← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 184

Sashe 54

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A bangaren Mama sosai ta zage take shirin bikin,kullum suna hanyar kasuwa ita da Hjy Izzatu,dan yadda ta dauro d'amarar had'a kaya na gani a tafi ana fad'e,a yadda take shirin kana kallo za ka san tana yi ne fiye da k'arfin aljihunta,kuma duk ba komai yasa take haka ba sai don kawai tana kwad'ayi da burin taji duniya ta d'auki labarin auren,while a gefe guda duk sanda suka fita suka dawo da kaya nik'i² sai su baje a parlor,musamman idan sunga Aunty tana wani abun sun yi ta yar mata magana kenan da tunanin za ta tanka musu,sau da yawa sai dai tayi murmushi ba ta tab'a tanka su sai dai ta bar musu gurin dan tuni ta fahimci rashin aikin yi ke d'awainiya da su. As usual yauma d'in bayan sun dawo daga kasuwa suna zaune a parlor duk sunyi d'ai² da kayan da suka shigo da su suna d'ad'd'agawa ana lissafa tsababan kud'in da aka narkar wajen siyayyar,da yake girkin Aunty ne lokacin ta fito za taje kitchen tayi murmushi tace "sannun ku da dawowa" Hjy Izzatu ta amsa ta,Mama kam was busy a lokacin tana duba fancy jewelries da suka siyo,Aunty ta wuce su ta nufi hanyar shiga kitchen tana murmushi,ta jiyo maganar Mama sanda ta d'aga wani sark'a tana kalla tayi squeezing fuskarta tace "k'awata think fa sai na sa Waleed ya k'aro kud'i gaskiya.." Hjy Izzatu tace "ai dama ni tuni na ga wautarki da tun farko kika ambaci 3.5ml,Allah na tuba idan kayan da muke son had'awa ne ko 10ml ya bayar ai ba lallai ma su kai ba" d'an tsaki Mama tayi tace "ki bari kawai kin san ba tab'a had'a lefe nayi ba bare na san kan harkar,shisa nayi tunanin za su isa,but bari kiga ma na kirasa nace ya k'aro kud'i wanda suke hannuna baza su isa muyi sauran siyayya ba" Hjy Izzatu tace "Atoh! Ya kamata dai mu fita kunya dan kina ganin irin gidan da muka je neman aure,gida ne na gaske ba gidan k'aranta ba,gwargwadon yadda za muyi harkar girma muma haka za'a yi mana" Mama ta gyad'a kai ta d'auki wayarta ta fara lalubo number Waleed,time d'in shi kam yana zaune office d'insa abun duniya ya ishesa,ya dafe kansa da yake mugun damunsa da ciwo tsabar damuwa da rashin baccin da baya samu cikin kwanakin,ya d'ago a hankali ya kalli wayar ganin sunan Mama akai gabansa sai da ya fad'i,but ya daure ya d'auka ya kai wayar kunnensa,kafin ma yayi magana Mama tace "hello Waleed!" Yayi shiru yana jira yaji me za tace,tace "kana jina?" Ya daure yace "ehh ina saurarenki" tace "yawwa! Dama ina son sanar maka za ka k'aro wasu kud'in,wanda ka bayar baza su isa ba,so ka k'aro mana wasu a k'arasa siyayyan dan ko boxes d'in da za'a zuba kayan ma ba'a siya ba har yanzu" still yayi idanunsa sun yi wani ja saboda tsabar ciwon da kansa suke masa,ya lumshe idanunsa a hankali yana messaging forehead d'insa da d'aya hannunsa yace "yanzu Mama kamar nawa kuke nema?" Wani murmushi tayi tace "yawwa d'an albarka,idan ka bamu ko 2.5 ma it's ok nake ga" bud'e idonsa yayi saurin yi da wani mamakin da ya bayyana fuskarsa yace "Mama 2.5 fa?" Tace "ehh mana,kai yanzun za