← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 184

Sashe 107

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mommella dai ta gaji da sauraren Abba suyi magana tace "toh Yaya ga mu mun had'u ku mana bayanin abunda ke faruwa" Abba yayi murmushin k'arfin hali yace "Waleed da sauran yara muke jira" ba'a d'auki lokaci ba aka bud'e k'ofa Amaar da Waleed suka shigo parlon,Amaar a forefront sai Waleed dake binsa sanye da fari kal d'in shadda sai walk'iya yake though fuskarsa babu walwala,kallonsa Abba da Daddy suka dunga yi ya nemi gefen da Amaar ya zauna yama kansa guri kansa a k'asa ya gaishe da iyayen nasa gaba d'aya da ladabi suka amsa,Abba ya kalli Aunty a hankali yace "go and get Ameerah and Manar!" Aunty ta mik'e ta fita,gaba d'aya ta gama shiga comfuse gani take ba alkhairi za su ji ba. Aunty na gaba Manar da Ameerah a bayanta sun sha hijab har k'asa,tunda suka tunkari b'angaren Dadda Ameerah ke addu'ah,a hankali ta tab'o Manar tace "sis wai me yake faruwa?" Manar ta girgiza mata kai kamar za ta fashe da kuka tace "i don't know,ni dai gabana ke fad'uwa ma" Ameerah ta rik'e hannunta da sauri tace "nima haka.." Ameerah dai sai kallon Manar take fuskarta da damuwa tace "Allah sa alkhairi ne" Manar ta langab'ar da kai tace "ameen.. But jikina bai fad'a min haka ba ni dai" a haka suka shiga parlon Dadda dake cike da mutane,Aunty ta zauna inda ta tashi,Manar da Ameerah suka zauna kusa da k'afarta,babu wanda ta iya d'agowa a cikinsu bare ta ga mutanen dake cikin parlon,Mama dai har ta fara sakin murmushi tana k'iyasta how al'amura suka faru,dan yau shi ne datelined da mutumin ya basu komai zai faru,gaba d'aya ta kasa boye how happy she is a wajen duk da yanda take ta k'ok'arin dakewa,tunda su Manar suka shigo da Aunty Waleed yake kallonta ko k'iftawa ya kasa yi gabansa bai bar fad'uwa ba,Abba ya bud'e taro da addu'a sannan a hankali yace "dukkan mu da muka ga mun had'u nan kusan zance magana ne guda d'aya ya tara mu,soboda haka ina ganin babu amfanin mu tsaya jan zance ko wani b'oye²,and then ina son kowa a nan ya d'auki abunda ya faru matsayin k'addara wanda aka ce ta riga fata,mu duka idan da za mu tattara mu zama abu guda bamu isa canja abunda Allah da kansa ya hukunta ba,so kana naka Allah yana nasa,nasan kuma shi ne dai²,dan haka sai mu k'ara gode masa saboda shi kad'ai yasan dai².. A tak'aice ba tare da na tsawaita ba,abunda nake son sanar da ku shi ne,game da maganar auren Zainab an d'an samu chanji,ba wai ina nufin an fasa auren nata ba kwata²,a'a da shi Azaan ne dai Allah bai hukunta za'ayi ba.." Kaf occupants d'in parlon babu wanda bai kalli Abba ba saboda shock d'in da maganarsa ya basu,ciki kuwa har da Mama dake jan salati tana zaro idanu, underneath hamdala take Azaan bai auri Manar ba,kamar abun ya dameta sosai tace "toh! Bai aureta ba shi wa kuma ya aureta? A kan wane dalilin shi kuwa zai fasa auren? Me yake faruwa haka?" Dadda dai kallonta kawai take tayi mitsi² da idanuwa ta k'i cewa komai,rik'e k'afar Aunty Manar tayi ta fashe da wani kuka mai ban tausayi,Mother dai bata iya d'aga kanta ta kalli kowa ba,ita kanta hawaye take a b'oye tana maimaita fad'ar "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. Allahumma ajirniy fiiy musibatin wa'aklufniiy khairan minha.." Aunty dai itama hawayen