← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 184

Sashe 77

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

faru tun zuwan su Dadda gidan,ran Hjy Sahiba a b'ace tace "dama na san wata rana sai anyi haka,banda kin dage tun farkon sai shi Allah na tuba me za kiyi da irin Hjy Asama'u,ni da ita fa kar ta san kar ne,ke kuma kika ce atafau sai shi kin samu miji,but don't worry wannan ai mai sauk'i ne,ni na san ta yadda zan b'illowa al'amarin,ki kwantar da hankalinki sai kace ba ni na haife ki ba,yadda nake zaune gidan ubanki hankali kwance ba damuwar kowa haka ke ma za ki zauna gidan nan,idan kinga kin fito sai dai gawarki wallahi" Afiyah tayi wani murmushin jin dad'i tace "that's how my Mummy is.. Allah k'ara maki lafiya" Hjy Sahiba tace "ko shi Waleed d'in yazo maki da zancensu kada ki nuna masa komai,ki sharesa kawai har ita yarinyar da ta so take miki rashin kunyar,tunda kin san ta hanyar da aka bi aka yi auren,ki nutsu ki bari har ya gama zuwa hannunki sai ki horasa yadda ya dace.. kinji ko" Afiyah ta gyad'a kai tace "to Mummy" Hjy Sahiba tace "ki kwantar da hankalinki kinji,babu mai saka miki ciwon kai a gidan aurenki,nan gaba zuwa gidanma duk sai yafi k'arfin danginsa in dai ina numfashi cikin duniyar.. Maganar kayan da nace zan bayar a kawo maki suna hanya.." Ji tayi ana tab'a k'ofa da sauri ta d'aga kai ta kalli gurin tace "Mummy za muyi waya anjima" bata jira cewar Mummy'n tata ba ta katse wayar,ta kwanta da sauri ta juya baya,Waleed ya shigo ya zauna gefen gadon yace "tashi ki zauna magana nazo muyi dake" ganin ta k'i tashi ya gyad'a kai yace "ko da baza kice komai ba i know kina jina,so u have to keep this in ur mind,u don't need to worry about what happened between ke da Hjy,that's how my grandma is,idan aka mata abu babu ruwanta da ko kai waye har su Abba bata bari ba sai dai idan basu yi abunda za tayi magana ba,Manar kuma she have no problem apart kawai ba ku fahimci juna bane,but she's very nice and sweet to stay with,ko a gida Hjy ba ta son a tab'a ta,ba ni ba ko waye ma,ranan za'aga other side of her because takwararta ce,besides kuma just few hours za su yi su tafi.." Ita dai bata kulasa ba,ya gaji da sauraren tayi magana ya tashi yace "idan kin gama fushin ki sakko downstairs muyi breakfast" wani juyowa tayi da sauri ta kallesa a fusace tace "bazan ci ba" ya d'age shoulder yace "okay" bai sake bin takanta ba ya juya ya koma downstairs,tun daga nesa yake kallon Manar da ta wani had'e rai har ya shigo parlon yace "baza ki sakko ki had'a shayin ba?" Kamar jira take yayi magana ta zumb'uro baki tace "ni na k'oshi" yayi shiru yana kallonta,can ya k'arasa kusa da ita yace "me yasa baza ki ci ba?" K'in cewa komai tayi,yayi murmushi ya zauna kusa da ita,ta d'auke kanta za ta mik'e ya rik'ota,ta fara k'ok'arin k'wacewa tana cewa "nifa na ce maka ba zan ci ba.." Muryar Dadda suka jiyo tana sakin salati tace "meye haka Kuma nake gani ni jikar laraba?" Saurin sakar mata hannu Waleed yayi,da sauri Dadda ta zauna kan kujera tana kallonsa tace "Anya lafiyarka lao kuwa Mamman kake matse y'ar mutane haka?" Ta gefen ido ya kalleta,Dadda ta juya ta kalli Manar tace "me kika masa?" Fuskarta a d'aure tace "Hjy nifa ba abunda na masa,kawai cewa nayi na k'oshi shi ne wai dole sai na ci" Dadda ta bud'e ido tace "iiiihhh! Kamar ya kin k'oshi kuma haka babu dad'in ji,uban me kika ci?" Ta kalli Waleed da ya musu banza tace "ko ta ci kafin na fito?" Ya tab'e baki yace "a'a" Dadda tace "to kuma shi ne dan munafurci za tace ta k'oshi,bata fa karya ba muka fito.. To ai shi kenan,ni dai rabu da ita ka had'a min shayin" murmushi yayi ya gama had'a ma Dadda shayi ya ajiye a gabanta ya d'auki plate d'in dankalin ya ajiye mata ta zauna k'asa tace "kai dai Allah sa ka gama da duniya lafiya,Allah kuma ya maka albarka ya baka