kaso muyi harkar k'aranta ne?" Yayi shiru shi dai bai ce mata komai ba,tace "Ko baka san y'ar waye na nema maka aurenta ba?" Ya girgiza kansa kad'an yace "not at all Mama,amma ba kya ganin kud'in sun yi yawa? Me za'a saka ne haka a lefen?" D'aure fuska tayi tace "ka ga Malam i don't want any complaints,idan za ka turo min kud'i ka turo ban nemi muyi wani dogon magana ba,idan an gama had'a kayan ai za ka gani ko?" Ajiyar zuciya yayi yace "Mama ni fa ba wai kud'in nake jin fitarsu ba,auren yayi albarka shi ne burina,at least yanzun idan na tura miki 2.5 aka had'a lissafin da wancan gurin 6ml fa,sai kace dai wanda zan siyi y'ar mutane" a hasale Mama tace "ka ga Malam za ka turo min kud'i mu k'arasa siyayya ko a'a?" Yayi shiru ya kasa ce mata komai,a fusata tace "idan ma baka sani ba ka sani kud'inka kaf a siyayyarka suka mutu,sisin kobo bamu ci maka ba,da kake jinjina adadin kud'inka,banda ma abu irin naka idan ban k'ara maka ba ai bazan rage ba,kuma a hakan ma ba komai da muka yi list muka siya ba,so idan za ka tura min kud'i to if not kuma ka fi kowa sanin abunda zai iya biyowa baya" jikinsa ne ya d'an yi sanyi saboda furucinta sosai ya fahimci inda maganarta ya nufa,a hankali yace "shi kenan Mama i'll send" tace "ko kai fa.." Daga haka shi dai ya kashe wayarsa,bai sake jira yaji abunda za ta kuma cewa ba,cikin takaici ya ajiye wayar abunda bai tab'a yi ba ya fara mita shi kad'ai "haba da Allah sai kace na ce ki siya min yarinyar,ko basu isheku ba sai dai ku san yadda za kuyi kuma daga haka na gama wanda zan iya,wannan ma ai duk fariya ne da son nunama duniya kai ga wani isashshe.. If possible sai a fasa auren dama ai bance ina son yarinyar ba.." Yana maganar yana mata transfer,ya gama ya danna wayar a flight mode,wunin ranar bai masa dad'i ba sam,motsi kad'an ya tuna sai ya ja tsaki yayi k'wafa,al'amarin Mama ya gama kaishi iya wuya,duk hakur'insa yau dai ya fara jin zai iya yi mata musu idan ta sake zuwa masa da wani bidi'ar. Cikin sati guda Mama ta kammala had'a lefe,al'amarin kai da gani za ka san anyi k'arya ta wuce hankali,akwatunan kansu da aka zuba kayan sun isa abun kallo bare kayan ciki,dan ak'alla kayan sawa kad'ai sai da suka zuba kala d'ari a cewarta ma sun barsu haka ne gudun magana,da Waleed ya saki bakin aljihu so tayi tayi 200 amma an barshi haka dai gudun bakin mutane,ta san a haka ma ba fita za tayi ba dole ayi surutu,ko da take sanarma Waleed an gama had'a kaya ya kamata ya duba ya gani,yayi murmushi yace "Mama ni kam ba sai na gani ba,wannan aikin na ku ne,idan akwai abunda bai yiba ma ba ni zan gani nace baiba" tace "amma dai ai yana da kyau ka bud'e d'in ka gani ka san inda kud'inka suka narke,kafin a wuce da su ko?" Yace "Mama yanzu dai sauri nake ina da important aikin da zanyi,kawai ina ga ba sai kun tsaya jiran sai na gani ba ku kai musu" tace "to ka tsaya na nuna maka mana" yace "please Mama later" ba yadda ta iya da shi dole tana kallo bayan ya bata uzurinsa ya fice,ai kam ta ji haushin k'in tsayawa ya gani d'in da baiba tace "dan ubanka da ni kake zancen idanma bak'in