Sashe 60
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amaar ne ya kula da tsaiwan da tayi ya d'an kalleta kad'an yace "k'anwata ya kika tsaya?" Tayi murmushin yak'e tace "babu komai" yace "really?" Ta gyad'a masa kai tace "absolutely sure" yace "okay! Think ko da wani matsalar ne" ta girgiza masa kai tace "a'a" harararta Ameerah tayi tace "ke dai sis wallahi kada ki tsaya b'ata mana lokaci,kin san dai we are about to leave ko?" Jikinta a mugun sanyaye ta b'alle bundle d'in kud'inta za ta fara masa lik'i,ba tare da ya kalleta ba ya motsa lab'b'ansa kad'an yace "don't dare.." Ita kad'ai ta jisa ta d'ago da sauri idanunta sun cika taf da hawaye seeing that ita kad'ai ya hana ta masa lik'in kaf cikinsu ta zuba masa idanunta da suka ji maskara gashin idanunta sunyi wani gazar kamar ta k'ara,da muryar kuka tace "Yaya!" Ya d'aure fuskarsa sosai ya kalleta babu alamun wasa yace "what?" Tace "me yasa sai ni kad'ai za ka hana nayi maka?" Fuskarsa a tamke yace "waye yace ki tambayi Azaan ya baki kud'i?" Wani irin kuka ne ya fara neman kwace mata tace "Yaya ni fa ban tambayesa ba" yace "k'arya zan miki kenan?" Ta girgiza masa kai tace "Yaya believe me ni bance masa ya ba ni ba fa,shi ne kawai yaga dama ya ba ni" ya d'auke kansa yace "okay! Yayi maki kyau" daga haka sai bai sake mata magana ba,Azaan da gaba d'aya bai niyyar zuwa inda suke ba tunda ta bar kusa da shi idanunsa suke kanta,haka kawai da yaga suna magana ya dunga jin zuciyarsa babu dad'i seeing her a tsaye sai jujjuya kud'in hannunta take yi kamar wadda aka girke ya mik'e a nutse ya nufi stage d'in cikin takun k'asaita,yana k'arasawa kusa da su ta gefen idanunsa ya kalli Waleed fuskarsa a d'an had'e ya matsa daf da Manar da ta zama kamar statue,ya rage tsayinsa kad'an dai² kunnenta yace "don't cry Guddi" saurin kallonsa ta juya tayi wani kuka yana sake taho mata,ya girgiza mata kai da sauri,da kyar ta daure ta had'iye kukanta,yace "tell me what happened?" Da muryar kuka tace "Yaya ne" yace "me ya had'a ki da shi?" Tace "wai kada na masa lik'in,kuma ni kad'ai ya hana na masa" wani murmushi Azaan yayi yace "okay! Let's dance ko sai mu wuce gida" a hankali ta gyad'a masa kai tana satan kallon Waleed da kad'an bai had'iye zuciyarsa a gurin ba tsabar kishin da yake cin ransa,yayi mata murmushinsa yace "smile please!" Murmushin tayi masa,yace "pyaar hain tumse (I love u)!" Wani dariya tayi ta rufe idanunta da palms d'inta biyu cike da jin kunya tace "Me too" suka tsaya gaban Waleed sai wani k'us² suke wanda tsaban yadda ya kasa kunnensa clearly yake jiyo su duk uban kid'an da ya cika gurin,tare da Ameerah da Amaar suka dunga rawan,Azaan sai spraying yake musu yana mata murmushi kamar bai jin fitar kud'in a jikinsa,nan da nan ta saki jikinta sosai yanayin ya mugun yi mata dad'i ta sake cikinsu tana rawa,kud'in hannunta k'arshe Azaan da su Ameerah tama lik'i da su,yayin da gaba d'aya suka zama abun kallo a hall d'in,MC ya ga yadda Azaan yake masa b'arin kud'i tuni ya koma wasa Prince Azaan Jarood ibn Maqbool,mutane sai wani video suke musu,kada kuso ganin yadda fuskar Waleed ya koma lokacin,da