Sashe 16
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani irin yammm yaji jikinsa yana yi,da sauri ya fizge hannunsa,ta sake kawo hannu za ta rik'esa ransa a b'ace yana mata wani kallo a kausashe yace "don't dare touch me!" Rau² idanunta suka yi da muryar kuka tace "Yaya!" Tsawa ya mata "be quite!" Jikinta har b'ari yake tsabar tsoron da maganarsa yasa taji,tana sakin wani irin kuka mai tsuma zuciya ta juya da niyyar barin gurin yayi saurin fizgota,k'ara ta fasa ta k'ank'ame jikinta she thought ko zai daketa ne,da sauri ya waiwaya yana kalle²,kafin tayi wani maganar tuni ya jata da sauri ya nufi backyard,a jikin apartment d'in Dadda ya tsayar da ita yana mata wani kallo ransa kamar a b'ace yace "me zan miki?" Sheshshek'ar kuka ta fara tak'i masa magana,sanda tayi mai isarta kafin tayi shiru,ya nad'e hannunsa a k'irjinsa ya zuba mata idanunsa da suka fara juyawa,sanda ta fara gajiya da tsayuwar a hankali ta zumb'uro baki still kuma bata da niyyar cewa wani abu,almost 15 minutes suna ta tsaye babu wanda yace da wani k'ala kafin Manar ta shawaran tafiya ba tare da ta yi masa magana ba ta fara k'ok'arin barin gurin,saurin rik'ota yayi ya dawo da ita,fuskarsa babu alamun wasa ya zuba mata idanunsa masu cike da kwarjini fuskarsan nan a daure still kuma har lokacin bai ji zai iya yi mata magana ba,idanunta ta d'aga tana kallonsa a shagwab'e tace "Yaya!" Yace "Uhn!" Ya d'aga mata girorinsa,ta k'ara narke murya tace "ina son tafiya" wani kallo ya mata yace "na ba-ki izini?" Ta dunga kallonsa kamar za tayi kuka tace "to ai na gaji da tsayuwa" kamar bai gane me take fad'a ba ya sake d'aga mata gira,kuka ta fara yi mara sauti sanda ta shammacesa tayi wuf za ta gudu,taji ya rik'o arm d'inta da k'arfi ya dawo da ita,fuskarsa a d'aure yace "u have nowhere to go girl!" Kuka ta fashe da shi bata gane me yace ba,da wani braking voice tace "to ni fa na gaji,kuma kak'i bari na tafi" wani murmushi yayi ya d'aga gira yace "hukuncinki kenan" saurin kallonsa tayi tana tsayar da kukan tace "ni me nayi maka to?" Yace "u have no idea?" Ta zuba masa idanu tak'i cewa komai,a d'an tsawace yace "ba dake nake ba?" Zumb'uro baki tayi tace "to ni na ji me kace ne?" Ya bud'a idanunsa yana kallonta yace "baki sani ba?" Ta gyad'a masa kai,gyad'a kai shima yayi kafin yace "wancan ranar me ya had'a ku fad'a,da zan aika a kiraki kik'i zuwa?" Squeezing fuskarta ta fara kafin ta b'ata rai tace "to ba su bane dai daga zuwa suka fara fad'a mana magana" idanunsa akanta yace "suka ce me?" Tayi shiru tak'i cewa komai sai da ya mata tsawa,a shagwab'e tace "kawai daga na tambayi Ameerah lokacin ba da su nake ba na ce har ta dawo? Ameerah tace kai sis mun dad'e fa a skul d'in tun 7am muka fita,na san time d'in ma ko juyin farko baki yi ba shi ne wannan Deejan ta tab'e baki tana mana kallon banza tace ya ma za'ayi ta sani tunda babu fuss! Ita kuma Diyanah tace dama tunda an fi ganewa a tafi wani duniyar karuwanci a b'ige da karb'an sabil ana cewa sana'a ake ai baza'a san komai ba,haka za azo a koma cikin duhun jahilci shi ne suka dunga mana dariya,sai ita Deejan ta sake cewa ai ko yanzu ma sis Diyanah kada ki fitar da tsammanin kamosu aka yi aka dawo da su,basu yi niyyar dawowa ba shi ne Diyanah ta dunga dariya har tana rik'e ciki tace wai kina nufin sun zama *TAKARI?