talatainin daren tsakani da Allah?" Yace "ina ruwanki da abunda ya kawo ni? Bance zanci abunda kike b'oyewa ba dai" ta tsuke fuska tace "ai dama ba'a kada kai a magana,kuma abunda nake cin ma ya k'are kafin ka shigo,ka gani sai k'ashi kawai ya rage idan za ka tsotsa" ya zauna kan kujera yace "ina wuni?" Ta amsa tana kallonsa tace "to kai kuma baka tafi gida ba har yanzu? Me ka zauna yi a nan d'in?" Yace
Chapter 67 · 0% Book details