← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 184

Sashe 22

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da kallo Mama ta dunga bin Diyanah sanda ta zauna,tana squeezing fuskarta tace "Mama u know what?" Mama dake kallonta har sannan ta kasa kauda idanunta a kanta tace "sai kin fad'a" Diyanah tace "yanzu naga wancan yarinyar ta fito daga d'akin Yaya,ko uban me ya kaita,ohoo?" Still Mama tayi tana kallonta kafin tace "wace yarinya?" Diyanah tace "wancan Manar d'in mana" wani irin zaro idanu Mama tayi da k'arfi ta kwala cewa "kutumar uba! Uwar me ya kaita d'akinsa,me za ta masa?" Diyanah ta watsa hannuwa alamun bata sani ba,Mama ta dunga cika kamar za ta fashe a fusace tace "Deejah maza² je ki k'ira min Yayanku" da sauri Deejah tace "kaiii! Mama ni dai gaskiya ki aiki Diyanah Allah ba na son zuwa kusa da shi" wani kallo Diyanah ta aikama Deejah tace "Tabbb' d'i wallahi bazan je ba,naga dai ke Mama tace ki kirasa ba ni ba,salon naje ya haure ni da k'afa ko ya rankwashe ni? Wallahi idan baza ki ba sai dai a bari har ya dawo gidan" ganin sun tsaya jayayya yasa Mama nufar hanyar fita ba tare da ta sake bi ta kansu ba,ta tsaya dai² bedroom d'insa tana knocking,kusan mintuna biyar ta d'auka tsaye a gurin ta k'i hak'ura sai bubbuga k'ofar take a tunaninta yana jinta yak'i bud'ewa sanda taji shirun ya yi yawa babu alamun da mutum a ciki da sauri tayi k'asa tana tambayar maids Waleed,Haulatu dake goge² ta sanar mata ya fita babu jimawa,ta gyad'a kai bata ce komai ba ta koma sama. Yinin ranar gaba d'aya Manar bata zauna apartment d'in Dadda ba,haka a b'angaren Mama itama ta wuni neman Waleed motsi kad'an taji sai ta fito daga ta duba ko shi ne ya dawo but ranar har dare bai shigo ba. Da daren lokacin Amaar ya shigo ya samu Dadda zaune ita kad'ai ta hard'e k'afafu tana girgiza su,da sallama ya k'arasa Dadda ta d'aga kai ta bisa da kallo sanda ya isa inda take yace "Hjy barka da dare" idan ta amsa materials da suke parlon sun motsa,yadda tayi ba k'aramin dariya ta kusa basa ba ya danne yace "Hjy Manar fa?" Kamar wanda take jira a mata magana a fusace ta d'ago tana masa wani kallo tace "wace ce wata Manar kuma?" Yace "jikarki mana" tace "aka ce maka kuma a nan gidan take?" Shima da yake tsokana yake ji sai ya nemi guri ya zauna k'asa² yake dariya yace "to wai a ina take ne?" Dadda ta masa banza,yace "Hjy ki taimaka ki fad'a min inda zan sameta" banza da shi tayi,da yaga ba ta da niyyar masa magana ya tashi yace "shi kenan tunda baza ki fad'a min ba,auren ma daga yau na daina tunda kina jina baza ki min magana ba" wani kallo ta watsa masa da yasa shi fashewa da dariya,a fusace Dadda tace "ni dai yau ina ganin masifa k'uru² wani ya fad'a maka akwai wata mai sunan a nan gidan ne?" Murmushi yayi yace "alright! Dama sak'o aka ba-ni,ko na ba-ki ki ajiye mata?" Cikin fad'a tace "kada ka ba-ni dan wallahi bazan aje ba,ni da ita haihata²,daga yau ni da ita kowa yayi ta kansa.. Allah na tuba me ake da mutane irin ku,duka taron marasa amfani" juyawa yayi saurin yi yana dariya ya san idan ya tsaya ta dunga mita kenan,duk fushinta a kansa za ta saukesa,yana fita ya hangosu