* Shi ne dan Ameerah tace musu wannan ai ba yi bane,me yasa za kuna fad'an irin maganganun nan? Shi ne Diyanah tace an fad'a d'in ko akwai abunda za kiyi? Da Ameerah tace babu abunda zanyi zan dai fad'awa Abba muddin baku daina ba,shi ne Deejah tace ai dama dole Ameerah ta tare min,tunda an tab'a k'anwar uwarta,shi ne dan Ameerah tace mata a'a Deejah kada mu kai nan,duk abunda za ku fad'a ya tsaya iya kanmu,amma kada ki kuskura ki k'ara saka iyayen mu,shi ne ita Deejan a tsiwace tace idan an tab'a me za ki iya yi? Ameerah tace sai kin gwada zan nuna miki abunda zanyi suka yi dariya su biyun suka tafa Diyanah tace kin ji fa sis kamar za ta iya mana wani abu,duk fa kwad'ayi ne yasa ta shiga maganar itama Deejah tace ke rabu da su kwad'ayi dai mabud'in wahala,idan ma za ku hak'ura da abunda kuke da shi ku zauna ku rungumi rayuwarku zai fi muku,amma kuna biyewa waccan tsohuwar tana d'ora ku turba mara kyau,duk sai kun yi dana sani a lokacin da bazai muku amfani ba" kallon bakinta ya dunga yi sanda yaji ta yi shiru yayi ajiyar zuciya yace "uhn! Daga nan sai aka yi yaya?" Manar dai sai cika take kamar yanzun abun yake kan faruwa tace "shi ne ni kuma na cakumo wuyanta,muka kama kokawa,nace wa take cema waccan tsohuwar?" Wani kallo ya dunga binta da shi kafin yace "su kuma sauran me ya had'a su?" Tace "Diyanah ce take k'ok'arin shigarwa Deejah,shi ne Ameerah ta tareta tace baza su min taron dangi ba,itama tana da wanda za su shigar mata,sai ita Diyanan tace ta matsa kafin ta bigeta,shi ne dan Ameerah tace wa za ta bige? Ai sai dai su buge juna,shi ne sai Diyanah ta ture Ameerah da k'arfi saura k'iris ta fad'i k'asa,da ta d'ago shi ne ta fizgo Diyanah,ita kuma Diyanah tana juyawa sai ta kai mata mari,da bata sameta ba shi ne itama Ameerah ta kai mata marin ita sai ta sameta,daga nan sai suka fara kokawa" Waleed dake saurarenta jin ta yi shiru yace "Uhn! Daga nan sai mene ya faru?" Tace "shi ne sai ka fito za ka tafi masjeed,ka ganmu muna fad'a.." Gyad'a kai yayi yace "and by then nace kar na dawo ban ganku a gurin ba,da yake kunnen k'ashi gareki sai kika k'i zuwa,saboda kina da wanda za ta d'aure miki k'ugu ko?" B'ata rai tayi tace "a'a" yace "haka ne mana" girgiza kai tayi za tayi magana ya maka mata tsawa yace "am i lied,ba haka bane?" Duk da yadda jikinta yake b'ari bata fasa bashi amsa ba "to ni ai ba-ni na fad'a mata ba" wani kallo ya dunga mata yace "idan baki fad'a mata ba ya akayi ta sani?" Idanunta suna kawo k'walla tace "to ba Ameerah kasa ta kira ni ba,shi ne Dadda ta tambayeta da tace kai ne kace nazo,tace me zanyi maka? Shi ne ta fad'a mata komai" tab'e baki yayi yace "matsalar duk maganar ki sai da shi ne ya fi yawa,taya zan gasgata abunda kika fad'a?" Sabon kuka ta sakin masa da sauri ta fad'a jikinsa tace "ni fa ban maka k'arya ba,kuma ma idan baka yarda ba ka tambayi Ameerah ko su" tamkar ginannen dutsen da aka kafe haka ya