Sashe 119
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
su cikin ruwa tana kallonsa za tayi magana ya sake d'aukansu,yanda suka yi kyau a pic d'in yasa shi kissing wayan yana sakin mata lallausan murmushinsa,Waleed kam yana can yana latse y'ar mutane a mota,sanda ya gama luguiguita ta ya saketa yama Azaan horn,bud'e motar Azaan yayi ya fito ya bud'ewa Ameerah ta fito Manar tana kallonsa sai dariya take tuntsirawa,sanda ya rakota ya bud'e mata back seat ta shiga ya d'an kashe mata ido da alamar sai sun yi waya,ta d'an gyad'a masa kai a hankali tana satar kallon Waleed,Waleed ya sauke glass yace ma Azaan "malam kana fa zak'ewa da yawa" harararsa Azaan yayi ya juya ya shige motarsa,Waleed ya fara yin gaba yana kallon mirror yaga Ameerah duk ta wani sunne kai,ya d'an tab'e baki yace "munafuka.. Dubi yanda tayi kamar ta Allah" Ameerah ji tayi kamar motar ya bud'e ta nutse dan kunya,dai² get Waleed yayi horn,get keeper ya bud'e masa ya shige,yana yin parking Ameerah tayi saurin ficewa daga motar,lokacin Azaan ya shigo yayi parking,saurin wucewa Ameerah tayi bata ma jira wani ya gansu ba ta wuce b'angaren Dadda,Azaan ya fito ya kulle motar sai wani murmushi yake saki ya nufi cikin gidansu Waleed,da kyar Waleed ya saki Manar tana fitowa daga motar ta kwasa a guje tayi b'angaren Dadda tana shiga d'akinsu ta fad'a kan gado tana maida numfashi,Ameerah dake cire kaya za taje wanka ta tsaya kanta tana kallon yanda take maida numfashi a hankali ta bugi cinyarta,Manar ta bud'a idanu tana kallon Ameerah tace "meye?" Zaunawa Ameerah tayi kusa da ita tace "ke wai kin san me Yaa Azaan yamin kuwa?" Manar ta fara dariya ta tashi za ta fita,Ameerah tace "wallahi duk Yaya ne ya janyo min ni ko hannuna namiji bai tab'a tab'awa ba,amma yau har k'irji na sai da ya mammatse wallahi baki ji yanda suje min zafi ba duk sun yi ja wajen kan" dariya Manar ta dunga tuntsirawa sanda taje k'ofa ta waigo tace "na ki kad'an ne ni meye Yaya bai min ba? Wallahi ko shi Yaa Azaan d'in da ya samu dama ina jin zaiyi abunda yafi haka" Ameerah ta tashi tayi hanyar bathroom tace "ni dai Allah bazan k'ara binku ba,duk inda zaku ku tafi ku kad'ai" wani kallo Manar ta mata tace "munafuka wallahi kema kinji dad'i ni za ki rainama hankali" daga haka ta fice ta bar Ameerah tana dariya dan gaskiya ta san gaskiya Manar ta fad'a,ko yanzu ya kirata za ta iya binsa ya k'ara mammatseta. Kusan a tare suka shiga gidan Amaar dake sakkowa zai fita saboda ya gaji da zaman shi kad'ai su kuma dama ba wai suna fita yawo ba ne tun asali ya ci karo da su suna shigowa Azaan a gaba sai Waleed da kusan button hud'u na rigansa suke bud'e yana tafe yana shafa k'irjinsa yana sakin wani wicked smile,Amaar ya kallesu da kyau ya d'auke kai sanda Azaan yace ma Waleed "brother i'm coming let me took my bath please" Waleed ya gyad'a kai yace "alright" ya kwanta kan kujera har lokacin bai daina shafa k'irjinsa ba,Amaar dai ya kasa hak'uri yana kallon Azaan dake k'ok'arin wucewa sama yace "hey! Wai ina kuka je ne?" Azaan ya saki wani murmushi yace "ina ruwanka?" Da sauri yayi sama,zaunawa yayi kusa da Waleed dake lumshe idanu yace "brother ina kuka je ne?" 