← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 184

Sashe 83

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaune ya tadda Dadda kan rug ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya tana bawa Afiyah labarin irin shak'uwar dake tsakaninsa da Manar,da irin fad'an da Waleed da Azaan suka sha a kanta tun daga ranan da aka haifeta,Dadda na kallon Afiyah da kyau tace "ai ke baki ga ba irin wahalan da suka yi da ita,ga fad'an da suke yi duk a kanta,to ni dai ma godiyan da na yiwa Allah da yasa cikin su biyun d'aya zai aureta,yo Allah na tuba irin sangartar da suka mata ai babu mai iya d'aukan a'alarta idan ba su ba d'in.." Though Afiyah wasn't interested with the story at first,dan yanda gaba d'aya hankalinta yake kan d'akin seeing that Waleed bai fito ba har lokacin,so bata san lokacin da tayi saurin watsoma Dadda tambayar "waye zai aureta yanzu?" Dadda tace "shi dai d'an uwanta na wajen uwarsu Hatsatu" wani kallo Afiyah ta dunga yima Dadda,lokaci d'aya ta fashe da wani dariyar da ita kad'ai tasan ma'anarsa,Dadda ta d'aure fuska tana kallonta tace "Allah na tuba mene ne abun dariya kuma a nan safiyah?" Dariya kawai Afiyah take b'ab'b'akawa,Dadda ta tab'e baki tace "to Allah dai ya kyauta" Waleed dai yayi still bakin k'ofar d'akin sai kallonsu yake ya kasa k'arasowa cikin parlon,Dadda tace "toh kuma abunki da shi wancan d'a dai d'an gidan sarakai ne,baki ga ba dai abubuwa cikin mutunci da girmamawa wallahi.." Katse ta Waleed yayi fuskarsa a d'aure yace ma Afiyah "tashi muje" ita dai sai gyad'a kai take,Dadda tace "ya haka kuma Mamman muna hirarmu kace ta taso ku tafi" Waleed yace "sai ki bari duk sanda kika ga ba na nan kyaje gidanta kuyi hiran.." Dadda tace "meye laifina a ciki Mamman,matar ka ce fa kawai muke hiran zumunci nake bawa labarin wanda zai auri k'anwarka,kuma shi kenan ka fi so mu zauna tana kallona ina kallonta kamar wasu abokan gaba?" Mik'ewa Afiyah tayi tana kallonsa tace "toh Hjy mu za mu koma,wata rana zan zo ni kad'ai in sha Allahu muyi hira sosai" Dadda ta washe baki tace "toh Safiyah shiga ku k'ara yin sallama da Manar d'in ko?" Tuni murmushin dake kan fuskar Afiyah ya d'auke,sai dai bata ce komai ba ta shiga d'akin,ta tsaya daga bakin k'ofa tana jefawa Manar dake zaune bakin gado kallon tsana,Manar ta d'aure fuska ko kallo Afiyah bata isheta ba,Afiyah ta ja tsaki tana yatsine fuska ta fita daga d'akin. Dai² lokacin aka yi sallama bakin k'ofa,Dadda ta mik'e da sauri tana amsawa tace "bisimillah ko waye ma ya shigo mana kuma ya tsaya can waje kamar bak'o" Azaan da Amaar ne suka shigo parlon,Azaan yana sakin lallausan murmushinsa,Dadda ta bud'a idanu tana kallonsa tace "waye wannan kuma nake ganinsa a nan?" Azaan yace "Muhammad ne Dadi" ya mik'awa waleyed dake tsaye bakin k'ofa yana kallonsa hannu,Waleed ma ya mik'a masa hannu still looking at him suka gaisa,suka gaisa da Amaar ma ya masa barka da dawowa,Dadda tana washe baki tace "toh kai kuma yanzu kake tafe Mamman?" Zama Azaan yayi kan lallausan rug dake parlon,Dadda ta kalli Afiyah tace "wanda zai auri Manar kenan Safiya da nake baki labarinsa,tana gama sakandire nan da wata biyu zuwa uku za mu sha biki idan Allah ya ara mana tsayin