Sashe 74
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
kai tayi tace "haba don Allah sai ka wani buga min pillow kamar za ka tada k'ato? Kai baza ka iya min a hankali har na tashi ba?" From head har toes d'inta ya dunga kallonta,ta tab'e baki ta kalli agogo,cike da tsiwa tace "sallah kuma tunda na san wajibi ne a kaina ai dai dole nayi ko k'arfe nawa ne" da mamaki yake kallonta yace "a gidan ku kina kaiwa har k'arfe goma baki yi sallah ba?" A fusace tace "toh gajiyan daka tara min fa zai barni na iya tashi yin sallah da wuri aka ce maka? Please Waleed ba fa haka ake treating new bride ba,u are not romantic at all wallahi,haba don Allah sai kace ba namiji ba kai" wani kallo kawai yake mata fuskarsa a d'aure yana kad'a mata index finger yace "look Afiyah i won't tolerate this,a gidana kina min wannan iskancin bazan d'auka ba idan kin saba haka a gidanku ni daka ki zanyi kin sani.. Tun asuba na shigo na tashe ki kiyi sallah shi ne har yanzu baki yi ba,is this ur home training?" Wani kallo ta dunga masa daga sama har k'asa tace "kai don Allah baka ji kunya ba?" Ta yatsine fuska tana kallonsa tace "wani wai tun asuba ka shigo ka tashe ni,ain't u ashamed of ur self please?" Tsaki tayi ta sauka daga gadon da y'ar figigiyar rigar baccinta za ta nufi bathroom,ya fizgota da k'arfi ta dawo yana kallonta ransa a b'ace ya cillata gadon,ya fara k'ok'arin cire jallabiyar jikinsa,ta matsa k'arshen gadon da sauri cike da tsoro tace "me za ka min?" Ya mata wani kallo bai ce komai ba ya bita saman gadon,tsoro fal idanunta tace "Waleed stop" yace "ni sa'anki ne?" Da sauri ta girgiza masa kai,yayi k'wafa ya sauka sanda ya juya zai fita yace "ki same ni downstairs yanzu idan kin gama" daga haka ya fice ya bar mata d'akin yana gyara rigarsa,yana sakkowa Dadda ta mik'e tana kallonsa tace "wai ka ji daga nace amaryar baza ta fito gaisheni ba har yanzu,shi ne wannan mata take min fad'a kamar ta haife ni,ni dai gaskiya Mamman idan baza mu zauna lafiya da ita ba sai ince mata ta tafi na sameta a gida,don da kyar ma idan ba kwana zan yi a nan ba gaskiya,tunda dai ga d'akuna nan birjik a gidan" Waleed ya k'arasa ya kunna TV yace "za ta sakko yanzu ta gaishe ki" Dadda ta koma kan kujera ta zauna ta tsuke fuska tana kallon TV,zaunawa Waleed yayi kan kujera yana kallon Manar ta gefen ido,ta b'ata rai sai turo baki take,wani murmushi yayi jin footsteps a stairs ya juya,Afiyah ce take sakkowa sanye da riga da wani crazy jean damamme,tana ganinsu tayi still a gurin,Dadda tayi mitsi² da ido tana kallonta da kyau itama,Afiyah ta d'auke kai ta k'arasa sakkowa ta shigo cikin parlon,Waleed ya kalleta yace "meet my grandma and my lil sis Manar.." Dadda ta washe baki tace "sannu Amarya! An tashi lafiya?" D'auke kai Afiyah tayi ta tab'e baki murya can k'asan throat tace "ina kwana?" Dadda tace "lafiya lao,sai dai ko sunan ki ban sani ba har yau" a hankali tace "Afeeyah" Dadda tace "To Safiyah Mamman dai ga shi nan kin tsinci dami a akala,ni nayi wahala da shi tun yana lab'ub'unsa,wahalar da nayi da shi kuwa wallahi sai dai Allah ya ban ladan,amma banda nak'udarsa Babu abunda Asama'u tayi masa kiji in fad'a miki" d'aure fuska Waleed yayi yana kallonta,Afiyah tayi sauri ta mik'e za ta wuce sama tace "sai an jima Hjy ina aiki a sama" kallon Waleed Dadda tayi,ya kalli Afiyah fuskarsa a murtuke yace "mind u,aikin da kike ya fi su muhimmanci ne?" Dadda ta gyad'a kai tace "aatooo! Gara dai ka tambayeta