Sashe 29
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Asama'u ta so ba ta ajiye Waleed ta tafi,yaro da farin jini gashi tun da aka haifesa kyakykyawa ne kamar ba d'an hausawa ba,Maryam tana kallonsa tayi murmushi ta mik'a masa hannu dake itama gwanar son yara ce tana masa murmushi tace "Zo na d'auke ka my boy" Mama azumi dake zaune ta gyad'a kai tace "anya wannan sarkin kuiyan zai zo kuwa?" Ga mamakinta ko gama rufe bakinta bata yi ba taga ya rarrafa ya kama Maryam ya tsaya yana d'aga k'afarsa zai hau jikinta,Maryam tayi murmushi ta d'aukesa ta ajiye kan cinyarta da fara'arta tace "Mama kuma kinga ya zo" Mama azumi dake kallonsu baki sake tace "bar ni da d'an kan uwa! Kuma fa k'uiya yake na bugawa a jarida" Maryam tayi murmushi tace "ni dai Mama tunda bai yi min ba ai bazan ce yana yi ba" cikin barkwanci Mama azumi tana dariya tace "a'a ke dai Maryam kika sani ko k'wan matarsa ya gani a jikinki shi yasa ya yarda kika d'aukesa" da sauri Maryam ta sunkuyar da kai cikin jin kunya bata sake cewa komai ba ta duk'ufa yiwa Waleed wasa,shi kuma sai dariya yake mata,Hafsah dake gefensu ta kalli yadda yake kyalkyala dariya ta kama baki tace "wallahi kuwa Mama ina ji maganar kin nan ya zama gaskiya kinga fa yadda yake mata dariya da tana masa wasa" Mama azumi tace "to nima dai da wasa na fad'a amma idan Allah ya tabbatar ai bazan k'i ba" ranar gaba d'aya hira suka dunga yi da Mama azumi,yayin da a b'angaren Maryam tun da Mama tayi wannan maganar ta kasa sakewa tayi wani dogon magana,hankalinta gaba d'aya ya koma kan Waleed ta dunga masa wasa yana dariya,da ta daina sai ya fasa kuka,k'arshen ko abunda ya kawosu basu yi ba a bayanta yayi bacci,suna zaune parlon har dare Abba ya dawo daga aiki ya shigo ganin mahaifiyarsa ya tarar da su sai hira suke,shigowarsa yasa su rage surutun da suke suka gaisa,a lokacin Waleed yana hannun Fatima itama ya yarda ta d'aukesa,ko da Abba zai fita bayan sun gaisa da yaje zai karb'esa a hannunta k'iri² yak'i yarda da uban,Fatima tayi murmushi tace "oh c'mon my boy! K'uiya za ka yima Abba kuma?" Yaro bai san me tace ba yabi bakinta da kallo yayi dariya,Abba da yaga haka shima sai yayi murmushi yace "tunda baza ka zo ba shi kenan mamarka ta zo ta d'aukeka" yayi sallama da Mama azumi da su Fatima,yana juyawa zai tafi Waleed ya bisa da kallo yasa kuka,Abba ya waigo ya kallesa yayi murmushi yace "Aatoh! Ai kuma wannan ba laifina bane da za kasa ma mutane kuka" Mama azumi ta tab'e baki tace "Yaro! Maza d'aukesa ku b'ace min kafin ya fusatoni na mangaresa" Fatima ta mik'a ma Abba shi tana dariya tace "haba Mama miji ne fa shi,kina matarsa kuma za ki dakesa?" Mama tace "yo zaimin kukan banza a nan ne,ba gara na masa dukan ba sai yayi mai dalili" Abba yayi dariya ya karb'esa yace "ai ita Hjy ba ta mijin da shi,nan gaba kuma idan kika ga y'an matansa suna zuwa zance kada ma kice za kiyi kishi da su" Mama tace "dawa zan yi kishin?" Abba yace "shi mijin da bakya so mana" ta tab'e baki tace "Allah sawak'a min nayi kishin wannan halittar" Fatima tace "a'a Mama kada lokacin yayi mu tuna miki kice ba haka ba kuma" Abba yayi dariya