rai,kin gansa nan wallahi yaro ne mai kirki da sanin ya kamata,duk da yake ya turo likita ya dubata amma bai hak'ura ba ya taso ya taho tun daga wata duniyar" Afiyah tana yima Azaan wani kallo tace "sannu da zuwa" Azaan ya mata godiya yana murmushi,Afiyah ta mik'e ta nufi k'ofa tana kallon Waleed sannan ta kalli Dadda tace "Hjy bari mu barki da bak'in ki sai na sake dawowa" Waleed yayi ma Dadda sallama ya fita Afiyah na biye da shi,sai da suka yi nisa ya tsaya yace "ki jira ni a b'angaren mu ina zuwa,i just forgot to discuss something with grandma" fuskarta da mamaki ta dunga kallonsa kafin tace "toh muje na rakaka" ya had'e rai yace "do as i say,we need some privacy" bai jira cewarta ba ya juya ya koma parlon,ta bisa da kallo har ya shige,Azaan suna zaune parlon Dadda ta kawo masa ruwa da drink Waleed ya dawo,cike da mamaki ta d'aga kanta tana kallonsa tace "kai kuma fa? Ba har kun tafi ba mai ya dawo da kai kuma Mamman.." Azaan ya d'aga kansa ya kalleshi,Waleed ya had'e rai yana kallonta,tace "ina tambayarka kuma ka yi min k'ik'am a tsaye,meye kuma na dawowa bayan mun yi sallama kun tafi?" Waleed dai bai fasa k'arasawa cikin parlon ba ya zauna,Dadda ta ajiyewa Azaan drink tace "toh ai kuma sai kayi ta yin shirun,mutum dai kamar gunki kayi masa magana yayi maka bakam alhalin yana jinka" Azaan ya d'auke kansa daga kallon da yake ma Waleed,Waleed dai bai ce mata k'ala ba,ta gaji da mitarta tayi shiru,yana ta zaune har lokacin Azaan yace ma Dadda "Dadi bari naje na dawo" Dadda ta kalleshi da sauri tace "toh kuma baka shiga ka ga jikin nata ba" yayi murmushi yace "zan dawo anjima kad'an" sai da ta tabbatar da gaske zai dawo kafin ta kyalesa,tace "to amma ai ya kamata ka ganta ku gaisa kafin ka dawo ko? Amma daga shigowa ma fisabilillahi ba sai ka tsaya ko y'ar hira muyi ba na tambayi auta ta" shi dai Azaan bai ce komai ba,ta kalli Waleed tace "toh ai shi kenan ma tunda ga Mamman yana nan ya tayani hiran kafin ka dawo" Azaan yayi murmushi without ya kalli Waleed dake kallon Dadda fuskarsa ba yabo bare fallasa,Dadda ta tab'e baki ganin yadda Waleed ya kafeta da ido har lokacin kuma bai ce mata komai ba ta d'auke kai tana kallon k'ofar d'akin da Manar take tana kwalo mata Kira,jin bata amsa ba ta d'aga murya tace "toh kuma Manar har cikin d'akin kike so ya biyo ki ne da baza ki fito ku gaisa ba?" Duk abunda suke yi tana jinsu tak'i ko da tari tayi,sai da Dadda ta sake mata magana ta fito sanye da enamours hijab,Waleed ya dunga kallonta hopping that za ta d'ago ta kalleshi,tunda ta fito ta gansa bai tafi ba ta mak'ale jikin kujera tana kallon Azaan a hankali tace "ina wuni,ya hanya?" Yayi murmushi yace "lafiya lao,how are u feeling now?" tace "da sauk'i" yace "maa sha Allah! Hope u've taken the drugs?" Ta gyad'a masa kai,Dadda sai kallonsu take tana murmushi,lokaci d'aya Manar ta saci kallon Waleed dake kallonta fuskarsa d'aure,ta d'auke kanta da sauri,Azaan yace "shikenan Dadi bari naje sai anjima idan na dawo" Dadda tace "toh Mamman Allah ya maka albarka,yi maza ki raka sa ke ko kya samu sauran ciwon da ya mak'ale mararki ya sauka.. Allah na tuba ai gara ma ku gama wannan k'adararren makarantar su Yaro su maki auren mu huta da