daskare ya kasa cewa komai cikin y'an mintuna jikinsa ya yi wani irin mutuwa,jinta kwance a jikinsa da sautin kukanta dake ratsasa nan da nan jikinsa ya fara wani irin vibrating kamar wanda ake jijjigawa,da sauri ta d'ago kanta tana kallonsa,a tsorace ta dunga share hawaye tace "Yaya!" Runtse idanunsa yayi da wani irin shak'ak'k'en murya yace "jeki!" Tsayawa tayi ta kasa tafiya,da wani irin murya ta sake cewa "Yaya! Me yake damunka?" A tsawace yace "bar nan nace" kuka ta sake fashewa da shi za ta rik'esa ya bud'e idanunsa da sauri,a tsorace ta koma baya ganin yadda idanunsa suka yi ja,ya zuba mata su yana binta da wani kallo mai cike da warning,babu shiri ta juya da sauri tana waiwayensa ta fara tafiya,komawa yayi ya jingina bayansa da bango a hankali yana sauke wasu irin ajiyar zuciya,sanda ya tabbatar ta bar gurin kafin ya juya ya bar gurin shima,ta backyard ya bi sai da ya kai apartment d'insu sannan ya zagaya ya shige,ko mutum d'aya bai tarar a parlon k'asa ba,ya haura sama cikin sauri kamar wanda ake hankad'awa ya shige bedroom d'insa yayi locking k'ofar ta ciki yabar key d'in a jiki,direct ya nufi bathroom bai ko tsaya cire kayan da suke jikinsa ba ya sakarwa kansa ruwa cold one,yadda ruwan yake sauka jikinsa haka yake jin sanyinsa yana ratsa jikinsa,for about 10 minutes ruwan yana sauka jikinsa then ya matsa ya cire jik'ak'k'en kayan ya jefasu washing machine ya d'aura towel ya fita,ya zauna bakin bed da duka hannuwansa ya rufe fuskarsa ya dunga sauke wani irin ajiyar zuciya kamar wanda yayi kuka then ya kife ya zubawa roofing d'akin ido. Da safe sanda ya fito kafin ya bar gidan sai da ya fara nufar apartment d'in Dadda because bai manta warning da Abba ya masa ba,yayi sallama bai jira a amsa ba ya shiga fuskarsa a d'aure,as usual kwance kan kujera ya sameta ta k'ure TV da idanunta tana sanye da gantalallun kayanta,kallo d'aya yayi mata ya d'auke kansa ya zauna kan kujera yana lumshe idanuwansa,ta d'ago da sauri jin mutum ya shigo ganin shi ne ta masa murmushi tace "Yaya ina kwana?" Kadaham kadahan ya amsa yana sake d'aure fuskarsa gudun kada taga fuska tace za ta zo jikinsa,daga haka babu wanda ya sake magana ta koma ta kwanta guiwoyinta a sanyaye ta ci gaba da kallonta,shi ma yayi shiru sai wayarsa da ya ciro ya fara dannawa,Dadda ta fito kitchen rik'e da plate da aka cikasa da farfesun kayan ciki k'amshin garlic sai tashi yake kamar shi kad'ai akasa ciki,tun kafin ta k'araso ta hangosa ta washe baki hak'orin makkanta suka fito tace "a'a Mamman maraba" kwantar da kansa yayi yak'i cewa komai,ta k'araso tana kallonsa tace "to me kuma ya faru kana ji ina maka magana ka share ni?" Ya d'ago kansa ba tare da ya saki fuskarsa ba har sannan yace "ina kwana?" Da fara'a sosai a fuskarta tace "lafiya lau,ka tashi lafiya?" A can k'arshen throat ya amsa "alhamdulillah" tace "har anyi shirin fitar ne?" Yace "ehh" daga haka ya mik'e,Dadda tayi saurin kallonsa tace "ko a zuba maka farfesun kaima?" Kai ya girgiza mata ya juya ya nufi k'ofa,ta bisa da kallo baki sake,har ya kusa fita ya waigo yaga shi take kallo yayi squeezing fuskarsa kamar