muji idan aikin ya fi mu daraja da k'ima" Afiyah ta d'an tab'e baki tace "this is not my business.. Zan je nayi abunda ke gabana.." Da sauri Dadda tace "ba zancen kije kiyi abunda ke gaban ki ba y'ar nan,kinga yanzu dai ko karyawa ba mu yi ba muka fito gidan,Manar ma da kyar na tado ta muka taho,ko d'an baccin safen nan da ake yi ban bari ta yisa ba.." Manar na kallon Dadda tace "ni kin ji na ce maki ina jin yunwa ne,ko wani ya fad'a miki ban ci abinci ba?" Wani matsiyacin kallo Afiyah ta jefa mata ta kalli Dadda bluntly tace "eyyyahhh! Ai kam sai dai kuyi hak'uri dan ba komai a gidan yanzu haka" wani kallo Waleed ya dunga mata trying hard to control his temper,Dadda ta bud'e baki tana kallonsa tace "toh me kuka ci a gidan ku?" Afiyah dai tuni tayi wucewarta sama bata ma tsaya sauraren Dadda ba saboda kallon da taga Waleed yana mata,tana wuce ya mik'e da sauri ya bi bayanta,yana shiga d'akin ya kulle k'ofar yana nunata da yatsa cikin tsawa yace "let me give u this warning Afiyah,if u don't want to show the other side of me u've got to respect my family,albarkacinsu ya sa zan kyaleki yanzu,but na rantse da Allah zan yi taking action d'in da zai mugun ba ki mamaki idan baki maida hankalin ki jikinki ba,breakfast kuma nace ki je ki had'a masu yanzun nan kafin na chanja shawara.." Ya k'are maganar a fusace yana kallonta,gaba d'aya ta gama tsorata sai kallonsa take tana komawa baya,lokaci d'aya hawaye suka kawo idanunta ta fashe da kuka mai cin rai,ya d'auke kansa da sauri zuciyarsa tana bugawa,right from time a rayuwarsa ya tsani ganin hawayen mace,ya sassauta muryarsa a hankali yace "u know babu yanda za'ayi y'an uwanki su zo nayi musu gaisuwar wulak'ancin da kika ma grandma dit'a right?" Ta d'aure fuskarta tace "amma kana ganin wannan yarinyar fa ko gaisheni bata yi ba" shiru yayi da farkon sai kuma yace "mind u ba sunanta kenan ba" tace "wace ce d'in ka ita?" Ya kalleta da kyau yace "she is my cousin sis" wani kallo ta dunga masa,ya gyad'a mata kai,ta tab'e baki kad'an bata ce komai ba ta juya,yace "ki fito ki had'a musu breakfast" daga haka ya juya zai fita,ta waiga ta bisa da kallo,Allah ya sani so ba na wasa ba take masa,tun ganin farko da ta masa a gidansu taji idan ba shi kamar baza ta iya rayuwa ba,dan haka take jin za ta iya yin komai a kansa. Waleed yana dawowa parlon ya tadda Manar ita kad'ai tana kallo,tun da ta kallesa sau d'aya ta d'auke kanta,ya k'arasa kusa da ita yace "me yasa baki gaida Afiyah ba?" Ta turo baki ta k'i cewa komai,da k'arfi ya daki kujeran da take zaune yana kallonta da kyau yace "look! Duk sanda kika zo gidan nan dolene ki gaidata because she is my wife.. Kin ji abinda nace?" Ta had'e rai bata yarda sun had'a ido ba tace "why will i greet her? Beside ko kallona fa bata yi ba,shisa nima nak'i gaisheta tunda ba wajenta muka zo ba.." Kallonta kawai yake ganin yanda take masa magana cike da tsiwa,ya d'auke kai yana sakin murmushi,zai yi magana ya ji motsi a kitchen ya kalli gurin kafin ya mik'e da sauri ya nufi gurin,seeing Dadda alone tana magana,ya tsaya a door way yana kallonta yana sakin murmushi,tana k'ok'arin kunna gas take cewa "idan ba jaraba irin na Mamman ba da safen ma bazai iya hak'uri ba,shi ne ya kama ya bi figaggiyar zabiyar matarsa d'aki bayan tare suka kwana daren jiya k'wak'ume da juna,yana ji fa nace masa ban karya ba ga yarinya na taho da ita itama bata karya ba,dama da ya ta yarda ta biyoni ma muka zo fisabilillhi.."