cikin kud'inka kake babu yadda za kayi dai kaya ne an riga an gama had'asu me ya rage kuma?" Ko da take bawa Hjy Izzatu labarin dariya taita yi itace ma ta d'an kare Waleed d'in tace "haba aminiya ya kamata ki masa uzuri fa,da wanne kike so yaji ne hidimomin akwai yawa fa? Kuma kin san su maza ma ai ba kamar mu mata bane,wani ganin lefe su sam ba damunsu yayi ba,ko cikin mu matan ma akwai da yawa da basu iya tsaiwa su lissafa kayan lefe ba" Mama ta kyab'e fuska tace "ehh to kuma dai da k'amshin gaskiya a maganarki." Har ana saura kwana biyu a kai lefe sannan Mama ta aika ma mother ta zo taga kayan kafin a kai shima kuma da biyu tayi haka,mother cikin jin dad'i tace "kuce zan shigo anjima in sha Allah,ina mata Allah sanya alkhairi" Deejah ta fita tana yatsina fuska tace "toh" bayan fitarta mother ta fara kiran Waleed da yake d'an gidanta ne tun yana k'arami duk da Mama ta sha dukansa akan shiga gidan mother da yake yi amma sau da yawa bai ji,tana gama dukansa ne ya fita zai shiga,ya d'auka da sallama mother ta amsa masa suka gaisa,cikin barkwanci tace "son kuma sai dai naji batun aure haka kwatsam babu sanarwa bare nayi tanadi?" Ajiyar zuciya yayi yace "i'm sorry mother,wallahi idan nace miki nima ban san maganar auren ba sai cikin kwanakin nan kada kiga laifina!" Mother cikin mamaki tace "toh! Kaima da kake ango baka sani ba,bare kuna mu y'an gayya?" Yace "Mama take shirinta,sai da ta gama nemo auren ta sanar min" mother dai duk ta shiga tunanin wannan wane irin neman aure ne haka da mace ce take nemowa ba iyaye maza ba? Suka gama magana da shi,da yake fahimci a damuwa yake taita lallashinsa tana sake k'arfafa masa guiwan yayi hak'uri yama mahaifiyarsa biyayya,yayi mata godiya kafin suka yi sallama suka ajiye wayar a tare. Da yamma mother ta sab'a autarta Hafsat a kafad'a ta fito gidan,ta hango su Manar suna fitowa daga gidan Dadda,ta d'an jira su a balcony har suka k'araso,Manar ta kalleta tace "mother unguwa za kije ne?" Tace "a'a zan shiga gidan su Aunty ne ganin lefen Yayanku" washe baki Manar tayi tace "muzo mu raka ki?" Wani kallo mother ta mata tace "ban ce ba,maza ku shiga ku jiremin gida na bar su Mu'awiyah kada suga ba na kusa sumin iya shege a gida" Manar tace "dan Allah mother mu biki kinji?" Wucewa tayi tace "bance ku biyo ni ba,da me yasa baku je kun gani ba sai dani saboda ga sa'ar ku ko me kuka maida ni?" Haushi ya ishi Manar da taji mother tace haka nan da nan ta cika tai fam,Ameerah ta kalleta tasa dariya tace "mother sai kin dawo" ta amsa tayi gaba tana hararan Manar,tana ganin mother ta bar gurin ta bi Ameerah da gudu,suka kasa tsere a compound d'in gada nan har part d'in Dadda,garin guje²nsu suka buge Waleed dake shiga parlon,ya kallesu a fusace ya musu tsawa "wane irin shirme ne wannan kuke yi?" Babu shiri suka nutsu suka bashi hanya,ya banka musu harara ya wuce,sum² suka yi suka wuce ciki,za su k'ule d'aki ya kira Manar,ta dawo ta zauna kusa da shi,ya zuba mata ido yayi shiru ya kasa cewa komai,a hankali tace "Yaya wai mene ne?" Ya sauke numfashi yace
Chapter 54 · 0% Book details