← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 184

Sashe 28

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba'a d'auki lokaci mai tsayi da shigar Muh'd aikin soja ba aka turasa course China,a can ya had'u da wani ba'indiye mai suna Mahmoud Ibn Maqbool shima soja ne course ya kawosa,da yake musulmi ne sannan daki d'aya suke da Muh'd,suke gaisawa a haka suka zama abokai ya zama komai tare suke yi,ko ina d'aya zai je suna tare,a haka aminci mai k'arfi ya shiga tsakaninsu,ko bayan da suka koma k'asashensu basu yasar da juna ba,duk da Mahmoud ya fito gidan sarauta,sai dai ba duk wanda ya gansa yake saurin ganewa ba,saboda yadda yake gudanar da rayuwarsa baza ma ka tab'a cewa ya had'a alak'a da masu kud'i ba bare aje ga masu mulki,ko shi Muh'd bai tab'a tunanin haka ba,sai da wani lokaci ya kai masa ziyara can indiya yankin Vishakpatnam ya masa waya yace zai zo,bayan saukarsu a k'asar Mahmoud yaje tarosa airport shi kad'ansa suna tafiya suna hira,sanda suka k'arasa katafaren gidan sarautar Muh'd ya cika mamakin al'amarin,a nan ya tambayi Mahmoud ko me yasa bai tab'a sanar masa ba? Mahmoud yayi dariya yace "mene amfanin bayyana maka kaina da asalina?" Muh'd yace "kamar yadda ban b'oye maka asalina ba,bai kamata kaima ka b'oye min ba" Mahmoud yace "tun ina k'arami ban tab'a sha'awar mulki ba,wannan dalilin yasa bana son fad'an ni waye ko inda na fito,wanda suka sani shi kenan,wanda basu sani bama wata rana zasu sanni,kamar dai kai da baka sani ba sai yanzun" tun daga lokacin da Muh'd ya san asalin abokin nasa bayan komawarsa gida gaba d'aya ya fara yin baya da al'amuran da suka shafi Mahmoud,ko da Mahmoud ya fara ganin canjin fuska daga abokin nasa,ba tare da ya ji d'ar ba ya tambayesa,Muh'd yace "babu komai yanayin aiki ne yasa kaga kamar wani abu ya faru" Mahmoud dai ya jisa amma bai yarda ba,bayan wani lokaci yaga still babu chanji,ba tare da ya sanar ma Muh'd ba ya kamo hanyar zuwa Nigeria,sai da ya sauka a k'asar ya kirasa yace yana son ya tura masa address d'insa,Muh'd cikin mamaki yace "me za kayi da address kai da ba a k'asar kake ba?" Mahmoud yace "ka sani ko wata rana Allah yasa na zo kawo maka ziyara?" Muh'd yayi murmushi bai sake cewa komai ba ya tura masa,ba'a d'auki lokaci mai tsayi ba cab ya kawo Mahmoud k'ofar gidan kasancewar cikin GRA suke lokacin,ya fito ya sallami mi taxi,ya sake duba house number daya tabbatar inda yake nema ne ya yi knocking,get keeper ya bud'e yana kallonsa da rashin sani,yace "wa kake nema yallab'ai?" Mahmoud ba ya jin hausa ya yi still bai gane abunda mai gadi yace ba,ko da ya tashi yin magana shima sai ya yi da turanci ya tambayi mai gadi lieut Muh'd Usman Maji dad'i,mai gadi babu turanci but sunan Muh'd da yaji ya ambata yasa shi fahimtar gurin wanda baturen ya zo,here yace ya d'an jirasa zai shiga ya sanar masa da yaren kurame,bai jira amsar Mahmoud ba ya juya ya shiga ciki,sai ga su sun fito tare da Muh'd mai gadi yana sake masa bayanin wanda yazo nemansa,akan abokinsa da bai tab'a mafarkin gani ba dai² lokacin idanunsa suka fara sauka,yayi still kamar statue yana kallonsa da mamaki,Mahmoud yayi masa murmushi da turanci yace "barka d'an uwa" Muh'd cikin tsananin mamaki yace "kai ne da gaske?" Mahmoud yace "ga shi ka