masu maka kaima" yayi murmushi yana satar kallon Manar data d'auke kai tak'i kulasu yace "ameen Hjy" tare suka yi breakfast da Dadda kafin ya tashi ya wuce sama,Manar sai kallonsa take tana ganin ya mik'e ya nufi sama ta d'auke plate d'in da sauri ta gudu kitchen,Dadda ta d'aga kai tana kallonta tace "kuga munafuka da kika ce ba kya ci kuma" bata kulata ba ita dai ta shige ta tsaya jikin kitchen island sai da ta cinye kafin ta dawo parlon ta tattare sauran plate da cups d'in ta kai kitchen ta had'a duk abunda suka b'ata ta wanke,ta mayar da komai gurinsa ta goge kitchen d'in har wall then ta fito,ganin Dadda ba ta nan ta share parlon ta gyarasa shima ta goge ta kunna turare,kafin kace me k'amshi ya cika parlon,Dadda dai tun da cikinta ya d'auka ta shige wani d'aki ta kwanta sai bacci kamar tana gida. Wajen 12 Waleed ya sakko parlon cikin k'ananun kaya da suka mugun karb'arsa,ya dunga kallon Manar dake danna wayarta,yana tsaye kusa da ita yace "Hjy fa?" Ba tare da ta kallesa ba tace "think bacci take" ya gyad'a kai bai ce komai ba ya zauna gefenta,jin footsteps a stairs suka juya tare suka kalli Afiyah dake sakkowa kamar tana tausayin k'asa,fuskarta babu walwala har ta k'arasa sakkowa,tunda suka had'a ido da Manar sau d'aya ta d'aure fuska,itama Afiyah haka tayi tana jin wani tsanar Manar dake taso mata ta wuce su ta shiga kitchen tana sak'e². Da kallo suka bita dukansu,Manar ta tab'e baki ta d'auke kai,Waleed ya kalleta a hankali yace "kun rage wani abu ne?" Ta kallesa tana d'aure fuskarta tace "a'a" yayi shiru yana tunani kafin ya mik'e yabi bayanta,Manar ta bisa da kallo tana murmushin mugunta,yana zuwa ya ganta tsaye ta gama dubawa bata ga abunda suka dafa ba ko kayan da suka b'ata ma bata gani ba,tayi shiru tana tunanin ya za tayi dan wani muguwar yunwa ke cinta,shisa ta sakko babu shiri,yanzun kuma da kunya ta tambayesa breakfast tunda ya mata magana ita tace baza ta ci ba,ya shiga yana kallonta yace "za ki yi girkin ne?" Da sauri ta kallesa tace "wane girki?" Yace "i mean lunch" wani kallo ta dunga masa kafin tace "me zai hana kace ta maku" ya kalleta yace "me yasa ke baza kiyi ba?" Strictly tace "ka ga Waleed ban iya ba,and ko a gidanmu ba ni ke yi ba,maids suke mana komai.. Sannan gaskiya bazai yiwu yarinyar nan tana zuwa min gida ba,daga yau ka fad'a mata kada ta k'ara tako min cikin gida,i'm sorry to say but i dislike ur sis,na tsaneta wallahi with all my heart" kallonta Waleed ya dunga yi da wani expression,fuska a d'aure yace "u are looking into my face and telling me u hate my blood? Meye matsalarki da ita? Let me tell u this ba ki isa ki hana 'yan uwana zuwa gida na ba tunda ba gidan ki bane.. And duk ma yadda za kiyi kiyi ki girka musu lunch" a mugun fusace tace "It's better kai da ka damu suci ka tsaya ka girka musu ko kasa blood d'in taka ta girka,amma wallahi ni bazan yi ba dan banma tab'a yi ba" tana kai wa nan ta fice d'aga kitchen d'in a fusace ta koma sama,Waleed dake tsaye gurin da ta barsa ya fesar da wani hucin iska trying hard to control his temper ya gyad'a kai yace "i've got to screwup that soon" daga haka ya fice daga kitchen d'in,yana fita ya kalli Manar dake zaune har sannan idanunta a kan TV ya koma ya zauna kusa da ita yana calming kansa,sanda ya dai² ta nutsuwarsa yayi lowering voice d'insa a hankali yace "za ki mana lunch?" Ta girgirza masa kai tace "sai dai kayi kai" yana kallon eyeballs d'inta yace "will u teach me?" Ta gyad'a masa kai,yayi mata murmushi yace "okay! Sai anjima sai muje ko?" Ta gyad'a masa kai,ranar a gidan suka wuni sai after maghreb ya d'aukesu ya mayar da su gida,Dadda dai har suka zo gida bata bar mitar matarsa ta yi musu wulak'anci ba,yana ta ba ta hak'uri,yana yin parking ta fice daga motar da sauri fuska d'aure tana ci gaba da mitar ta..
Chapter 77 · 0% Book details