Sashe 68
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
"korata kike yi ne?" Tace "to ai gani nayi dare ya yi" yace "yanzu zamu wuce" tace "kai da wa?" Yace "matar gidan" ta bud'a ido da kyau tace "Iiiiiihhh! Tare kuke dama?" Yace "ehh! Na barta a nan naje asibiti" tace "amma shi ne ko ta zo gaishe ni?" Ya kalleta yace "bata shigo ba?" Ta girgiza kai tace "nace maka ko kyallinta ban gani ba" yace "but mun shigo d'azun akace kinje masjeed,thought za ta sake zuwa da kika dawo" Dadda ta kyab'e baki tace "to ni dai ban ganta ba wallahi" ya gyad'a kai ya tashi da sauri yace "ina zuwa Hjy" tace "Iiiiiihhh ba sallama za muyi ka tafi ba?" Yace "um'um yanzu zan dawo" ya fita da sauri,sanda ya shiga gidan bai samesu parlor ba ya haura sama yayi knocking bedroom d'in Mama kafin ya tura k'ofar ya shiga da sallama,Mama ta d'ago rai b'ace tana k'are masa kallo ya k'arasa ya gaisheta,ko amsawa bata yi ba ta fara zazzaga masa ruwan bala'i,ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba,sanda ta gangaro kan maganar da suka yi da Afiyah bayan tafiyarsa d'azun tace "yanzu Waleed abunda za ka saka min da shi kenan?" Ya sunkuyar da kansa k'asa yace "me nayi Mama?" Tace "dama ai ka fad'a min ba tun yanzun ba,muddin na dage akan maganar aurenka da k'afarta sai ta bar maka gidanka,saboda ka nuna ma duniya ba ni da muhimmanci a gurinka shisa tunda kayi aure baka tab'a had'a shimfid'a da ita ba?" Saurin d'agowa yayi ya kalli Afiyah dake cike fam yace "get set za mu wuce yanzu" yi tayi kamar bata jisa ba,ya kalleta bai dai ce komai ba though ransa ya b'aci da halin ko in kula da ta nuna masa,Mama ta kallesa tace "yanzu Waleed irin sakayyar da zaka min kenan?" Ya d'ago da sauri yace "Mama!" A fusace tace "wane Mama za ka cemin? Zaifi maka ka kira ni da sunan da uba na ya rad'a min kawai shi ne zan san wuyanka ya yi kauri" ya dunga kallon Afiyah ya kasa cewa komai saboda bai so Mama tayi masa fad'an a gabanta ba,yayi ajiyar zuciya a hankali yace "i'm sorry Mama" cikin fad'a tace "ba hakur'in ka na damu da shi ba,ni abu d'aya kawai nake so daga yau naji an samu canji shi ne kawai zaisa nayi hak'uri" gyad'a mata kai yayi yace "in sha Allah za'a gyara" tace "idan baka gyara ba ai ni na san matakin da zan d'auka" shi dai bai sake cewa komai ba sai hakur'in da yayi ta bata,ganin duk ya damu da fad'anta ta sassauta masa suka yi mata sallama suka fita,zuciyarsa banda suya babu abunda yake masa,ko kallonta bai kuma yi ba ya wuce forefront ta bisa a baya..