yace "Aatoh! Gara dai ku fad'a mata tun yanzu" Dadda ta dage akan maganarta suna mata dariya,Abba ya juya ya musu sai da safe ya fita. B'angarensu ya k'arasa lokacin ya samu Asama'u tana waya duk ranta a b'ace sai masifa take tana fad'in "kinga ba na son shashanci idan baza ki zo ba ki fad'a min" bai ji me aka ce a d'ayan b'angaren ba yaji ta yi k'wafa tace "shi kenan ke kika sani idan baki zo ba,kanki za ki yiwa ba ni ba" k'it ta kashe wayar ta ajiye sai huci take,Abba ya k'arasa inda take a hankali ya dafa shoulder ta d'aya yace "lfy? Ko akwai wani matsala ne?" Asama'u da bata ji shigowarsa ba sai maganarsa ta tsinta tayi saurin waigowa ta kalleshi,fuska babu wadataccen fara'a tana sauke ajiyar zuciya tace "wallahi ni da wannan sakarar ce Rabi" a hankali Abba ya zauna gefenta yana rungume da Waleed a jikinsa yace "Uhn! Me yake faruwa?" Kawar da kai tayi tace "it's a secret" ya kalleta da kyau yace "really?" Ta gyad'a masa kai,jinjina kai yayi bai sake mata magana ba ya ajiye Waleed ya tashi,ta kalli yaron ta tab'e baki tace "sun yarda sun ba ka shi ka dawo min?" Saurin kallonta Abba ya juya yayi yace "ban gane me kike fad'a ba" tace "wasu yara k'awayen Hafsah masu iyayin bala'i da suka zo,akan su nake magana" dariya ta bawa Abba yadda yaga tana magana,yace "Ohhhoooo! Ko su ne naga Waleed a gurinsu?" Da sauri Asama'u ta kallesa tace "Waleed d'ina?" Yace "sure!" Tayi murmushi tace "Waleed d'in da ba da kowa yake yarda ba shi ne suka d'auka?" Abba yace "kina mamaki ne?" Tace "ai dole nayi,Yaron da muma bai bari ba wani lokacin k'uiya yake mana idan za mu d'aukesa shi ne yau ya yarda da bak'i?" Shi dai Abba ganin ta mayar da maganar abun reputation kamar tana son k'aryatasa kawai sai ya fara cire kayansa ba tare da ya sake ce mata komai ba ya wuce toilet. Washe gari gaba d'aya su Hafsah basu zauna a gidan ba sun tafi gyaran jiki,tun safen Asama'u take kiran Rabi amma ta k'i zuwa sai yamma,kusan a tare suka shigo da su Hafsah,suka gaisa da ita cikin sakin fuska,suna shigowa compound Hafsah ta hango fitowar Prince Mahmoud Maqbool daga b'angarensu ta yi still tana mamakin yaushe yazo,mutumin da babu jimawa ya mata waya shi ne bai sanar mata yana hanya ba,yadda ta tsaya tana kallonsa fuskarta cike da mamaki yasa Maryam ta rik'ota tace "what happened sister?" Hafsah tayi ajiyar zuciya tace "kun ga mutumin nan d'azu fa muka yi waya shi ne bai ce min yau zai zo ba" dariya suka yi Fatima tace "banda abunki surprise yake son baki,and da alamun kin karb'a" dariya itama tayi musu suka k'arasa sai kallonta yake yana sakin murmushi,Fatima tace "amma fa sister kinyi sa'a wallahi mijin kin nan he's more than handsome,banyi tunanin haka zan gansa ba" Maryam tace "nima dai banyi tunani ba,but duk da haka our princess ta fisa had'uwa" suka yi dariya duka,suna cikin gaisawa tana gabatar masa da k'awayenta,Muh'd ya fito daga apartment d'in yana dariyar Mama azumi,tsayawa yayi cak idanunsa akan Maryam dake magana da Mahmoud tana sakin murmushi,lokaci d'aya yaji kamar an kwad'a masa guduma a kai,ya dunga jin wani irin sensational feeling yana taso masa,Hafsah da taga