'Dago kai Waleed yayi ya kalleshi bai san sanda bakinsa ya kub'uce yace "kayi aure kawai malam ka daina tambayana inda naje" ya k'ara lumshe idanu,wani kallo Amaar ya dunga masa yace "ohh! Ni kuka mayar d'an iska kenan? Yayi muku kyau" daga haka ya mik'e ya fita. Afujajan Mama suka shigo gidan after sallar maghreb lokacin su Waleed suna parlor sai hira suke suna ma juna tsiya shi da Azaan,Amaar dai ya saka su gaba sai kallonsu yake ya buga tagumi da hannuwa biyu yana tausayin kansa shi da ko budurwa bai tab'a yi ba,har Mama ta shigo ta wuce stairs bata kula da su ba sai da suka yi ihu suna dariyan abunda Waleed ya fad'a na taliyar murji,ta waigo da sauri tana ganinsa ta furta "Waleed!" Da wani murya,Waleed da yaji maganarta ya d'ago ya kalleta,karon farko ya kalleta yaji gabansa yayi mugun fad'uwa saboda yanda yaga Mama ta rame ta yi duhu,da sauri ya tashi yana mata wani kallo yace "Mama! Kin yi rashin lafiya ne?" Kuka ne ya kufce mata,hankalin Waleed a d'an tashe ya rik'o hannunta ya jata suka nufi sama yana cewa su Azaan yana zuwa,sanda suka shiga bedroom d'inta ya zaunar da ita bakin gado ya rik'o hannunta yana kallonta yace "Mama tell me what's going wrong? Me ya same ki? Meye matsalar?" Cikin kuka Mama tace "Waleed ina ka shiga? Ka daina zuwa ka ganni? Ko a waya ka daina kirana bare kaji lafiya na? Laifin me nayi maka Waleed?" Wani ajiyar zuciya yayi yace "please Mama kiyi shiru" d'an sassauta kukan tayi tana kallonsa,ya kai hannu ya share mata hawaye,a hankali ya zauna sosai a gabanta yayi flexing legs d'insa,fuskarsa da d'an damuwa yace "Mama me yake faruwa?" Ajiyar zuciya tayi tana kallonsa sosai tace "Waleed" yace "na'am Mama" tayi shiru tana kallonsa da tunanin me za tace,can dai ta daure ganin ita yake kallo tace "ina son tambayarka wani abu ne,ban sani ba ko za ka iya min" yace "ki tambayi ko mene ne Mama if ina da iko da shi zan miki" a hankali tace "za ka iya min duk abunda nace ina so?" Ya gyad'a mata kai yace "ki fad'a kawai" kai tsaye tace "so nake ka saki yarinyar nan" wani zabura yayi ya mik'e tsaye yana kallonta Dldan ya gane wanda take nufi,Mama na ganin haka ta sake fashewa da kuka tace "dama na san baza ka tab'a iya min abunda nake so ba,shi kenan kaje tunda wasu sun fini" Waleed dake tsaye yana mata wani kallo yace "amma Mama" cikin kuka tace "dalla rufe min baki,munafuki ai na san dama baza ka tab'a iya goyon baya na ba,bakinku d'aya da ubanka" d'an numfashi ya fesar idanunsa har sun fara canjawa ya taking steps a hankali ya sake zama gabanta,da wani sanyayyan murya yace "Mama yanzun idan kin sa na saketa me kike so na fad'a ma Abba?" Ta kalleshi tayi shiru kamar tana tunani,ya kamo hannunta ya rik'e a hankali yace "Mama kinga lokacin da kika sa na auri Afiyah kinfi kowa sanin she's not my choice,and Manar kuma zab'in Abba ce,though na tab'a fad'a miki ina sonta ke kika hana na aureta,but yanzun ba ni da ikon sakinta,idan kin sa ni dole na saketa me kike so na fad'awa Abba?" Kallonsa ta dunga yi kafin ta sauke numfashi tace "shi kenan idan har baza ka iya sakinta ba,lallai in so ka dawo da Afiyah d'akinta" kallonta ya dunga yi ya kasa magana can dai ya daure yace "shikenan Mama zan