take tana fad'an "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,me yake faruwa Alh?" Amaar yayi k'asa da kansa bai iya ya kalli mutanen parlon ba duk da ya san komai amma jikinsa yayi mugu sanyi ba kad'an ba,Waleed dai sai kallon Abba yake ko k'iftawa ya kasa yi zuciyarsa tana bugawa da sauri²,Daddy yayi k'arfin hali yace "duka hak'uri za muyi,we never saw this coming,komai ya samu bawa a duniya dama rubutacce ne,babu wanda ya isa ya kaucewa k'addararsa,wannan yaron fa ba cewa yayi bazai auri y'armu ba,wani abu yaga yana shirin faruwa ya samemu ya mana bayani tun kwanaki biyu da suka wuce,mu kuma da kanmu muka ga dacewar yanke hukuncin da muke ganin zai fi zama mana alkhairi,ya nemi chanji daga garemu mun basa,so duk banga abun tada hankali a nan ba,idan mun kalli maganar da idanun baseera.. Sai muyi addu'ah Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi gare mu baki d'aya.." Hayaniya parlon ya fara d'auka,Abba yace "ya isa dan Allah ku bari mu gama abunda ya taramu kafin ku samu abun fad'a.. Shifa aure ba'a yinsa dole,kuma duk abunda bai faru ba,dama Allah ya rubuta ba mai faruwa bane,babu ruwan ku da wasu k'ananun maganganu,zan k'ara jan kunnenku duka,ban amince wani ko wata ya tada maganar nan a ko ina ba,yanda muka yisa a nan a nan nake so kowa ya barsa,Allah sa hakan shine mafi alkhairi ga y'ay'anmu,abunda yaron nan ba kunyata mu yayi ba,shi ba cewa yayi ya fasa auren y'armu ba,and bamu baro masallaci ba sai da na tabbatar na fitar da mu kunya na d'aura masa aure da tawa 'yar saboda saka masa halaccin da ya mana,na had'asa da yata wanda nake da iko da.." Lokaci d'aya mutanen parlon suka sake bin Abba da kallon tsartsar mamaki,kowa ya kasa kunne jira yake yaji da waye akayi auren,sannan mene ne makomar Manar,ita kanta Manar kallon Abba take zuciyarta tana wani bugawa,Mama ta had'iye yawu da kyar tana kallon Azaan da kansa ke k'asa,ji take jikinta yana wani shaking ta ciki dan wannan shi ake kira anyi ba'ayi ba,tunaninta wace yarinyar aka aura masa kuma? Dan it's da Deejah ko Diyanah taso had'asa,Waleed dai sai kallon Abba yake zuciyarsa kamar za tai skipping ta fito waje saboda yanda yake harbawa,Abba yana kallon Dadda da itama idanunta suke kansa tana kallonsa,da wani confidance a maganarsa yace "na d'aurama Mamana aure da Waleed,Azaan kuma na masa canji da Ameerah,saboda wasu dalilai wanda ba sai na fito na sanarma kowa ba ko na bayyanasu,na tabbatar zai rik'e min 'yata da amana,sannan banyi haka ba sai da nayi shawara da d'an uwana da kuma mahaifiyarmu.." Wani zabura Mama tayi ta mik'e tsaye tana kallon Abba da wani irin shock,Mother dai bata ce komai ba,lokaci d'ayq ta tsayae da hawayen da suke zubo mata jin da wanda Abba ya d'aurawa Manar aure ya sosai maganar ya samar mata da relief kad'au suke sakko mata,even though ta girgiza da farkon but lamuranta duka ga Allah take mik'a su shisa sai bata wani damu ba,Mama ta k'arasa gaban Abba cikin kid'imewa bakinta yana rawa haka ma ko ina na jikinta tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.. La'ilaha illa anta subhanaka inniiy kuntu minaz'zalumiiyn,dan girman Allah Alh ka min banyani yanda zan gane,wallahi ban fahimce ka ba,ban gane ba sam kwakwalwata ta dod'e ba na iya fahimtar maganarka,wane Waleed d'in kama aure? 