ita da Ameerah suna fitowa apartment d'in mother,da kallo ya bisu ya tsaya gurinyana murmushin fad'an Dadda sanda suka k'araso Manar tace "Yaah Amaar ina wuni?" Yace "lfy lou y'an matan Hjy Dadda,daga ina kuke?" Manar tace "munje gurin mother" ya gyad'a kai yana sakin murmushi yace "yaji kuka yiwa Dadda yau?" Dariya suka kalli juna suka yi,yayi murmushi yace "yanzun ina za ku?" Ameerah tace "abinci za muje kai mata" ya gyad'a kai yace "sai kun dawo ni bari na tafi.. Allah tsare ku da fad'anta" har ya yi gaba ya waigo ya kwaloma Manar kira,ta juya tana kallonsa,yace "idan kun dawo ku sameni d'akin Aunty akwai sak'on da zan ba-ku" amsawa suka yi suka nufi k'ofar apartment d'in kowa tana had'e rai suka yi sallama,Dadda bata ko d'aga kai ta kallesu ba,Ameerah dake d'auke da folded basket green colour ta k'arasa kusa da ita ta ajiye tace "ga shi inji Aunty Mammy" kamar ta kunno Dadda ta fara fad'a "d'auki abunta ki mayar mata bazan ci ba,ko an fad'a muku ni y'ar yunwa ce da za ku kawo min wani shegen shinkafar da babu dad'i babu dadad'awa" kallonta suka tsaya yi baki sake,a fusace ta tura basket d'in gefe tana mita,Manar tayi k'wafa suna had'a ido da Ameerah ta gyad'a kai ta k'araso gurin,ta kai hannu za ta d'auke basket d'in a fusace Dadda ta kai mata duka,fashewa da dariya suka yi,Ameerah dake kallon Dadda tana dariya tace "Ha'a! Kefa kika ce bakya so a mayar mata" cikin jin haushi Dadda tace "kuji wani masifar kuma! Ni yaushe kika ji na ce haka? Salon dai kar abar mutum ya zauna lafiya,yanzu idan Maryam taji fisabilillahi ba sai ku janyo ta k'ullace ni ba" Manar ta had'e rai tace "ke dai Dadda ki daina haka Allah,sai ki fad'i magana idan ance kin fad'a kice ba haka ba?" Dadda ta juya ta kalli Ameerah tace "yanzu y'ar nan tsakani da Allah kin ji na ce muku wani abu tun shigowarku?" Dariya Ameerah ta sake fashewa da ta girgiza ma Dadda kai,nan da nan Dadda ta k'ule saboda dariyar da Ameerah keyi tace "ke ni fa ban son haka,sai kuzo kusa mutum gaba kuna masa wani dariya kamar kwancen mahaukata" da sauri Ameerah ta juya ta kalli Manar tace "Sis muje Yaah Amaar yana jiran mu" Dadda ta tsuke fuska bata sake ce musu komai ba ta ja basket ta fara fito da warmers dake ciki,kusan tare suka shiga gidan da Waleed Manar ta dunga kallonsa ganin ya d'aure fuska ta kasa masa magana,Ameerah kad'ai ta gaishesa Manar kam tuni ta yi sama,ta gefen idanunsa ya bita da kallo yayi k'wafa,bai dai ce komai ba ya nufi saman shima Ameerah ta biyosa a baya,yana wucewa ta bud'e bedroom d'in Aunty ta shiga,ta tarar da Manar ita kad'ai a d'akin sai cika take k'iris take jira ta fashe,da kallo ta bita ta tsaya doorway bata k'arasa shiga ba tace "Ina Yaah Amaar d'in kuma?" Manar ta watsa hannuwa fuskarta a d'aure tace "nima ban samesa ba da na shigo" juyawa Ameerah tayi da niyyar zuwa ta kirasa taga ya fito daga d'akinsa d'auke da wata jakar kwali,yana zuwa yace "muje ko da bina za kiyi?" Tayi murmushi bata ce komai ba ta shiga ya biyo bayanta,kujeran gaban mirror ya janyo ya zauna,Ameerah ta matsa kusa da Manar ta zauna sai kallon jakar hannunsa take,ya mik'a ma Manar yace "take! Azaan ya