Sashe 57
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana kallon wani guri yace "me kike tak'ama da shi?" Tayi dariya tace "kai baka san da me nake tak'aman ba?" Ya tab'e baki suka yiwa juna shiru,shi yana tunanin makomarsa a gurin Mama,ita kuma wani farin ciki ya mamaye zuciyarta ganin Mama ta sa shi dawowa and ba tare da yaran d'azu ba,gaba d'aya ta k'uresa da idanu tana k'ara kallon how cute he is tana hango yadda za ta ja zarenta cikin colleagues d'insu,duka team d'insu y'ay'an manya ne,daga governors,president,ministers sai y'ay'an manyan ma'aikatan gwamnati,kaf babu d'an wani mai k'aramin matsayi a cikinsu,haka samarinsu duka y'ay'an manyan gwasake ne,ita kad'ai ce kusan za'a ce ta fita daban but duk da haka shima ba wai matsayi ne baida shi ba,mahaifinsa ne dai bai taka wani matsayi a gwamnati ba but da yawa sun san wane ne field marshal na wannan lokacin,dole za'a san matsayin Waleed a gurinsa kasancewarsa k'ani a gurin Abbansa,sosai ta shagala da kallonsa sanda yaga ba ta da niyyar magana yayi siririn tsakin da ya dawo da ita hankalinta,fuskarsa a daure yace "ba na son kallo.. And idan za kiyi magana ina jinki if not kuma zan tafi and don't ever think wai ni zan sake dawowa nan,ba Mama ba ko waye za ki fad'ima sai abunda naga damar yi,fahamtiiy?" Dariya tayi tace "yanzun wai sai ka sake tafiya?" Ya mata banza,tace "alright! Bari na fad'a ko kada naita wahalar da angona" kamar ta caka masa mashi haka yaji kalmarta,cike da isa tace "maganar tsare²n biki tunda kai baka ce komai ba har yanzun,and bama ka tab'a zuwa ba bare na san abunda ya dace,that's nace Mama ta turoka muyi maganar because ni ban fad'a musu baka tab'a zuwa ba" ya wani d'age kai yayi fuska kamar ma ba da shi take magana ba,sanda tace masa "yanzun ya kake gani za ayi?" Strictly yace "kinga Malama ba abunda ya kawo ni kenan ba,ina ga ki had'a maganarki guri d'aya ki fad'a amsa d'aya nake tunanin zan iya ba-ki a duka maganar ki,so if u're ready go on.." Wani kallo ta dunga binsa da shi kafin tayi murmushi tace "D duk fa kafin muyi aure ne kake min wulak'ancin nan" shi dai bai tankata ba sanda ya d'auki mintuna biyar,yaga ta k'i magana kawai ya bud'e motarsa ya shiga ya sauke glass d'in kad'an cike da aji yace "idan kina da wani maganar da baki fad'a ba just give me a call ko ki tura min sak'o,ok bye.." Ya mayar da glass d'in ya rufe,tsaye tayi tana kallonsa har yayi zooming off ya bar gidan,yana fita ta kira Mama a waya ta sanar mata ya tafi basu gama magana ba,Mama cikin fad'a tace "wane iskanci kenan haka?" Tace "And he said duk abunda nake buk'ata kada na kirasa na tura masa text" Mama cikin jin haushi tace "alright! Kada ki damu zai dawo ya same ni" bayan sun gama waya,Mama ta fara kiran Waleed but abun mamakin wayoyinsa a kashe,ta gyad'a kai tace "da ni kake zancen za ka shigo ka tarar da ni.." Waleed kam cikin kwanciyar hankali yayi parking bakin get dan ma kada Mama taji alamun shigowarsa ya san dole tana da masaniya akan abunda ya faru tsakaninsa da Afiyah,ya rufe motar ya fito ya shiga gidan da k'afarsa,direct ya nufi gidan