dawo da ita in sha Allah" tana jin ya amsa tayi murmushi tana shafa kansa,shi dai duk bai so tace ya dawo da Afiyah ba dan a niyyarsa tunda ta kwashi k'afarta ta bar gidan bazai tab'a cewa ta dawo ba,because ya gaya mata dama ji ne bata yi ba,Mama sai murna take saboda k'udurinsu zai cika idan har Afiyah ta dawo gidan Waleed,gaba d'aya daren ta hanasa fita suna tare a d'akinta sai wani nan² take da shi kamar ta damu da shi,sai da dare yayi sosai yace zaije ya kwanta bacci yake ji,kafin ta kyalesa ya mata sallama ya fita. Washe gari around 8am jirginsu ya tashi zuwa India,duka gidan aka watse sai Mama kad'ai da y'ay'anta masu mugun hali,tunda suka taso su Waleed suke tsokanar Amaar,shi dai bai ce musu komai ba suka yi suka gama,sanda jirginsu ya sauka India manyan motoci suka tarar da za su d'aukesu zuwa yankin Vishakpatnam,kuzo kuga idon Dadda a India,sanda suka isa ana musu barka da zuwa,Dadda ba Indianci sai raba ido take ba ta jin yaren,gara Waleed da Amaar ma sai Manar da yake itama tayi zaman gidan Mommella a nan ta iya wasu abubuwan,Raj Jarood bn Maqbool da matarsa Rani Naheed sai *RANIA* k'anwar Azaan da aka haifa kusan tare da su Manar sun fito compound d'in gidan tarban bak'insu lokacin da motocinsu Dadda suka fara parking suka fito cikin mutunci aka dunga musu barka da zuwa kafin suka d'unguma gaba d'aya suka shiga cikin gidan sarautar,hadimai suka dunga shigowa da kayansu zuwa masauki,sanda aka zauna cikin makeken parlon aka fara gaisawa da harshen nasara,Mahmoud mijin Mommella shi ya gabatar da kowa ga Raj Jarood kafin suka d'unguma aka fara lunch a makeken table d'in da kaf sai da ya d'auke su duk yawansu,bayan an gama ciye² aka fara hira ana labarai,Dadda da rigima tace sai tayi magana ga ta muguwar comedian in ta fad'i abu dole sai Azaan yama iyayensa translation,suna ta dariya saboda su basu tab'a ganin Dadda ba,Ameerah anzo gidan surukai sai wani sunk'e kai take,Manar ta zungurota tace "dallah mene haka kuma?" Ameerah tace "ke kunya nake ji" Manar ta fara dariya,tana d'agowa suka had'a ido da Waleed ya lumshe mata idanuwa ya mata blowing kiss,murmushi tayi ta d'an kautar da kanta,Rania k'anwar Azaan ta tab'a Manar tace "kuzo muje d'aki na" suna tashi za su bar wajen Azaan ya taho ya gansu za su wuce ya rik'o hannun Ameerah ya jata bayan pillar yana mata wani kallo yace "ina za kuje?" Ta d'an sunkuyar da kanta tace "d'akinta za muje" ya gyad'a kai yace "okay! Anjima ku shirya za mu fita" saurin d'agowa tayi ta kalleshi,ya mata wink ya saketa ya wuce,da sauri tabi su Manar,makeken d'akinta Rania ta kaisu wanda aka masa adon golden hatta paint d'in d'akin,ba k'aramin burge su Manar d'akin yayi ba,suna ta kallon d'akin abun sha'awa kuma wai ita kad'ai take kwana cikinsa,gefe teddy bears ne da yawa anyi decorating d'akin da su,nan dai suka lalace suna ta hira. Da yamma kamar yanda Azaan ya fad'awa Ameerah,Waleed ya kira Manar yace su fito za suje unguwa da sauri,Manar da suka shirya cikin riga da skirt irin na India rigan har kusan kwaurinsu amma tana da tsaga ta tsakiya da ya kai har saman cibiya,sun sak'ala mayafai kayuwansu a bud'e,suna fitowa suka lek'a gurin iyayensu Mata suka