← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 184

Sashe 34

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ware idanunsa akan bayanta,idanunta a rufe tana jira ya gama ta ji shiru,a hankali cike da tsoro duk da muryarta ba ta fita tace "Yaya!" Kasa amsawa yayi duk da he clearly heared her,ta sake cewa "Yaya" sanda taji ya k'i mata magana muryarta tana rawa tace "Yaya na zauna? K'afafuna sun rik'e" ya ja numfashi ya fesar a hankali yace "stay still" da kyar ya daure ya mata alluran,sanda ya tsira bata ji zafi ba,sai da ya zare ta kuwa fasa masa kuka,da sauri ta juya ta fad'a jikinsa,yace "sake ni ki murza gurin" a shagwab'e duk ta k'ank'amesa tace "ni ka murza mun bazan iya ba" jikinsa duk ya mutu da kyar ya kai hannunsa gurin ya fara mulmula mata,ta kulle idanunta da k'arfi tace "assshhh! Yaya da zafi kake min fa" da wani murya mai nuni da mutum baya cikin hayyacinsa yace "oohh! Sorry" taji yana sake cuddling nata jikinsa kuma was vibrating a little,da sauri ta tureshi tace "Yaya!" Ta koma bakin gadon ta zauna tana zumb'uro masa baki,bai iya ce mata komai ba ya juya da kyar ya kwashe kwalbar alluran ya fita. Hjy Dadda zaune a parlor ita da Abba da Aunty suna magana,ya fito zai wuce Abba ya kirasa,bai iya amsawa ba ya tsaya because ya san dole a ganosa,Abba yace "ka gama ne?" Yace "ehh Abba" Abba yace "ina wayarta daka karb'a?" Idanunsa a k'asa yace "suna can gida" Abba yace "ka d'auko ka kawo min" ya amsa ya fita ransa a b'ace,bai dawo ba sai da yayi wanka ya shirya,ya shigo parlon sanye cikin k'ananun kaya ya tarar da Dadda ita kad'ai tana goge²,ba tare da ya kalli inda take ba ya wuce ya nufi hanyar d'aki,ta d'aga kai ta bisa da kallo tak'i kulasa,da ya shiga yaga tana bacci bai tsaya ba ya fito,ya kalli Dadda dake aikinta tana wak'e irin na mutan da,ya tab'e baki yace "Abba fa?" Kamar tana jira ya yi da ita a fusace tace "yo Allah na tuba shi Yaron asararre ne da zai ta zama yana jiranka kamar wani kai ka haifesa?" Bai tanka ta ba ya nufi k'ofa yana fad'a mata dosage d'in maganin Manar,yana gamawa ya sa kai ya fice. Manar tana jin fitarsa ta bud'e idanunta tana hararan k'ofa,ta zumb'uro baki ta tura hannunta k'asan pillow ta d'auko wayar da Ameerah ta kawo mata kafin ta tafi skul,number Azaan kad'ai ne a call log tayi dialing ta fara kiransa,yana ganin kiran ya katse ya kira back,ta d'auka ta kai wayar kunnenta,a hankali tace "Yaya!" Yayi still jin muryarta kamar mai rad'a yace "Baby! Ya kike?" Tace "lafiya lao" jin ta sake masa magana a haka yace "me ya samu muryanki naji shi haka?" Hawaye suka fara kawowa idanunta ta kai hannu ta share tace "ba ni da lafiya" yace "Subhanallah! Me ya sameki?" Da muryar kuka² tace "zazzab'i da ciwon kai" yace "eyyahh sannu! Allahu k'ara lafiya" tace "ameen!" Yace "kin yi kuka da yawa ko?" Ta gyad'a kai kamar yana kusa da ita a shagwab'e tace "to ba Yaya ne yasa nayi ba" yace "me yasa kika yi?" Tace "kukan" yayi shiru yana tunani kafin yace "me kika masa? Na san maybe kin masa laifi ko?" Ta girgiza kai tace "ni fa ban masa komai ba" yace "no! Tell me the truth" zumb'uro baki tayi tace "nifa banji me kace ba" yayi murmushi yace "fad'amin gaskiya nace" ta kyab'e baki tace "to ba wayana daka sa a k'ara kawomin ya kuma kwace min ba" murmushi yayi yace "shi ne yasa kika yi kuka?" Tace "ehh!" A shagwab'e irin yadda sakarkarun yara keyi,yayi murmushi yace "anya baki masa laifi ba baby?" Tace "nifa ban masa komai ba,shi ne dai yake takura ni" a hankali ya lumshe idanunsa yana tuno lokacin yarintarsu,rashin jituwarsu da fad'an da suke akan Manar tun sanda ya zo Nigeria,haka komai ya dunga dawo masa fresh kamar yanzun yake kan faruwa,taji ya yi shiru bai ce mata komai ba tace "Yaya" a hankali ya bud'e idanunsa yace "Na'am! Guddi (absolute beauty)" zumb'uro baki tayi tace "me kace?" Ya dafe forehead d'insa yace "sorry baby! Ba wani abu nace ba" tace "amma ai ka yi magana" yayi murmushi yace "na manta abunda nace ko za ki tuna min?" Ta tab'e baki tace "me zan tuna maka?" Yace "abunda kika ji na ce" tace "to ni na ji me kace ne?" Yace "okay! Tunda baki ji ba shi kenan" kulle idanunta tayi a hankali tace "Yaya bacci zan yi" yace "ok! Sleep tight,Allah kara sauk'i" ta tab'e baki bata