Dadda dan can kad'ai yake zaunawa ya samu nutsuwa babu hayaniya babu takura da fad'an Mama,yana shiga Dadda tace "kai kuma fa?" Ya kalleta ya wuce ya zauna kan kujera,sai lokacin yaji zai iya mata magana yace "me ya faru?" Tace "yo na ga kun fita da su sun dawo suna fushi,kai d'in ina ka tsaya?" Ya d'auke kansa yace "ina ruwanki da inda na tsaya? Ko dai kin fara saka min ido?" Harara ta wurga masa ta tab'e baki tace "Allah ga ni.. In ji kishiyar mai doro,kai dai wannan mutumi ba ka da kirki ko d'is,dan ka ga za kayi aure ko,shi ne kake kwab'a min magana,to Allah ya so dai kafin kayi nima na yi auren bare ka gwada min iya shege.." Murmushi yayi bai sake mata magana ba ya d'auki wayarsa da ya jefa flight mode yana kallon pics d'insu na d'azun kafin su fita,sosai ya shagala da kallon pictures d'in Manar da ta fito d'aki tana video call da Azaan ta wuce kan kujera ta kwanta tace "Yaah Azaan Allah ni dai ban yarda ba" yace "yanzun ya kike so ayi?" Tace "kawai ka taho tare da Mommella ni dai ina son ganinka" dariya yayi mai sauti yace "banda ganin da kike min yanzun har wani kike buk'ata?" Ta gyad'a masa kai a shagwab'e tace "ai wannan a waya ne ni dai kawai ku taho tare,ka ji?" Yace "no way Guddi akwai ayyuka sosai gaba na" ta marairaice tace "to ni dai Allah idan baka zo ba zan daina kulaka" ya zaro ido yace "me yayi zafi gemu zai ci wuta?" Dariya ta kyalkyale da shi tace "ba sai asa masa ruwa ba" yayi murmushi yace "ni dai ki bar maganar zuwan nan ba zan samu dama ba" haushi taji sosai cikin muryar kuka tace "to kada ka zo d'in Allah na daina kula ka ma daga yau.." Tana fad'ar haka tayi disconnecting,cike da jin haushi ta jefar da wayar gefenta tana jan tsaki,kamar ance ta d'ago kanta suka had'a ido da Waleed ya kafeta da wani mugun kallo fuskarsa kamar za ta tsage tsabar b'acin rai,ta murgud'a masa baki ta d'auke kanta dan shima d'in haushinsa take ji,bai iya ce mata komai ba ya mik'e a fusace ya fice daga gidan,ta bisa da kallo tana tab'e baki a hankali tace "za kayi za ka gama." Tun daga ranar da ya fita gaba d'aya bata k'ara saka shi idonta ba,ya daina shigowa gidan,kullum suna zuwa skul da su Deejah da yake ba ta kulasu sai ta kasa tambayar yana nan,yayin da a gefe d'aya rashin ganin san yake mugun damunta,har zuciyarta take jin damuwa da rashinsa but duk ta tattara komai ta ajiye gefe,ba ta son kiransa saboda ba ta san uzurin da ya hanasa zuwan ba,ranar alhamis lokacin saura kwana uku bikin wajen 6pm sun taso islamiyya,haka nan ranar suka jin tafiyar k'afa ita da Ameerah suna tafiya suna hira da yake ranar drivern nasu Mama ta aikesa,and su kad'ai ne Deejah basu je ba suna hidimar biki,suna tafiyar motar Waleed ya giftasu da mugun gudu ya wucesu lokacin ko nisa da makarantar ma basu yi ba,bin motar da kallo suka yi Ameerah tace "Laaa! Kinga Yaya ya wuce mu,dama ya tsaya ya k'arasar da mu gida wallahi na gaji" Manar tayi shiru tabi motar da kallo bata ce mata komai ba har suka zo bakin get d'insu suka shige ciki,suna tafiya compound za su wuce gidan Dadda,Manar ta juya ta kalli parking space d'insu Waleed,ai