← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 168 OF 184

Sashe 168

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Since ta fara maganar Waleed yake mata wani kallon ki yi ki gama ba inda za ki kai min iyali,taji baice komai ba tayi mitsi² da idanuwa tace "amma Mamman da kai fa nake magana kak'i cewa komai?" Bai d'ago idanuwansa ba,hankalinsa akan waya yana amsa sak'on fatan alkhairi da barkan da Dr Mahfouz ya aiko masa though sunyi waya tun ranan da Manar d'in ta haihu yace "me kike so nace maki?" Ta karyar da kai cike da sanyin murya na son lallab'asa saboda ta fi kowa sanin halinsa tace "yo ai na ji ka yi shiru ne baka ce komai kan maganar da nayi ba" wani murmushi yayi yace "uhmn! Da ce maki akayi zan yi magana?" Yanda yayi maganar yasa ta jin haushi,a fusace tace "d'an walak'anci ai na san dama kana ji amsa ne babu" murmushi ya sake yi bai k'ara cewa komai ba yaci gaba da duba sak'onnin barkan da ake ta masa,ta gaji tace "tou ni dai ko ka yarda ko karka yarda,da amincewarka kou babu zan tafi da ita idan Allah ya kaimu gobe can b'angaren sarauniya" strictly yace "uhmn! A matsayinki na wa?" Saurin kallonsa duka occupants d'in parlon suka yi da tun farkon muhawaran nasu babu wanda ya saka musu baki,hasalima yi suka yi kamar basa gurin,ai kuwa nan Dadda ta hayayyak'o masa tace "a matsayina na uwar ubanka,kuma kakar matarka tunda kai baka d'auke ni mutum mai daraja ba" ya saki murmushi yace "wallahi ba da yawuna ba,kuma ko k'ofar bedroom d'inta ban amince ki fito da itaba,bare ki rabata da gidanta,idan wanka za ki mata me zaisa ace sai an fita daga gidan nan zuwa wani gurin? Ko kuma dai shi wankan ya zama wajibi ne ban sani ba?" Sakin baki Dadda tayi tana kallonsa,da haushi ya isheta kawai ta gyad'a kai bata k'ara cewa komai ba,idanuwanta cike taf da hawaye ta koma ta lafe a jikin kujera,tunda tayi shiru Ameerah ke kallonta tana k'unshe dariyan yanda taga fuskarta kamar za ta fashe da kuka,Manar ta kalleta ta kalli Waleed da hankalinsa ke kan wayarsa da yake dannawa,ta girgiza kai cike da rashin jin dad'i,sai dai bata ce masa komai ba,har suka gama hira su Ameerah suka musu sallama suka tafi,Dadda dai still ta kasa magana,Manar ta tashi ta wuce bedroom sanda ta gama shirin bacci ta fito sanye da pyjamas riga da wando masu kauri saboda sanyi ake yi sosai mai shiga k'ashi,a parlor ta samu Dadda ta takure guri d'aya har ta fara bacci,tayi ajiyar zuciya a hankali ta tsuguna gabanta ta fara tashinta,Dadda da baccinta ya fara nisa ta bud'a idanu tana salati,calmly Manar tace "Hjy ki tashi muje ki kwanta a d'aki nan akwai sanyi sosai" kamar jira Dadda take ta fashe da kukan da bata yi tun sanda akayi abun ba tana cewa "ashsha! Yi tafiyarki ki kwanta kawai ki barni,ko kashe ni sanyin zai yima ai ni na kawo kaina,da banzo ba baza'a walakanta ni ba.. In ba don haka ba har Mamman ya kalli idanuna ya gasa min magana.." Sai ta kuma kecewa da kuka,Manar ta sauke ajiyar zuciya tace "kiyi hak'uri Hjy,zan masa magana,yanzu ki tashi muje ki kwanta kinga dare ma ya yi sosai" da kyar ta samu ta lallab'a Dadda ta tashi suka wuce ciki tana cewa ita gobe² ma