gani" suka rungume juna cikin tsananin farin ciki,kafin Muh'd yace "amma baka sanar min kana hanya ba?" Mahmoud yace "mene ne amfanin sanar maka,yanzu ba ga shi ka ganni ba?" Muh'd ya gyad'a kai ya karb'i jakarsa yace su shiga ciki,b'angaren iyayensu ya fara kaishi ya gabatar da shi gurin Mama Azumi (Dadda) da yayansa Ibrahim tare da matarsa da yake lokacin kusan shekara biyu kenan da aurensa da Asma'u,bisa ga jagorancin Alh Na Abba da ta fad'awa tun farko ita dai ta ga mijin aure,ko da ya tambayeta babu tsayawa jin kunya ta sanar masa Ibrahim ne d'an wajen yaronsa Malam Usman,sanda ta sanar masa take shima ya samu Malam Usman da maganar,karamci irin na Malam d'in yasa ba tare da ya yi shawara da Ibrahim ba ya amsa,sai bayan da suka tsayar da lokacin aure sannan Malam ya tara iyalinsa ya sanar da su hukuncin da ya zartar,cikin hukuncin Allah kuma sai aka yi sa'a a lokacin shi Ibrahim ko budurwa ba shi da ita,irin halaccin da Alh Na Abba ya yi musu a rayuwa sai yasa shi amincewa shima,ba'a d'auki lokaci mai tsayi ba aka yi biki amarya ta tare gidan mijinta,da yake kuma rabon a kusa yake,watanni goma dai² da zuwanta gidan ta haifi d'anta namiji,Abba yasa masa sunan Muh'd suna kiransa Waleed. Lokacin ko da Mahmoud ya sauka gidan Hafsah ba ta nan tana makaranta basu had'u ba,sai yamma lokacin ta dawo a galabaice sanye da fararen kaya irin na d'aliban likitanci,tun da ta sawo kai compound d'in idanun Mahmoud dake zaune saman farin plastic chair suna hira suka sauka kanta ya kasa k'iftawa,hankalinsa da nutsuwarsa gaba d'aya suka tattara suka koma kanta,saboda Hafsah ta kasance irin matan nan da ake kira full option,duk da ba fara bace ita amma baza'a sa ta cikin sahun bak'ak'e ba,kyau dai² gwargwado da diri Allah ya mata shi,da wahala lafiyayyan namiji ya kalleta bai ji wani abu game da ita ba,sai dai itan ce bata cika sakin fuska ba saboda burinta na son zama likita yasa bata bawa samari damar zuwa mata da maganar soyayya,har ta k'araso gurin da suke zaune Mahmoud bai daina kallonta ba,cikin ladabi tayi murmushi dimple d'inta ya bayyana hankalinta gaba d'aya akan Yayanta da yake kallonta tace "Yaya barka da hutawa" murmushin shima yayi mata yace "yawwa k'anwata kin dawo lfy,ya studies da hanya?" Tace "alhmdllh" juyawa yayi ya kalli abokin nasa yace "Bhidu! (Dude) Meet my sister Hafsah" itama ya juya ya kalleta yace "Sister meet my friend Mahmoud Ibn Maqbool" idanunta ta wulga gefen da yake tana sakin masa kayataccen murmushinta,suka had'a ido da shi tace "Assalamu alaikum warahmatullah!" Haske gami da kwarjininta yasa gaba d'aya Mahmoud yaso rikicewa but da yake namijin duniya ne a hakan ma kuma soja ya maze ya amsata,da harshen nasara suka gaisa,tayi musu sallama kasancewar a gajiye take ta wuce,Mahmoud ya sake binta da kallo yana hasaso wani abu a ransa,bayan tafiyarta ya waigo yana sauke wani ajiyar zuciya suka kalli juna shi da Muh'd kai tsaye bai tsaya b'oye² ba da yake Mahmoud irin mutanen nan da basu iya b'oye² ba,matuk'ar sunga abunda yayi musu take suke zartar da hukunci yace "Bhidu! I love ur Sis,za ka ba ni ita na aureta?" Muh'd yayi murmushi bai ce komai ba,sai ma hiran da yayi k'ok'ari ya canja musu,Mahmoud bai ji dad'i ba rashin amsan da bai samu daga abokin nasa ba