kyar ya danne b'acin ransa aka tashi gurin,lokacin su Manar sun fita za su tafi gida Waleed ya fito cikin sauri zai tafi shima dan suna barin gurin yaji bazai k'ara iya ko da minti guda ba,akan idanunsa motar su ta bar gurin ya had'iye wani mugun yawu kafin yayi following d'insu zuwa gida. A parlor lokacin da suka shiga part d'in suka tarar Dadda sai mita take ma aminiyarta Tasallah,suka k'arasa ciki suka zauna suna hira k'asa² suna kuma sauraren su Dadda,Dadda tana kallon Tasallah tace "kaiii³ yanzu Mamman ya rasa wanda zai aura sai zabiya? Dan Allah Tasallah ki gane min wani had'in gambiza a nan gurin,wani fari fauu abu babu ko kyaun gani haka" Tasallah tace "haba Malam! Nima dai sai da nayi wannan maganar,to wai dama Azumi bai tab'a kawo maki ita ta gaisar dake ba ne?" Dadda ta kyab'e fuska tace "ina fa ta tab'a zuwa,da irin su Asama'u a zuri'ar Mamman zai kawo min matar da zai aura? Ni a su wa?" Kame baki Tasallah tayi tace "ai shi kenan.. Kuma su duk wad'annan masu jahannama ga fasinjan dangin amaryar ne?" Dadda ta wani zaro ido tace "huuu mene ne haka kuma?" Tasallah tace "yo kema dai kamar bakya gani,duk baki ga d'inkin da suka yi ba sun d'ad'd'ame jiki anyi wani shaftareren wuya hantsar su duk a waje" Dadda tace "yo Allah na tuba ni kaina ai banyi zaton suna jin hausa ba bare na sa musu ran sun san gabas,kayuwansun nan kuwa kina ga kamar na y'ay'an oduduwa an zuba uban gashin doki.. Kaiii³ abun dai babu ko kyau bare tsari.. Ni dai bari Mamman yazo inji inda ya samo wannan mata da zai aura." Tasallah tace "atooh! Gara dai ki yiwa tufkar hanci kafin ta warware miki da jika,tsakani da Allah kema banda Azumin da abunki duk ki rasa wanda jikanki zai aura sai wannan aba mai kama da an tada akuya tsaye,me yasa baki masa gata kin had'asa da wata a jikokinki ba?" Tun shigowarsu suke dariyan mitar su Dadda wanda fuskarta take nan cike da b'acin rai kamar dai ace mata ga Waleed ta rufesa da balbalin fad'a,suna jin Baba Tasallah ta ce haka duk suka nutsu suji amsar da Dadda za ta ba-ta,Dadda da tayi saurin kallonta tace "wane irin magana kike haka Tasallah?" Tasallah tace "ko Manar d'innan ba kya had'asa da ita ba tsakani da Allah tunda duk ke kika yi wahala da su.." shiru duka suka sake yi suka zuba musu idanu,Dadda ta wani tsuke fuska tace "A'uzhubillahi minashshaid'anir rajiim,wane irin sab'o kike haka Tasallah..?" Waleed da ya shigo gidan a bayansu yayi parking bai nufi ko wane gida ba ya zauna cikin motarsa,ya fara kiran Manar a waya,da yake ita kam wayarta ma duka wunin a silent yake tunma kafin ace sun tafi dinner duk kiran da ya mata bata sani ba tana can sai dariya take ma su Dadda,haushin kin d'aukan da bata yi ba da kishi ya k'ara cikisa a fusace ya bud'e motar ya fita ya nufi b'angaren Dadda lokacin suna tsaka da maganar ya afo ko sallama bai ba ya kalleta yace "ke zo nan" fuskarsa a d'aure ya juya zai fita,wani zaro ido tayi tace "ni Yaya?" A fusace ya waiga idanunsa sun kad'a sunyi wani mugun jaa yace "a'a ba keba ni" Dadda ta kallesa fuskarta a tsuke tace "to me kuma yarinya ta maka?" Ya kalleta da sauri yace "dan Allah Hjy kada kisa