fitowarsa tace "Yaya tare kuke ne?" Murmushin k'arfin hali yayi mata yace "no! Nima ban san da zuwansa ba ganinsa kawai nayi,tunda ya zama d'an gari,ya daina nemana sai dai na gansa kawai" ta gyad'a kai tana sakin murmushi sai dai bata sake cewa komai ba,su Maryam suka gaishe shi then suka wuce suka bar Hafsah gurin masoyinta,Mahmoud yayi saurin matsowa kusa da ita da turanci yace "me kuke cewa ke da yayanki? Kin san ba gane yarenkun nan nake ba" tayi dariya tace "nima ai ba jin naka yaren nake ba" murmushi yayi mata yace "after munyi aure zan koya miki" tace "sure?" Ya gyad'a mata kai yace "nima ai za ki koya min naku ko?" Tace "idan kana so me zai hana" yayi murmushi yace "yana bani sha'awa sosai and ina so na iyasa" tace "babu matsala nima idan ka koya min naka sai na koya maka namu" da murnansa yace "really?" Ta gyad'a masa kai tace "absolutely sure" basu wani jima suna hiran ba sosai yace ta shiga gida ta huta anjima zai dawo,suka yi sallama ya wuce part d'in Muh'd itama ta shiga gidan. Rabi ce tayi sallama part d'in yayarta,Asama'u tana jinta ta fara k'unduma mata ashar,ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba,fad'a kamar za ta aro baki,Rabi ta tsaya kallonta da mamaki tace "wai duk akan me kike wannan kumfar bakin?" Asama'u tace "ban sani ba,banza mara hankali,tun wancan satin nake kiranki kizo Muh'd ya zo,amma yarinyar nan saboda kin mayar da ni sha³ kin d'auke ni y'ar iska kika k'i zuwa sai yau,ai ki ma tattara kayanki ki koma zuwanki yanzu baida wani amfani" zaunawa tayi tana sauke ajiyar zuciya tace "kema dai da tun farkon kin fad'a min haka ai da tun a ranar na taho" harararta Asama'u tayi ta d'auke kai,Rabi tace "to yanzun ya ake ciki?" Ajiyar zuciya Asama'u tayi tace "ki tashi kije ki gaida Hjy yanzu ki dawo kin san ta gurinta za mu fara kamun k'afa" Rabi tayi dariya ta mik'e tace "bari to naje na dawo" ta fita da sauri tayi b'angaren Mama azumi,sanda ta shiga ta tarar da su Maryam suna hira da Mama ta zauna bayan sun gaisa suka d'an tab'a hira da su Maryam then ta fita,tana komawa ta sanar ma Asama'u,here ta d'an mata lecture akan yadda za ta shigewa Muh'd har shi da kansa ya fito yace yana sonta,bata zo da niyyar kwana ba amma Asama'u sai da ta san yadda tayi ta rinjayi ra'ayinta tace "ba dai kayan sawa kike tunani ba?" Tace "ehh! Wallahi kinga ban taho da komai ba" Asama'u tace "kada ki damu zanje gidan gobe gurin Hjy sai na taho miki da su.." Tun daga ranar Rabi ta fara baza komarta sai dai ta kasa kama kifin,gaba d'aya ma tunda tazo ko hanya basu had'o da Muh'd ba,sai ranar dinner auren hafsah shima ba ita da shi ba,can a gurin dinner ta hangosa kusa da abokinsa gefensa Maryam suna d'an magana da ita k'asa² suna dariya,d'ayan side d'in kuma Fatima,har aka tashi gurin dinner bata samu damar ganinsa a keb'ance ba,suna komawa gida take fad'awa Asama'u tace "wai dama haka Muh'd ya sake zama handsome?" Asama'u ta maka mata harara tace "ban sani ba,da da nake kiranki kina min iskanci,yanzun ai idanunki sun gane miki" Rabi tace "gaskiya idan na samu guy d'in nan na yi sa'a" Asama'u ta karb'e zancen da fad'in "idan kika