kam nan ta gansa tsaye jikin motar da ya shigo da shi yana waya yana murmusawa,haka kawai taji wani haushi ya sake ciyota a fusace ta wuce bata tsaya ba,da kuka ta shiga gidan ko ta kan Dadda dake zaune parlor bata biba ta wuce d'aki da gudu tana rafzar kuka,Dadda dake hira da Tasallah k'awarta da tazo biki suka saki baki suna kallonta har ta shige,Ameerah ta shigo da sallama bayan ta gaisar da su ta wuce da niyyar zuwa ta cire uniform d'inta tana shiga Dadda ma ta shigo,taga Manar kwance sai kuka take,hankali tashe ta k'arasa tana salati ta d'ago ta a rikice tana tambayarta "me aka maki kike kuka ni jikar laraba? Wani malami ne ya bugar min ke yanzu na d'au gyalena mu koma?" Da sauri Ameerah ta tari numfashinta tace "babu wanda ya doketa fa" Dadda tace "Iiiiiihhh! Idan ba dukanta akayi ba me zaisa tayi irin kukan nan na fitar rai? Ni dai gaskiya ba'a kyauta min ba wallahi sam,haka kawai a dunga sa min yarinya kuka ana cutata,koma uban waye yaje shi da Allah,wallahi ban yafe masa ba.." Ameerah tace "Hjy ina jinfa Yaya da muka gani ne bai d'auko mu ba ya barmu muka taho da k'afa" Dadda tayi mitsi² da ido tace "waye kuma haka?" Ameerah tace "Yaya Waleed" tace "ganinsa kuka yi shi mutumin?" Ameerah tace "ehh! Muna fitowa islamiyya lokacin an tashi shi ne to ina jin da bai tsaya ba,yanzun kuma muna shigowa muka ga ashe gida ya taho,ina jin shi ne dalilin kukan nata" cikin jin haushi Dadda tace "shi Mamman d'in ne yak'i tsayawa ya d'auko min ku?" Ameerah tace "ehh!" Dadda ta girgiza kai tace "ni wallahi ban san yaushe Mamman ya zama haka ba,bak'in ciki da mugun halin uwarsa ban san sanda ya kwafesu ba.. Amma bari naje na samesu har shi har uwar tasa naji ko ita tace idan ya ganku kada ya rage muku hanya" ta fita tana mita,Tasallah dake zaune ta d'aga kai tana kallonta ganin ta nufi hanyar fita da sauri tace "to ina kuma za kije kike sauri?" Dadda ta waigo a masife tace "kyale ni dai naje bin ba'asi,idan ba bak'in ciki da mugun hali ba,wai ace kamar Mamman ne zaiga yaran nan suna tafiyar k'asa ya kasa d'auko su sai dai su zo sugansa a gidan" Tasallah tace "a'a wannan dai ba halin k'warai bane gaskiya,kuma Waleedi dai na san bazai musu haka ba sai dai in zugasa aka yi ya walaak'anta su" Dadda tace "Uhn! Nima dai sai da nayi wannan tunanin,amma bari naje dai naji ko Asama'u ta hanasa d'auko su" da sauri Tasallah ta mik'e tace "ai kuwa dai nima banga ta zama ba wallahi muje kinji mubi ba'asi" suka fita suna mita,Waleed da har lokacin yake tsaye gurin da su Manar suka barsa yana ganin shigarsu Dadda gidansu yace "we'll talk later" ya katse kiran ya wuce gidan Dadda fuskarsa a d'aure,ko da ya shiga bai tarar da su a parlor ba ya wuce bedroom da yake jiyo maganar Ameerah sama²,yana tura k'ofar suka waiga tare idanun Manar sunyi ja tsabar kukan da tayi sun d'an tasa,Ameerah ta gaisheshi ta nufi k'ofa ta fice,tsaiwa yayi door way yana kallonta,ta d'auke kanta tana sake share guntayen hawayen da suke mak'ale idonta,a hankali ya kalleta yace "me aka miki kike kuka?" Ta masa shiru ta k'i ba shi amsa,yayi k'wafa yace "ba dake nake