← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 150 OF 184

Sashe 150

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

#Asli Smasher.
51...

*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*

*Subscribe and read happily without feeling any guilt.. It's ₦200 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman,Access Bank or MTN recharge card/VTU and then show ur evidence of payment through my whatsapp account 08165726609 to be added in the paid group.*

'Dan janye jikinta tayi tana kallonsa da kyau da wani cool voice tace "please me ya faru? Fuskarka ya sanar min ba lafiya ba,what happened to u?" A hankali ya bud'a idanunsa da suka k'ank'ance yana kallonta,voice d'insa a d'an dashe yace "ke kika fad'a ma mother ban tab'a zuwa gurin Mama ba?" Kallonsa ta dunga yi kafin ta daure tace "me yasa zan fad'a mata?" Yace "idan baki fad'a mata ba,ya akayi ta sani? And cikin kwanakin nan kin min shigen maganar,right?" Gyad'a masa kai tayi tace "yeah! Na maka shigensa,har kayi fushi da ni ranan.. But ko a lokacin ba idea d'ina bane,Mother ta sani tace na maka maganar saboda tana ganin za ka saurare ni idan na fad'a.." A nutse ta warware masa yanda suka yi da mother ranar,sanda ta kai k'arshe tayi shiru tana jiran yayi magana,taga ya sauke numfashi a hankali ya kulle idanuwansa,then ya fara bata labarin yanda suka yi da Mother shima har ya gama,tana kallonsa da kyau dan kada ma ta tambayesa wani abu game da hukuncin da ya yanke kan maganar ransa ya b'aci tace "Allah kyauta" daga haka ta mayar da kanta ta kwantar a k'irjinsa,tana d'an caressing jikinsa,yayi shiru shima bai k'ara cewa komai ba a haka suna y'an lalube² har wasan ya canja salon tafiya. Ranar alhamis sanda ya fito da rana daga hospital da yake sunyi magana da Abba da jimawa akan Mama sanda yake kan hanya ya kira Manar a waya,ta d'auka cikin zumud'i tace "hello! Master kana hanya ne?" Ya d'anyi shiru kafin yace "um'um! Zanje wani unguwa yanzun,and ba na tunanin zan dawo gida yanzu sai na tashi daga aiki" d'an dum tayi sai kuma a sanyaye tace "alright! Allah tsare hanya" yanda yaji ta yi magana yasa shi d'an lumshe idauwa ya bud'e a hankali yace "i'm sorry Lilac zanje duba Mama ne" d'an murmushi tayi a shagwab'e tace "ko za ka zo ka d'aukeni muje tare?" Murmushin shima yayi yace "i'm sorry but ki bari ba yanzu ba" tace "mesa ba yanzu ba?" Yace "ni dai bance ki tambayeni ba kawai ki bari next time idan zan sake zuwa" ta gyad'a kai da wani muryan kamar ta yi fushi tace "shi kenan" yace "shi kenan me?" A shagwab'e tace "tou ba dai baza ka da ni ba kuma?" Yace "ai na ce ki bari ba yanzu ba" kukan shagwab'a tasa masa tana bubbuga k'afa a k'asa,yana jinta ya zaro k'ananun idanuwansa yace "ki rufa min asiri ki bar abun nan kar kimin asara" wani dariya ta kyalkyale da shi tace "bangane ba?" Yace "kin fi kowa sanin ba ke kad'ai bace yanzun,right?" Tace "tou ba kaine kak'i tafiya da ni ba" yace "please kiyi hak'uri na fara zuwa yanzun later sai muje ko?" Tana d'an kuka k'asa² na tab'ara tace "ni dai ban yarda ba sai dai idan za ka hak'ura da zuwa yanzun kaima" yana ji ta ce haka yace ''shi kenan bari na fasa zuwa nima duk sanda zanje dake sai mu tafi tare.. I'm coming home" da sauri tace "a'a ni bance ka fasa ba ai" yace "kin hak'ura naje ni kad'ai?" Ta gyad'a kai tace "ehhh!" Yace "thanks" yana d'an murmushi,tace "bari na kyaleka kayi driving,sai ka dawo?" Yace "in sha Allah" tace "ka gaisheta tou" suka yi sallama,dai² nan ya tsaya wani super market yayi mata siyayyar kayan amfani sosai kafin ya tada motar ya d'auki hanyar da za ta kaisa gidan. Sanda ya k'arasa unguwar da Abba ya sanar masa ya bata gida ta zauna halak malak,yayi parking dai² k'aramin get d'in gidan,unguwar shiru da yake sabon guri ne,ya d'an jima a mota yana studying arean kafin ya fito ya rufe ya k'arasa bakin get yayi knocking,daga ciki ya jiyo muryar Mama tana tambayar "waye?" D'an shiru yayi,a hankali sanda yake jin footsteps d'inta kusa da k'ofar yace "Waleed ne" ita