mana baki,ita ta san me tayi" ya kalli Manar yace "kada ki b'atan lokaci ki same ni parking space" wani irin tsoro ne ya cikata seeing his face har wani jaa tayi tsabar fushi ta kalli Dadda idanunta suna kawo hawaye tace "ni wallahi bazan je ba" ta tashi da sauri za ta wuce d'aki bata san yana tsaye balcony yana jinta ba,sai ganinsa tayi kamar walk'iya ya dawo ransa a mugun b'ace kafin ta gama shigewa taji an dank'o hannunta an fizgeta,ta juya da sauri taga Waleed za tayi magana ya daka mata tsawa yace "keep ur mouth shut before i hurt u" ta fashe da kukan da dama k'iris take jira tana waigen Dadda,janta ya dunga yi bai tsaya ba sai da suka fice daga gidan,Dadda dai ta kasa masa magana baki sake ta bisu da kallo sanda ya fice da ita daga gidan Tasallah da itama ta rakasu da idanu mamaki k'arara fuskarta ta kalli Dadda tace "Anya Azumi baki yi sakaci ba kuwa?" Dadda da ta kasa dakatar da Waleed tayi saurin kallonta kamar za tayi kuka tace "kuji dai wani magana gurin Tasallah kuma,sakacin me kuwa zanyi ni jikar laraba?" Tasallah tace "fisabilillahi kina kallo ya fita da yarinya ki kasa tsawatar masa,da kin tare shi kinji ina zaije da ita da wannan tsohon daren?" Dadda tace "ni dai zanga ranar da Mamman zai bar sa ni dogon magana,tsakani da Allah duk irin d'awainiyar da nayi da Mamman kawai sai ya dunga azabtar da ni? Gaskiyarki Tasallah zanje yanzu na samu Yaro naji ko shi yake aiko min shi" Tasallah tace "wane dawainiya kuma Allah na tuba? Ai wannan kuma ya tashi a banza tunda kika kasa masa gatan nan,kyaunta ace wannan uban shak'uwar da kuka yi da shi,kin nemar masa aurenta kawai suje can su zauna tare,abunda ma ya fi kowa sanin yarinyar nan,ba shi kenan sai suyi ta haifo maki y'ay'ansu su zube maki kiyi ta bari²n da kika jima baki yi ba,ku dai zumuncin ku duk kame² ne ba shi da wani amfani,banda haka ba sai ayi tuwo na maina ba,ko don Asama'u ta had'iye zuciya ta mutu,shi kenan kin kawo k'arshen k'iyayyar da take ma jikarki da surukar ki.." Tagumi Dadda tayi kamar za tayi kuka tace "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,ni dai yau na shiga uku na ni jikar laraba.. Wai³ gaskiya Tasallah baki yi min adalci ba,ke kin san gagarumin sab'on da kika buga kuwa? Haka kawai muna zaman² mu ki ja mana fushin mahalicci.. Kai wasu dai suna abunda bai dace ba sam" Tasallah tace "Sab'o don na ce Waleedi ya auri y'ar uwarsa? Ke dai Azumi baki son gaskiya,kuma baki tsoron Allah wallahi,anya ba iya bakinki kad'ai kike fad'in kina k'aunar Waleedi ba kuwa?" Dadda da ta wani tsuke fuska tace "ni wallahi duk kaunar da nake ma Mamman,billahillaziiy da ya aurar min jika gwara tayi ta zama ba aure ina kallonta,me zata ci da shi Allah na tuba? Me ake da suruka irin Asama'u,ke ma dai muguwa ce Tasallah,waye kuma Mamman da za ki ce ya aurar min jika? Ina Manar za ta kai wannan kamfacecen mutumi haka amma ke dai wallahi muguwa ce ta bugawa a jarida" kallonta Tasallah ta dunga yi ta kasa cewa komai,tayi k'wafa tace "ai shi kenan ma ji ma gani.." Dadda tace "yo Allah na tuba yarinya ma tana da wanda take so yake sonta,haka kawai ki ja mana masifa muna zaune"