Sashe 155
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A nan suka samu Dadda,Mommella,Mother da Aunty suna maida zancen haihuwar,Mommella cikin jimami tace "ni dai na rasa gane yanda akayi wannan al'amarin ya faru,ace kaf gidan nan babu wanda yayi noticing faruwar haka sai yanzu?" Aunty ta had'iye wani yawu fuskarta cike da damuwa tace "ki bari sister,ni kaina al'amrin nan ya mugun d'aure min kai,amma wallahi ban san komai ba akai,tunda yarinyar nan idan nace miki na fi 4 month ban sa ta a idanuna ba kada ki musa,sam ta daina fitowa cikin mutane,ko abinci sai dai a ajiye mata bakin kofar d'akinta idan ta ji yunwa ta fito ta d'auka,jiya da dare kawai sai ciwo Deejah ta zo take sanar min,kafin kice me sai kukan yaro ni dai naji,tsabar mamaki har yanzun na kasa yarda da abunda ya faru.." Shigowar su Daddy dai² lokacin yasa su yin shiru suka amsa sallamar da suka yi,suka zauna bayan sun gaisa da Dadda da su Mommella,Daddy yasa Aunty ta je ta zo da Diyanah da sauran yaran,su Manar dama su suna cikin gidan,Dadda taje k'ofar bedroom d'insu na part d'inta tayi knocking tace "tou kuzo ko ubanku Muhammadu yana kiranku.. Ai tunda aka janyo mana bala'i kuma kun shiga cikin fad'ansa,duk da dai na san ku baza ku aikata haka ba" Manar ta kalli k'ofar daga cikin d'akin tace "ga mu nan fitowa" suka taso su uku ita da Ameerah da Rania suna sanye da manyan hijabs suka fito,a k'asa suka zauna suka gaida iyayen nasu maza,hankalin Manar kaf yana kan Waleed da ya lumshe idanuwa,Abba dai ya kasa magana gaba d'aya ya koma wani dumb,ko magana akayi sai dai ya biku da idanu,su Amaar ma suka shigo tare da Azaan,suka zauna kusa da Waleed da ya zama wani very quiet,sanda Aunty suka shigo tare da su Diyanah, Deejah ta samu guri kusa da su Manar ta zauna,Diyanah dai ta rakub'e gefe tana sharar kwalla,Daddy yayi gyaran murya yayi sallama,suka amsa masa,bayan nan yana kallon occupants d'in parlon yace "dalilin da yasa muka buk'aci ganinku,ba wani abu bane sai domin mu shaida muku,yanzun haka daga masjeed muke,an riga an d'aura auren Halima da yaron wajen Alh Idris Baffanyo,saboda rufuwar asirinmu duka,Alh Baffanyo ya buk'aci ayi d'aurin auren cikin sirri,tou kuma muma sai muka ga dacewar hakan tunda har ya zo da sulhu,ba sai mun tsaya ana jan maganar ba" here yayi musu bayanin duk yanda suka yi da Alh Baffanyo sanda suka je masa da maganar jaririn,Dadda su Mommella duka dai sai gyad'a kai suke cike da gamsuwa,sanda Daddy yayi shiru yace "Allah sa hakan shi ne mafi alkhairi garesu" duka occupants d'in parlon suka amsa da ameen,ya d'an gyara zama ya fito da sadakinta ya mik'awa Dadda yace "ga sadakinta nan da iyayen yaron suka bayar" ya ajiye bundle 5 na 1k a gabanta,bud'a ido Dadda tayi kamar wanda ke jin tsoro tana kallon kud'in tace "iiiihhh! Yo ni ka turo min kud'in kuma? Ba kune iyayenta ba? Fisabilillahi ni me zanyi da dukiyarta da ka bani? Da dai na takwarata ne sai in amshe in sai mata kadara,amma wannan bazan karb'a ba maza mik'a mata abunta Allah sanya albarka.. A toh! Maganar gaskiya fa kenan.." Gyad'a kai Daddy yayi ya mayar da kallonsa kan su Aunty a hankali yace "kafin suyi maganar lokacin d'aukan amarya,tunda ku ne