but babu yadda zaiyi ya had'iye damuwarsa bai nuna ba,sai dai ya ci alwashin duk hanyar da zai bi dan ya samu Hafsah zai bi saboda shi dai yaji ta kwanta masa kuma yana sonta da gaske,tun daga ranar bai sake ma Muh'd maganar ba har ya gama kwanakin da zai yi a Nigeria ya koma gida,bayan komawarsa gida ya samu mahaifinsa Raj Maqbool da maganar shi fa ya samu matar aure,Sarki yayi farin ciki yace "a ina take?" Ba tare da b'oye² ba ya sanar masa komai,jin wai daga Nigeria yarinyar take yasa sarki k'in amincewa da farkon,sanda yaga d'ansa ya fara shiga damuwa ya aika takanas zuwa Nigeria a masa binciken y'ar waye ita a Nigeria,ko da wakilan sarki suka sauka gidan sarautar Kano,sarkin Kano da kansa ya aika aka masa binciken yarinyar da Raj Maqbool ya sanar masa maganarta,a nan suka koma da sakamakon da ya yiwa sarki dad'i kasancewar sun samu cikakken bayani akan asalin Hafsah da mahaifanta,daga nan ne kuma magana ta fara fitowa,ba tare da b'ata lokaci ba Raj Maqbool ya sake aiko wakilansa cike da shiri tare da jagorancin mai martaba sarkin Kano aka nemawa Mahmoud auren Hafsah,a lokacin ko da suka zo da maganar daga b'angaren iyayen Hafsah suma dai sun so k'in amincewa ganin bambancin yare da k'abila yasa su nuna damuwarsu akan maganar,maimartaba da kansa ya d'an ja ra'ayinsu bayan ya musu bayanin yin hakan ba wani matsala bane,tunda dukansu sun had'u a addini,sannan sun had'u ta wani yaren ai ba matsala bane dan sun yi aure,nan dai ba a son ran iyayen Hafsah ba suka amsa suka bada aurenta ga Mahmoud maimartaba sarkin Kano ya karb'a masa,aka tsayar da lokacin aurensu wata d'aya. Tun da labari yaje kunnen Mama Azumi (Dadda) gaba d'aya ta kasa sukuni tunaninta shi kenan an rabata da y'arta,nan ta dunga kuka tunma kafin lokacin yayi,duk wanda ya zo mata Allah sanya alkhairi kuwa tun daga farko har k'arshe sai ta basa labarin yadda al'amarin ya kasance,tana kuka tana fad'a da kyar aka samu Muh'd da Malam Usman suka shawo kanta ta daina yawan koke² ta hak'ura ta daina mitar abun,a hankali kwanaki suka dunga wucewa biki sai sake gabatowa yake,ana saura kwana uku biki da kyar ranar bayan Hafsah sun fito final paper na k'arshen session da suke ta janyo manyan k'awayenta biyu Maryam (Mammy) da Fatima (Bebie),cikin shirunsu na tahowa biki suka sauka bakin get d'in gidan da kayansu sai an gama biki za su koma,Hafsah ta tsaya za ta sallami mai napep Yayanta Muh'd ya sawo kai zai fito idanunsa suka sauka kan Maryam,nan fa yace dawa Allah ya had'a mu,ya tsareta da kaifaffun idanunsa,Hafsah ta sallami mai napep ta gabatar da k'awayenta gurin Yayanta suka gaishesa suka wuce suna tafiya suna hira,sanda suka shigo suka iske Mama Azumi da surukarta Asama'u zaune a parlor suna hira,haka kawai tun da su Hafsah suka shigo ta kallesu taji k'awayen tan nan basu mata ba,ko da suna gaisheta ma a yatsine ta amsa su,daga haka ta tashi ta d'auki Waleed za ta fita da shi,Mama Azumi ta kalleta tace "ke kuma fa ina zuwa kika sab'i yaro za ki da shi?" Asama'u cikin had'e rai tace "Mama zanje gida ne,ba na d'an jin dad'i" Mama azumi ta jinjina kai tace "Aihooo! To ai da kin bar yaron a nan wuri na ko? Ke da bakya jin dad'i kuma ta ina za ki iya kula da shi idan kin tafi da shi?" Ba don
Chapter 28 · 0% Book details