← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 184

Sashe 25

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

#Share pls.
#Asli Smasher.
💠💠💠💠💠
©®2021.

*♡MANAR¸.•💥*

*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://t.me/joinchat/VHlmxxheyxG6m9VoUJZbZA

_Devoted to My Mamma Hjy Maryam Alhassan (Jikar Kulu)._

_Bestowed to Fateema Abdulmajid._

08.

#Their origin..

Hjy Asama'u zaune gaban bokansu ita da Hjy Izzatu cikin tsananin tashin hankali bayan ya gama musu bayanin matsalar dake tunkarosu,Hjy Asama'u tace "gaskiya Boka a san yadda za'ayi a juya lamarin nan,idan da hali ina son a cire tunanin yarinyar gaba d'aya daga zuciyarsa a cusa masa tsanarta" Wani k'ak'k'arfan dariya Bokan ya saki sanda yayi iya yinsa da wani irin murya mai ban tsoro yace "wannan ba mai yuwuwa bane,tun farko na fad'a miki,d'anki bazai tab'a jin tsanar yarinyar ba kome za kiyi,soyayyar da yake mata ba abune mai sauk'i da za mu iya rabasa da ita ba" cikin tsananin tashin hankali Hjy Asama'u tace "ni dai Boka kayi wani abu akai,wallahi ko mutuwata ban tsana kamar yadda na tsani yarinyar ba,ni dai idan da taimakon da za ka iya yi kayi ka raba su" directly yace "ki canja wani k'udurin" Hjy Asama'u kamar za ta d'ora hannu aka ta runtuma ihu tace "yanzun boka me kake ganin za ayi?" Wasu irin surutan tsafi ya fara kafin ya kafeta da idanunsa da suka juya,lokaci d'aya yayi shiru idanunsa suka yi wani irin jaa mai ban tsoro gumi duk ya wanke masa jiki,bakinsa yana fitar da bak'in hayak'i yace "akwai hanya d'aya.. Sai dai itama babu tabbas" bakin Hjy Asama'u har b'ari yake ita da Hjy Izzatu wajen tambayarsa "wane hanya ne?" Yace "hanyar shi ne idan har kina son su rabu sai dai idan aure za kisa d'anki yayi,muddin ya bar gidan shi kenan" wani gagarumin ajiyar zuciya tayi tace "idan aka yi haka shi kenan an cire masa ita daga zuciyarsa?" Boka ya kece da dariya yace "ba shi kenan ba" hankalin Mama ida ya kai d'ari ya kai k'ololuwa gurin tashi cike da sarewa tace "sai me kuma?" Yace "Mu nan da bak'ak'en shaid'anu muke aiki,abune mai matuk'ar wahalar gaske mu iya cutar da ita ta ko wane irin fuska,rabasu abune da ya gagari iyawarmu.. Akwai wani sirri tattare da yarinyar,wanda duk k'ok'arin da muke da bincikenmu wajen gano kan al'amarinta abubuwa sun faskara,sun kasa fitowa yadda za mu gane,ko yaushe muka yi bincike haske kad'ai muke gani,sannan wani abu guda yarinyar nan baza ta tab'a fita zuciyar yaron ba,yau ko gobe,yanzu ko anjima tabbas d'anki zai zo da buk'atar yana son aurenta,abune da yake zane cikin zuciyarsa,soyayyar da yakema yarinyar da wuya ya goge daga zuciyarsa,wannan wani k'uduri ne da komai sauyawar zamani wata rana wannan burin zai cika.. Kada ki manta da wannan maganar.." Mummunan fad'uwa gaban Mama ya dunga yi bakinta da jikinta suna b'ari,hawaye suna sauka fuskarta a hargitse cikin gushewar hankali take fad'in "kada ka bari haka ya faru boka,wallahi da kai kad'ai na dogara,ba ni da mafita sai ta ka,ka taimake ni kada su yi nasaran rabani da d'ana.." Zane² yayi cikin iska kafin ya kalli Mama yace "me kike so ayi miki?" Tace "ba na son maganar aurensu nan" yace "idan har ba kya son yazo miki da maganar kiyi gaggawar nema masa mata" cikin sauri ta gyad'a kai tana share hawayen da suka b'ata mata fuska tace "zzzz... Zanyi wallahi,zan nema masa da gaggawa ma" Boka yace "sannan akwai wani abu guda" da sauri Mama tace "mm.. Mene ne shi?" Yace "kun san wanda za ta aura gaba idan an raba ta da d'anki?" Hjy Asama'u tayi sauri tace "duk ma wanda za ta aura Allah gafarta boka taje ta aura mana tunda dai ta rabu da d'ana ai shi kenan,ni d'ana kad'ai ne ba na son ta rab'a,koma waye taita auransa me zai dameni?" Hjy Izzatu ta kara da cewa "koma meye zai faru mu bai dame mu ba,ta auri koma waye" a nan suka bashi kud'ad'e masu ciwo tare da alkawarin idan wata matsala ta taso zai gansu,sanda suka taho a hanya suke sake tattauna maganar cike da sanyin jiki Mama tace "idan har hak'anmu zai cimma ruwa babu matsala,ni zan k'arasa sauran aikin.. Matuk'ar dai ace ina numfashi bazan tab'a bari ahalin Maryam su kusance ni da y'ay'ana ba" Hjy Izzatu ta gyad'a kai tace "ai baima kamata mu bari wannan alamari ya faru ba" har suka k'araso gida maganar da suke yi kenan.

*Flashback...*
Chapter 25 · 0% Book details