iyayenta sai ku fara shirye²,duk abunda ake buk'ata kuma sai a sanar min" tun bai k'arasa ba Abba ya d'ago yana jifansa da wani kallo,kafin ya girgiza kansa ya kalli direction d'in da Diyanah take cikin kausasa murya yace "ka kirasu yanzu suzo su tafi da ita,babu amfanin da zamanta zai min a gida" Daddy zai yi magana Abba ya d'aga masa hannu cikin fad'an da basu tab'a gani ba yace "wallahil aziim baza ta k'ara min ko da cikakken awa guda a gina ba,idan kuma ka zab'i ta zauna ni zan bar gidan yanzu" baki sake Dadda take kallon Abba jin abunda yace,da sauri tace "iiiihhh! Me yayi zafi haka kuma Yaro? Ai ba sai ka rantse ba,ko ni nan ma ban yarda ta k'ara zama mana a gida ba,tunda an d'aura auren yazo su tafi haka,Allah ba mu alkhairi,mu kuma Allah saka mana da alkhairi" Daddy dai kallon Yayan nasa ya dunga yi ya kasa magana,ganin irin kallon da Daddy yake masa,nan take Abba ya fusata ya mik'e tsaye yace "Allah bamu alkhairi" da sauri Dadda ma ta mik'e tace "a'a Yaro ai ba na bari ka tafi kai kad'ai ba,yo na san inda za kaje idan ka tafi? Tsayani ka ji,duk inda za kaje mu tafi tare.. Yo zan barka ne haka kai kad'ai,wani abu ya sameka ina nan sake da baki in shiga uku" da sauri Aunty da mother suka bisu ganin har sun fita suna basu hak'uri,Dadda ta fashe da wani kuka mai cin rai tace "Allah ma ya sani kaf zuri'ata da ta ubansu babu wanda ya tab'a d'auko abun kunya sai yarinyar,saboda haka idan baza ta tafi ba mu sai mu bar maku gidan kawai" Mother ta sauke numfashi tace "kiyi hak'uri Hjy bari nayi magana da Daddy ya kira gidan mazan.. Ai duk ba'a kai nan ba" Dadda ta tsaya tana share kwalla bata dai ce komai ba,dai² nan Manar ta k'araso tana kallon Dadda tace "Hjy ba'a haka fa,kina ganin Abba zai ji dad'i ne da kika goyi bayan Diyanah ta bar gidan nan? Ko me ya faru ai itama jininki ce,hannunka ba ya rub'ewa ka yanke ka jefar" da sauri Dadda tace "ke y'ar nan wallahi sai dai in bai dameka da warin bala'i ba,amma tuni za ka gutsire d'an banza ka cillar" Manar ta dunga kallonta tace "tou ai shi kena.. Daddy yace na fad'a muku ya kira Alh Baffanyo suna hanyar zuwa yanzu" take Dadda ta washe baki tace "tou² yanzu aka yi magana mai ma'ana,Allah kawo su lafiya,bari naje na sanar ma Yaro ya kwantar da hankalinsa ba sai munje ko ina ba" Aunty dai da Mother kallon juna kawai suka yi,sanda Dadda ta nufi part d'in Abba,then suka koma part d'inta. Sanda su Alh Baffanyo suka k'araso da driver d'insa,har cikin gidan Daddy yasa aka shigo da su b'angaren Dadda saboda Alh Baffanyo ya sanar ma Daddy yana son zuwa ya bawa mutanen gidan hak'urin abunda yaronsa yayi,after an gaisa da shi ya nemi afuwa gurin Dadda da su Aunty kafin Daddy ya musu rakiya har bakin mota,Diyanah kam tare da Aunty suka wuce gurin Abba,tana kuka take neman afuwa,Abba dai ko kallon inda take baiba,Aunty ta zauna kusa da Abba,cikin tausasa murya tace "dan Allah Abbansu kayi hak'uri ka yafe mata,k'addara ne kuma babu yanda za'ayi,dole sai haka ya faru.." Da sauri Abba ya d'aga mata hannu,ya kalli Diyanah da rinannun idanuwansa yace "Allah tsare.." Daga haka bai k'ara cewa komai ba ya mik'e ya wuce sama,kuka sosai Diyanah ta fashe da shi tana durk'ushe gurin