bayar a kawo miki" kallon jakar ta dunga yi,mamaki k'arara a fuskarta tace "Yaya mene a ciki?" Ya d'age kafad'u yace "abun a hannunki kina tambayata,ki bud'e ki duba mana" Ameerah ce tayi saurin karb'a tace "kawo muga tunda kin kasa fitowa da su" tasa hannu ciki ta janyo kwali biyu dake ciki masu d'an girma,waya ne guda biyu k'iran samsung galaxy A70,Ameerah ta zaro ido tace "Yaya ai phones ne" yace "yeah! I knew" murmushi tayi kafin ta fara duba kwalin phones d'in,ya mik'e zai fita yace "akwai layi ciki,and akwai numbers d'in kowa sai ki duba abunda bai yi ba ki gyara" godiya ta dunga masa kamar shi ya ba-ta,Ameerah ta fito da su duka Manar ta kalli wayoyin taga iri d'aya babu bambanci sai na colour tayi dariya tace "Sis ki d'auki d'aya nima na d'auka d'aya" Ameerah ta girgiza mata kai tace "a'a ni bazan d'auka ba" saurin kallonta Manar tayi tace "saboda me baza ki d'auka ba?" Ameerah tace "ai duka ke yace a kawowa" Manar tace "to kuma iri d'aya? Ni me zanyi da waya biyu?" Ameerah tace "a'a ki rik'e duka kin san dalilin da yasa ya aiko miki su?" Manar tace "ko mene ne ni dai ba na so d'aya ya ishe ni" duk yadda Ameerah za tayi sai da tayi akan baza ta karb'a ba itama Manar ta dage,dole daga k'arshe ganin ranta ya b'aci ta d'auki d'ayan tana fara mata godiya ta katseta tana aika mata harara a fusace ta tashi ta fita. Yana shiga bedroom d'insa ya fara unbuttoning shirt d'in jikinsa Mama ta banko k'ofar kamar wanda aka cillota,ya juya da niyyar ganin waye ya shigo,ganin Mama yasa shi yin ajiyar zuciya,but kallon da take aika masa yasa jikinsa ya bashi akwai matsala,a nutse yana kallonta yace "Mama lafiya?" A fusace tace "uban me ya had'a ka da yarinyar can?" Zaro k'ananun idanunsa yayi cike da mamakin maganarta yace "wace yarinya?" Tace "yarinyar Maryam nake maka magana" tunani ya tsaya yi because bai fahimci akan wanda take magana ba,cikin fad'a tace "yarinyar da kakarku ta gama gurb'atawa ita kake shige ma Waleed? Shin ban hanaka mu'amala da duk abunda ya shafi Maryam ba?" Sai lokacin ya fahimci akan wa take maganarta,ya sauke wani heavy ajiyar zuciya ba tare da ya ce mata komai ba ya koma bakin bed d'insa ya zauna,fad'a sosai Mama ta rufe ido ta dunga masa har kamar za ta aro baki,yayi shiru bai ce mata komai ba sai da ta gama yace "Mama babu wani abu tsakanina da ita fa" wani kallo ta masa tace "ehh! Saboda ka d'auke ni sha³ ko? Shisa kake fad'a min babu komai tsakaninku,bayan an fad'a min an ganta d'akinka? Idan har babu komai tsakaninku me ta zo ta maka?" Still yayi yana kallonta fuskarsa d'auke da mamaki yace "waye ya fad'a miki Mama?" Wani kallo ta aika masa tace "me ka d'auke ni ne kam Waleed? Bazan san abunda kake aikatawa a bayan idanuna ba kake nufi?" Zai yi magana ta katsesa "ba na buk'atar jin ko wane irin magana daga bakinka,ka rufe min baki kafin raina ya b'aci" kamar yadda ta buk'ata haka yayi shiru,sai da ta gama masifar fad'an dan kanta tayi shiru,a hankali yace "i'm very sorry Mah,amma abunda kike tunani ba haka yake ba,Abba ya aikota ta karb'i sak'o" kallonsa ta dunga yi tace "sak'o?" Ya gyad'a mata kai yace "sure"
Chapter 22 · 0% Book details