kanta Mama jin muryarsa sai da ya ba ta mugun mamaki,ta bud'e k'aramar k'ofar jikinta a mugun sanyaye kanta a k'asa kamar surukinta tace "sannu da zuwa" ya amsa yana kallon yanda ta zumbulo hijab har k'asa tace "shigo" tana basa hanya,yace "thanks" then ya shiga,ta mayar da k'ofar ta rufe tana juyowa ta gansa a tsaye yana kallonta,ta d'anyi k'asa da kanta tace "mu shiga ciki" ta fara wucewa yabi bayanta zuciyarsa a mugun raunane saboda yanda yaga Maman ta koma wata quite kamar wanda akayi sabon version na ta,suka shiga parlor ta nuna masa gurin zama,a k'asa kan carpet ya zauna yayi flexing legs d'insa ya gaisheta,ta amsa bata yarda sun had'a idanu ba ta koma kan darduma ta zauna,tace "ya mutanen gidan da aiki?" Yace "alhamdulillah,duk lafiyarsu lau" tace "ya iyali fa?" Shi dai kallonta kawai yake kamar zai mata hawaye tsabar ramar da yaga ta yi da duhu,yace "lafiya lau tana gaisheki" tace "ina amsawa,ya k'annenka da kakarku?" Ya d'an sauke numfashi kafin yace "basu san ma zan zo ba" tace "Allah sarki" daga haka suka yi shiru,can ta tashi tace "ina zuwa" yace "toh a fito lafiya" ta wuce hanyar kitchen,ya bita da kallo cike da tausayi,tsakanin d'a da mahaifi sai Allah,duk abunda ta masa da yake mugun jin haushinta lokaci d'aya tausayin halin da ya ganta ya shafe komai,yana zaune ta kawo masa jellop d'in taliya da taji kifi da kayan lambu,da sanyayyan sob'o ta ajiye masa tace "bismillah ga abinci" d'an murmushi yayi mata yace "na gode" ta koma ta zauna tayi shiru,shima shirun yayi yana d'an kallonta,sun kusa 30 minutes a haka shi bai ce mata ba itama haka,can ta d'an d'ago taga bai ci abincin ba tace "kaci abincin mana kar yayi sanyi" yayi murmushi bai ce komai ba ya d'auki fork d'in data saka masa ya fara ci,bai wani ci da yawa ba ya ajiye cokalin ya tsiyaya lemon ya sha,ta kalleshi ganin ya ajiye cokalin yana danna wayarsa tace "ba dai ka k'oshi ba?" Yace "alhamdulillah na ci ai da yawa" tayi d'an murmushi tace "ko dai bai maka dad'i ba na dafa maka wani abun?" Ya girgiza kansa yace "a'a haka ma na gode,sauri nake zan koma gurin aiki" tace "tou Allah tsare hanya,na gode sosai da ziyara,a gaida mutanen gidan da iyali" yace "in sha Allah" ya tashi zai fita sanda yaje kusa da k'afarta ya sunkuya ya ajiye mata 50k yace "kiyi hak'uri zan dawo in sha Allah,ko rik'e wannan a hannunki" hawaye suna sauka fuskarta tace "na gode sosai Allah saka da alkhairi yayi albarka" ya amsa ya fita ta tashi ta biyo bayansa da niyyar ta rufe k'ofa,yana jin takun tafiyarta a bayansa ya kasa juyawa saboda ya ga kuka take tun kafin ya fito,da zai fita yace "bari na d'auko sak'o a mota" tace "tou" ta d'an tsaya daga ciki ya fita ya bud'e booth ya fito da manyan ledoji da cartoons d'in spaghetti,macaroni,couscous hatta su maggi sai da ya siya mata da ruwa da drinks,yasa almajiran da yaga za su wuce ta line suka shigar mata da kayan,sanda suka gama kwasar kayan ya rufe booth d'in ya zagaya ya bud'e motarsa ya shiga,Mama ta k'araso inda yake tana kallonsa tace "na gode sosai Waleed,dan Allah idan ka je gida ka k'ara yima mahaifinku godiya sosai" yayi mata murmushi yace "in sha Allah" tana tsaye sai da taga ya bar line kafin ta shiga gidan ta kulle k'ofarta,ranar Mama kwana tayi tana kuka,sosai ziyaran da Waleed ya kai mata ya tuna mata abubuwa da yawa daga rayuwarta,bata tab'a zaton zai zo ba saboda abubuwan da tayi masa a matsayinta na mahaifiyarsa. A nasa gefen shima tun da ya bar unguwar jikinsa ya k'ara yin sanyi da al'amarin,tun a lokacin kuma ya d'auki alwashin zai dunga zuwa yana dubata lokaci² ko dai bai samu ya je kullum ba zai yi k'ok'arin ganin ya je duk ranar Friday,a haka ya koma hospital,sai da lokacin barinsa asibitin yayi ya kama hanyar gida,a hanya sanda ya tsaya ya siya mata apples da yawa because ya san abunda take mugun so kenan kafin ya k'arasa. Sanda yayi parking ya fito ya d'auki ledar daya ajiye d'ayan seat d'in ya fito ya wuce ciki,ya bud'e k'ofa ya shiga da sallama,sanyayyan k'amshin dake tashi gami