wannan gantalallen ciwo da bai jin magani,tunda ma dai likita yace idan akayi auren zai daina ni dai gara ayi² mu huta" kamar Manar za ta nutse dan kunya,Azaan ya nufi k'ofa yana cewa "Dadi mai zan taho miki da shi?" Dadda tayi saurin kallonsa tace "a'a d'an nan barshi yau dai ba sai ka kasiyo min komai ba,kada ka kashe kud'in jirginka a kaina ka rasa na komawa gida" dariya sosai maganarta ya bashi,yayi murmushinsa yace "Dadi ba'a jirgin kasuwa nazo ba" Dadda tana kallonsa tace "iiiihhh! A na me ka zo?" Yayi murmushi yace "emirate flight" Dadda bata game me yace ba ta kyab'e baki tace "uhn! Kai dai jeka abunka kaji d'an nan Allah maka albarka" yace "ameen Dadi bari naje na dawo muyi hira" tace "toh shikenan Allah dawo da kai lafiya" yana sakin murmushi ya nufi k'ofa,Dadda ta kalli Manar ta had'e rai tace "ke kam na ga ranan da za kiyi abu ba'a sa ki ba,yanzu baza ki tashi ki rakasa ba kuma?" Manar ta turo baki ta mik'e ta bi bayan Azaan,Dadda ta kalli Waleed tace "shifa nan daka gansa kullum ba ya gajiya da hidima,aikinsa kenan fa yayi ta aiko min 'Dan fodiyo da garar arziki kullum da dare sai yasa an shigo min da kunshin kaza ko irin hantar da kake siyo min da can,wallahi akwaishi da sanin ya kamata,ku ma dai ku dunga koyi da shi.." Mik'ewa Waleed yayi da sauri ya fice daga parlon. A tsaye ya gansu k'asan balcony,Manar dai sai wani k'udundune jikinta take a hijab ta sunkuyar da kanta,shi kuwa Azaan sai kallonta yake kamar ranan ya fara ganinta,kamar wanda aka yiwa dole haka ya dunga tafiya babu wanda ya kula da fitowarsa,murya can k'asa Azaan yace "look at me please Guddi,let me feel relieved,i've missed u alot" kasa d'ago kanta ta kalleshi tayi,a hankali ya rik'o hannunta,ta d'ago manyan idanunta da sauri tana kallonsa,yayi murmushinsa mai tsuma zuciyar abokin tarayya da cool voice d'insa yace "pyaar hain tumse Guddi.. I'm always dreaming to be with u by my side as my Humsafar.. I wish idan na rufe idanuna na bud'e zan ganki cikin gidana kin zama matata.. I just can't.." Sai kuma yayi shiru ya lumshe idanunsa jin footsteps a bayansa,still Manar tayi seeing Waleed a tsaye d'an nesa da su yana kallonsu,da sauri ta zare hannunta daga na Azaan ta b'oye cikin hijab d'inta,Waleed ya d'auke kansa gently ya ci gaba da tafiya,though Azaan bai juya ba amma yasan shi ne,shisa ya k'i yarda ko kallonsa yayi har sai da yayi nisa kafin ya bi sa da wani kallo,ya d'an gyad'a kansa yana smiling,Manar dai duk a takure take jinta a hankaki tace "Yaya zan je na kwanta na gaji" sympathetically ya kalleta yace "alright! Hope cramps d'in ya yi sauk'i yanzun?" Zaro ido tayi sai kuma ta rufe fuskarta da sauri tana masa dariya k'asa²,ya dunga kallonta yana sakin murmushi,ya sunkuya dai² kunnenta a hankali yace "a day will come da zan san komai naki,including ur menstrual.." Bata bari ya k'arasa fad'a ba da sauri ta kallesa tana turo baki tace "kai Yaya wai ba ka jin kunya kai?" Murmushi yayi murya can k'asa yana kallonta yace "i want to ask a favor and please don't deny me" tana kallonsa tace "akan mene ne?" Yayi murmushi yace "i'll call u because yanzun Amaar yana jirana" ta gyad'a masa kai a sanyaye tace "alright! Sai ka
Chapter 83 · 0% Book details