za ta koma inda ta fito baza ta iya zama a walak'antata ba haka kawai da gatanta,sanda Manar ta samu suka shiga bedroom d'inta tayi ajiyar zuciya ta zauna bakin gado,tana kallon Dadda ta wuce bathroom ta kama ruwa ta d'auro alwala then ta haura kan gadon ta kwanta tana karanto addu'o'in kwanciya bacci,itama addu'o'in tayi then ta musu deactivating fitilun suka kwanta Manar na d'an tambayarta mutanen gidansu,tun Dadda ba ta amsata har dai ta sauko ta fara ba ta labarin how al'amura suka kasance bayan tahowarsu nan,wasu tayi murmushi wasu taji haushi a haka bacci ya d'auke Dadda,Manar da taji shiru tayi murmushi tana tunanin ko Mother za ta zo kuwa? Ta yi nisa a tunanin lokacin kusan 12am taji an bud'e k'ofa,ta juya da sauri ta kalli yanda ya tsaya a door way,ta tab'e baki ta d'auke kanta,ya kusan 5 minutes a gurin kafin ya tako ya shigo,da wayarsa ya haskasu,Manar ce a farkon Dadda tana d'aya side d'in,ajiyar zuciya ya sauke ganin a kusa da ita ya tsaya,then ya d'an sunkuya kanta ya kirata calmly,tana jinsa ta masa banza dan d'azun ta mugun jin haushinsa,even though k'amshinsa ya mugun cikata,but haka ta danne ta ki basa space d'in da zai san idonta biyu,abunda bata sani ba kuma tun shigowarsa d'akin ya san ba bacci take ba,hatta juyawan da tayi ta kalleshi tsaf ya gani,da yaga ba ta da niyyar motsawa kawai ya d'agota yayi waje da ita kaman ya d'auki jaririya ya wuce bedroom d'insa da ita,yana shiga ya ajiyeta kan gadon ya zauna kusa da ita yana kallonta da wani murya yace "I knew u aren't getting any of what u are doing.. Ki bud'a idanunki ki min magana,me na miki ne kike jin haushi? Tun d'azun na kula dake da irin kallon da kike min" kamar dama jira take ya tsokano maganar,ta bud'a idanunta da sauri tana jan numfashi ta fesar a hankali,cikin muryanta mai sanyi tace "I don't know what really happened to u,me isa kan y'ar maganan da Hjy tayi maimakon ka mata a sannu har ta fahimta za ka nuna mata kai tsaye kaman bata isa ba? Don't u look shekarunta sunyi nauyin da sai muna binta a sannu? I think bai kamata ace kai da za kaga munyi ka hanamu ba kaine kake mata magana this way ba.. Me yasa haka ne Yaya?" Wani irin sanyayyan kallo yake binta da shi tunda ta fara maganar har tayi shiru ta zuba masa na ta idanuwan tana jiran taji ya yi magana,a nutse ya sauke numfashi,idanuwansa har sannan a kanta yace "ohhh! Akan wannan kike fushi kenan?" Da d'an k'arfi like ranta har sannan a b'ace tace "ya bazan ji haushi ba tsakani da Allah? Matar nan fa saboda mu tazo nan,me isa kuma za mu b'ata mata rai fisabilillah?" Tab'e baki yayi because shi dai ya san duk abunda yayi baiyi da niyyan ya b'ata mata ba,he just said that saboda bai son ma ta fara kawo maganar raba musu gida,shi dai bai ce baza'a mata wanka ba,kawai maganar tafiya da su side d'in Rani Naheed ne bai so yayi nisan da za su sa ya amsa ba da son ransa ba,so sai kuma akayi rashin sa'a duk sun fahimcesa a bai²,da wani sanyayyan voice ya kai hannu ya janyota jikinsa while saying "ke a tunaninki na yi haka saboda na b'ata mata rai?" Da sauri ta gyad'a masa kai,ya gyad'a kai shima yana sauke numfashi yace "lallai idan haka ne duk kun fahimci al'amarin ba dai² ba" saurin d'ago kanta tayi tana kallonsa tace "kamar ya?" Ya lumshe idanuwansa yace "kamar yanda kika ji" wara masa idanuwa tayi tace "i didn't get u" a hankali ya bud'e idanunsa ya sauke su a kanta,kamar bazai ce mata komai ba then kuma sai ya fara mata bayanin dalilinsa har ta fahimta,a nutse suka sauke ajiyar zuciya tare ta k'ara yin luf a jikinsa tana shak'ar k'amshinsa dake k'ara mata nutsuwar zuciya,lokaci d'aya wani irin bacci ya fara kawo mata ziyara,a hankali take sakin hamma,har sanda baccin yayi gaba da ita yana rungume da ita yana shafa ta. Da safe sanda yaje gaisar da Dadda k'in kulasa tayi saboda har lokacin bata bar jin haushinsa ba,sai da ya ba ta hak'uri da dabara ya mata bayanin dalilinsa na k'in amincewa su tafi b'angaren Rani,a cewarsa ai bai kamata suje can sun takurasu ba suyi zamansu a nan kawai ai zai fi,da ya gama mata bayanin ya samu ta sauka daga mugun fushin da ta fara yi da shi,here ya zauna suka d'anyi hira ma,can ta kallesa tace ita ya nuna mata mad'bak,da sauri Waleed dake satan kallon Manar tun shigowarsa tana bacci ya kalleta yace "me za kiyi a mad'bak kuma Hjy?" Tace "iiiihh! Yo girki zan ma Manar mana" yayi murmushi yace "kiyi zamanki ki huta komai kike so akwai masu yi a nan" baki sake ta kallesa tace "me suke yi?" Yace "everything!" Wani kallo ta masa tace "meye hakan kuma?" Manar da farkawanta a bacci kenan tana jinsu bata san sanda ta fashe da dariya ba,Dadda ta d'aure fuska tana jiran amsansa,yayi murmushi yace "na fad'a maki komai suna yi" sanda ta karkace kai tace "sun iya tuwo?" Da sauri ya kalleta sai kuma ya girgiza mata kai yana tab'e baki,ta tab'e baki itama tace "aikin banza dama me suka iya in ba jagwalgwalon turawa ba? Allah na tuba wannan har abincin da ya kamata mai jego taci ne?" Yanda take magana yasa suka fashe da dariya,Manar har da hawaye,Dadda ta tsuke fuska tace "ka ga tashi muje ka gwada min inda mad'bak yake yanzu na shirya mata abinci mai rai da lafiya,wanda zai gina mata jiki" Manar dai couldn't help it dariya kawai take musu yanda taga Dadda ta dage,Waleed ya tab'e baki yace "muje to in ba rakaki nayi ba na ga alama baza ki hak'ura ba" tace "na ji dai muje" tasa shi gaba suka fita,Manar ta sauko daga gadon tana goge hawaye ta shiga bathroom,sanda ya rakata suka dawo tare yana cewa "tou ke yanzu in banda rigimanki ma Hjy ina za ki samu wani abun da za kiyi tuwo da shi a nan tunda ba Nigeria kike ba?" Bata kallesa ba tace "ka tsaya kai kallo Malam,ni nan da ka ganni da komai na nake tafe.. Yo Allah na tuba mu da mukayi zaman saudiyya ina ne za mu shiga mu kasa rayuwa?" Ya jinjina kai yace "babu kam" tace "aatooh! Ai shi isa nake fad'a maka dama" suka shigo d'akin tare,Manar dake fitowa bathroom sai murmushi take musu,ya bita da wani adorable kallo sanda ta koma kan gado ta zauna tana k'ara jan bargo ta rufa,Dadda dai bata kalle su ba ta wuce gurin jakunkunanta ta janyo wani ta ajiye,sanda ta zuge ta fara fito da kaya,su man shanu soyayye da aka d'urasa a gallon,yajin daddawa da su kukarta mai kyau da kub'ewa
Chapter 168 · 0% Book details