ta kasa tashi,sai da Aunty tazo ta kamota ta mik'ar da ita tsaye suka fito,suka k'arasa gurin mota ta shigar da ita back seat ta rufe mata k'ofar tana mata addu'ar Allah tsare tare da fad'a mata sai sun zo ganin gidan da take,ta gyad'a kai tana share hawaye,driver yaja suka bar gidan. A balcony lokacin da Waleed ya fito daga b'angaren Dadda suka had'u da Manar da ta fito b'angarensu,tun daga nesa take masa kallon tuhuma,sanda suka zo kusa da juna taga zai wuceta babu ko magana,da sauri ta kamo hannunsa ta rik'e,idanunta suna tara hawaye ta dunga kallonsa a sanyaye tace "Master! Lafiya kuwa?" 'Dan lumshe idanuwansa yayi yana sauke numfashi ya kasa mata magana,tayi saurin matsowa gabansa ta rungumesa sosai tana kallon fuskarsa da yayi pale kaman wanda ya shekara yana ciwo tana masa wani kallon k'urilla tace "mmm! Anya ma yau ka ci abinci kuwa?" Tayi maganar tana shafa cikinsa dake nan flat,sake lumshe idanuwansa yayi yana tunanin maganar da ta fad'a,da sauri ta kai hannunta fuskarsa ta d'anyi tapping cheeks d'insa tana kallonsa da idanunta da suke shirin fara zubar da kwalla tace "tell me please when last rabonka da abinci?" Girgiza mata kai kawai yayi ya fara k'ok'arin raba jikinsu,da sauri ta k'ara kwak'umesa tana goga jikinta a nasa,ta marairaice tace "ai to baka fad'a min ba kuma?" Kamar zai fashe mata da kuka,dan yau duka ba ya ma son ayi masa magana ya d'an langab'ar da kansa da wani sanyayyan voice yace "ban ci ba tun safe" zaro idanuwa tayi da d'an k'arfi tace "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.." Hawaye suna sauka fuskarta take kallonsa tace "mesa za ka min haka Master? Ka zauna da yunwa idan ni nayi kuma kace za ka b'ata ranka?" Kulle idanuwansa yayi da k'arfi a hankali kamar ba ya son fad'a taji yace "na yi losing appetite,bazan iya ci ba,sam ma ba na jin sha'awar cin komai" cike da tausayinsa ta kai hannunta ta share fuskarta ta zuba masa idanuwanta tana kwantar da kanta saman k'irjinsa tace "idan na kawo maka za kaci ai ko?" Kai ya girgiza mata alamun a'a,ta narke fuskarta kamar za tayi kuka tace "za kaci mana,ai to da kaina ma zan baka" d'an zuba mata idanuwansa yayi da suke a birkice ba tare da ya ce komai ba,ta rik'esa da sauri tace "muje to yanzu sai na kawo maka ko?" Ba tare da ya ce mata komai ba ya fara binta ganin ta rik'e masa hannu alamun su tafin,sanda suka isa part d'insu ta tsayar da shi tace "ka jirani bari na fito" shi dai kamar rak'umi da akala haka ya tsaya a gurin har ta shiga b'angaren nasu,ta wuce kitchen ta had'o masa lafiyayyen sinasir da miyan egusi da yaji nama ta had'o masa da banana and coconut milkshake da yayi mugun sanyi cikin wani midi basket,tana fitowa ta gansa tsaye ya jingina da pillar a balcony d'in sun,ta k'arasa gurinsa da sauri ta rik'o hannunsa tace "let's go Master" binta yayi suka wuce part d'insu,basu tarar da kowa ba da suka shiga suka wuce sama,asalin bedroom d'insa suka shiga tare,Manar tayi sallama k'asa²,suka k'arasa ta fara sakinsa ta wuce ta ajiye basket d'in hannunta,da kallo ya bita sanda ta wuce ta barshi tsaye kafin ya sauke wani nauyayyen ajiyar zuciya then ya wuce bathroom,k'aran rufe k'ofa yasa ta juyawa da sauri,sai