da sanyin AC daya kai ma hancinsa da gangar jikinsa ziyara yasa shi lumshe idanuwansa a hankali yana sauke ajiyar zuciya,then ya fara bud'esu a hankali,a kanta idanunsa suka sauka tana tsaye a kan staircase ta d'an karkace ta side d'aya ta rik'e waist tana masa wani kallo mai tsuma zuciya,tun d'aga k'asa ya fara kallonta sanda ya kai kan k'ugunta da yake nan fam kamar zai fashe ta cikin creazy jeans d'inta,yabi fresh skin d'inta da yake hangowa ta wajen thighs da kallo yan fesar da wani iska,ya k'ara yin sama da inanunsa sanda ya kai k'irjinta bai san sanda ya fara tafiya ba ya nufeta,gaba d'aya ta gama tafiya da shi,ji yake idan bai rab'a jikinta a nasa ba sam ma ba zai samu nutsuwa ba,tsayawa tayi a matakala ta uku har ya k'araso,kafin ya hauro tayi saurin tahowa kamar za ta fad'o,da sauri ya saki ledojin hannunsa ya tarota,yana kallonta a tsorace yace "why Lilac kike son min wasa da abu mafi tsada da muhimmanci a rayuwana? Idan da kin fad'o fa kin ji ciwo sai kice min tsautsayi ne ko?" Dariya ta kyalkyale da shi tace "ai na san kana nan shisa,and baza ka tab'a bari wani abu ya same mu ba" ya zuba mata idanu yana sauke ajiyar zuciya can ya juya ya kalli yanda tasa ya b'arar da komai,then ya kalleta yace "kinga kinsa na zubar ko?" Ta kalli gurin tana dariya tace "sai ka kwashe ni ai bance ka zubar ba" yace "ohh! Ba ke kika sa na zubar ba ma?" Ta gyad'a masa kai a shagwab'e tace "ni ba ni bace" ya gyad'a kai a hankali ya saketa ya tsuguna ya fara tsincewa,tayi dariya ganin yana kwashewa baice komai ba ta tsuguna tana tayasa. Da dare lokacin suna kwance taji har sannan baice mata komai game da zuwansa gurin Mama ba,ta daure tace "Master! Ya ka baro Mama?" A hankali yace "tana lafiya,ta ce a gaisheki" ta dunga kallonsa ta kasa yarda wai Mama ta ce a gaisheta,ya kalleta jin ta yi shiru,da sauri kuma sai ta waske tana d'an murmushi tace "ina amsawa ka sameta lafiya?" Yace "alhamdulillah!" Tace "maa sha Allah" daga haka sai bai sake ce mata komai game da abunda ya shafi Maman ba,har suka gama budurinsu suka yi bacci,itama kuma bata damu kanta ba bare ta masa tambaya kan al'amuran Maman. Washe gari Friday around 7am Deejah ta kirasa hankalinta tana kuka tace "Yaya dan Allah kazo gida yanzu" yace "lafiya?" Dan shi bacci ma yake kiranta ne ya tashesa,tace "please kazo dai dan Allah yanzu" ya amsa mata,yana d'an tab'e baki ya juya ya kalli side d'in Manar,ya yi zaton tana kwance sanda yaga wayam,da sauri ya sauka daga gadon ya fad'a bathroom yayi wanka ya fito ya shirya a gurguje cikin manyan kaya kasancewar jumu'ah ya fito daga d'akin ya nufi downstairs,a kitchen ya sameta tana had'a musu breakfast ta d'aure hancinta da handkerchief,ya k'arasa shiga yana kallonta yana cewa "aikin kamar ya zama wajibi kiyi?" Ta waigo da sauri tana sanye da riga oversized da short nickers,ta d'anyi maea murmushi tace "dole ne mana" ya girgiza kansa yace "a'a bai zama dole ba tunda ina nan" ta sake masa murmushi tana kallonsa tace "waye ya tasheka na san sanda na fito bacci kake?" Yace "Deejah ta kirani wai naje yanzu,so ban san me yake faruwa ba bari naje naji" gyad'a masa kai tayi tace "za ka dawo ne idan ka fita?" Ya d'an girgiza mata kai yace "i don't think so" kallonsa ta dunga yi kafin tace "tou kayi breakfast kafin ka wuce" yanda yaga tana kallonsa yasa shi cewa "noo! Na kusa makara,idan kin gama ki bayar kawai zan wuce ina sauri" wani kallo ta dunga masa baki bud'e ta kasa cewa komai,kawai hawaye suka fara biyo idanunta,da sauri ya k'arasa kusa da ita ya rik'ota yana tambayarta "me ya faru?" Fizge hannunta tayi ta bud'e hancinta cike da masifa tace "na hana idanuna bacci na maka breakfast d'in shi ne za kace na bayar?" Yana k'ok'arin sake rik'eta tace "ni karka tab'a ni,tunda baza ka ci ba jeka kawai Allah tsare hany.." Bata k'arasa fad'a ba warin gas da ba ta so yasa ta fara yunk'urin amai,ya matso da sauri zai rik'eta ta turasa da k'arfi ta nufi hanyar fita da gudu tana toshe bakinta..
Chapter 150 · 0% Book details