'Da na kake nufi? Wanda na haifa da cikina? Ko kuma wani mai irin sunan ka samu? Kayi min bayani don girman Allah Alhaji" Mommella dai da duka sauran occupants d'in parlon da kallo suka binta ganin yanda take hauka tuburan sun kasa d'auke idanunsu daga kanta,Mommellah dai ta yi tagumi sai kallon Dadda data tsume fuska ta k'i cewa komai take,Manar kam sai lokacin ta gama fahimtar abunda Abba ya fad'a few seconds ago,tun bayan maganarsa komai ya tsaya mata,ta daina fahimtar abunda ake fad'a,da kyar ta gano me yake faruwa da ita bayan ta gama tattara maganganun Mama,can ta juya a hankali ta kalli inda Waleed yake zaune,ganin ya rufe fuskarsa da palms d'insa ba ka iya gane wane irin yanayi ne akan fuskarsa ta sake duk'ar da kanta,ko da Abba ya tambayeta tana son Waleed k'asa magana tayi,Mama ta durkushe kan knees d'inta ta fashe da kuka,gaba d'aya ta birkice bata ma san inda take ba,Aunty dai sai murrmushi take cikin farin ciki tace "lallai alk'awarin Allah tabbatacce ne.." A hankali Waleed ya zame hannunsa daga fuskarsa da ya rufe yana kallon Mama da idanuwansa da babu komai cikinsu face zallar farin ciki,Abba ya waiga yana kallonsa yace "kana son Manar?" Sai da ya d'an kalli gefen Mama kafin ya gyad'a kansa a hankali,lokaci d'aya kuma ya mik'e ya fice daga parlon without ya bari Mama ta ga fitarsa,tafiya yake yana k'ara godema Allah a fili,fuskarsa ta kasa b'oye how happy he is,ranan yau jinta yake kamar an masa gafara,da Afiyah ya fara gamuwa za shi parking space,tayi masa murmushi tace "good afternoon D" bai ko tsaya bin ta kanta ba ya wuce ya bud'e motarsa ya shiga zai rufe ta rik'e murfin motar tana kallonsa tace "D wai me yake faruwa,na shigo nake jin rumors kamar wai ko an fasa auren,what's happening?" Bai tanka ta ba ya sake kai hannu zai janyo murfin motarsa,da sauri tana binsa da wani kallon mamaki tace "me kake wa murna haka D?" Murmushin da bata tab'a ganin ya yi ba ya sakar mata a hankali yace "kije ciki babu komai,i'm going out for a little bit" sosai taji dad'in murmushin da ta gani kan fuskarsa because tun da suka yi aure bata tab'a ganin murmushinsa kamar haka ba sai yau,sanda ta fara mayar masa da murmushin kafin tace "toh dear! But akwai bikin ne har yanzu?" Ya d'an gyad'a mata kai kafin yaja murfin data sakar masa ya rufe ya tayar da motarsa ya fice daga gidan,haka nan bayan fitarsa yaita zaga garin yama rasa ina zai nufa,Afiyah tabi motarsa da kallo tana murmushi then ta juya tana d'aga shoulder ta wuce cikin gidan dan amsa kiran da Mama ta mata,kafin ta k'arasa ta hangota tana tahowa hankalinta kamar baya jikinta,a rikice Mama take kallonta tace "Afiyah shi kenan asirinmu ya tonu.. Mun shiga uku mun lalace.." Da mamaki Afiyah take kallon Mama tace "lafiya? Me yake faruwa?" Gaban Mama sai fad'uwa yake,tayi still tana kallon Afiyah zuciyarta yana bugawa,Afiyah ta sake cewa "wai me yake faruwa ne,kimin bayani?" Cike da k'arfin hali Mama tace "sun munafurcemu wallahi.." Sai kuma ta sake fashewa da matsanancin kuka cikin tashin hankali tace "wallahi bai isa ba.." Ta juya da sauri ta koma cikin gida tana goge hawaye bata saurari Afiyah ba,tana shiga bedroom d'inta ta fara kiran Waleed jikinta sai b'ari yake,Waleed dake driving ya kasa controlling tears dake zubowa fuskarsa saboda farin cikin da yake ciki ya
Chapter 107 · 0% Book details