amsa ba ta fara kashewa. Da dare Waleed ya dawo a gajiye ya samu Abba zaune a parlor yayi sallama,Abba ya amsa yana kallonsa bai ce masa komai ba,Waleed yace "barka da hutawa Abba" yace "yawwa! Ka dawo?" Yace "ehh Abba!" Abba ya gyad'a kai yace "ya aikin?" Yace "alhmdllh" Abba yace "ina maganar da muka yi da safe?" Kansa a k'asa yace "na je can ban sameka ba" Abba ya d'ago yana kallonsa yace "ya za'ayi ka sameni dama,ko kuwa zanyi ta zama ina jiranka?" Ya sake yin k'asa da kansa yace "i'm sorry Abba" d'auke kai Abba yayi yace "je ka kawo min kada ka b'atan lokaci" d'agowa yayi kad'an ya kalli Abba then ya tashi ya haura sama,ya bud'e bedroom d'insa ya shiga,a inda ya ajiye nan ya gansu ya d'auko yana fitowa Mama ta fito daga bedroom d'inta ta bisa da kallo tace "yaushe ka dawo?" Bai tsaya ba yace "yanzu na shigo" ta gyad'a kai ta biyosa tana tambayarsa office yace "alhamdulillah" ta k'arasa kusa da Abba tana fad'in "sannu da hutawa Alh" yace "yawwa!" Ba tare da ya kalleta ba,Waleed ya k'arasa ya zauna k'asa kan rug yace "ga shi Abba" kallonsa Abba yayi yace "kaje ka mayar mata abunta,daga yau kuma idan ka san ba kai ka sai mata ba kada ka sake ganinta da abunta ka gwada mata fin k'arfi.. Ka ji me nace?" Ya gyad'a kai yace "in sha Allah" Abba ya d'auke kai ya ci gaba da kallon news d'insa,Mama dai sai kallonsu take bata fahimci komai ba har Waleed ya tashi ya nufi k'ofa zai fita ta bisa da kallo tana kallon hannunsa mamaki duk ya hanata cewa komai. A ciki² yayi sallama ya shiga,Dadda dake zaune ta d'aga kai ta bisa da kallo,ya zauna kan kujera fuskarsa a d'aure yace "ina yini?" D'auke kai tayi itama kamar an mata dole ta amsa tace "lafiya" ya dunga juya wayan da d'ayan dake cikin kwali kafin da kyar ya daure yace "ina yarinyar nan take?" Dadda tayi kamar bata jisa ba,ya kalleta ya tabbatar ta jisa,haushi yasa shi mik'ewa ya nufi hanyar d'akin,a kan gado ya ganta ta juyawa k'ofa baya,ya taka cikin d'akin bai yi magana ba sai da yaje kusa da ita ya kai hannu ya yaye bargon data rufa,still tak'i motsawa ya kai hannunsa ya d'agota ta bud'e idanunta da sauri tana zumb'ura baki tace "Yaya meye haka bacci fa nake ka tashe ni" ya kalleta yace "yaushe kika fara baccin?" Tace "yanzu" sake kallonta yayi sosai fuskarta babu alamar ta fara bacci yace "da kika ji shigowata ko?" Ta b'ata rai ta k'i kallonsa,ya mik'a mata wayoyinta yace "take" d'aga kai tayi ta kallesa,yace "karb'i nace ki bar kallona" ta karb'a tana b'ata rai,har ya juya zai fita ya waigo yaga shi take kallo,ya d'aure fuskarsa yace "kiyi duk yadda kike so kin ji?" Tana kallonsa ya sa kai ya fice gaba d'aya daga apartment d'in" sanda ya koma gida,yana shiga yayi hanyar sama Mama ta tashi za ta bisa Abba ya d'aga kai ya kallesu gane nufinya yasa Abba ya kirasa ya amsa ya dawo,Mama ma ta tsaya gurin taba jin kamar ta dawo,ganin kallon da Abba yake mata yasa tayi sama cikin jin haushi,ya zauna kusa da k'afar Abba yace "here i'm Abba" Abba ya ajiye remote d'in hannunsa yace "wane magana muka yi da kai kwanaki?" Waleed yayi squeezing fuskarsa yana tunani,Abba yace "ka manta?" Ya girgiza kai yana sauke ajiyar zuciya yace "a'a Abba" Abba ya gyad'a kai yace "to ya ake ciki?" Waleed yace "Abba ai kai kace za kamin magana idan ka yi tunani,and i thought ko da naji baka ce komai ba an fasa ne" Abba yace "ba'a fasa ba" Waleed yace "to Abba yanzun ya za'ayi?" Abba yace "na yi magana da Aunty'n ku,ta ce min suna hanya k'arshen shekara,and she said shawararka mai kyau ce" yayi murmushin gefen baki duk da ba ya cikin mode d'in yin hakan,Abba yace "ina ga gobe idan Allah ya kaimu ka d'auketa kuje makarantar su Ameerah,duk abunda ya dace kayi" ya amsa da "toh Abba" sun d'anyi maganganu sosai kafin Abba ya sallameshi ya tashi ya haura sama zuciyarsa fari tas,yana bud'e bedroom d'insa ya shiga Mama ta fito ta biyo bayansa,ya juya da sauri jin an shigo idanunsa suka sauka kan Mama dake masa wani kallo,ya juya ya zauna ta k'araso tace "Waleed wayar waye na gani a hannunka?" Kai tsaye tace "na Manar ne" wani kallo ta dunga masa tace "Manar?" Ya d'auke kai bai ce komai ba,tace "me ya had'a ka da kayanta? Ban hanaka shiga shirginta ba?" Ya d'ago da sauri zai yi magana..
Chapter 34 · 0% Book details