Sashe 99
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
To amma.muhammad jadda fa?,ta sani farin sani cewa wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa. Alfarmarsa ta wuce duk yadda ake tunani,duk arziqi da alfarmar ubanta da take taqama dasu bai wuce yaron jadda ba. Ta sake tsinkewa da lamarinsa sanda daddynta da kansa yake bata labarin yadda fu'ad din ya soke masa wata kwangilar millions of naira,wanda gwamnatin tarayya taso bashi amma jaddan ya fahimci cin hanci da rashin kyan aikin yayi yawa. Ya fusata a sannan baisan waye jaddan ba,ya kuma bazama da zummar a nemo masa wayeshi a hada musu zama....saidai randa ya soma yi masa ganin farko ya kuma zauna dashi da qyar ya qwaci kujerarsa ta ambassador. Har qasa yakai yana hurwa da neman ya rufa masa asiri,ya barshi ne bisa sharadin komai zai dinga tafiya bisa adalci da amana,ya kuma tsaya da iya muqami da dukiyar da Allah ya bashi. Tun daga ranar suka yiwa juna farin sani,labarin da daddyn nata kuma ya bata ya sanya mata tsananin son mallakar fu'ad din. Tanason namiji me qarfin izza da mulki gami da iko takowacce fuska,a duk inda ya tsaya yayi magana za'a dakata a saurareshi,a duk inda yayi umarni dole za'a bi.....to amma sai gashi dare daya komi ya watse komi ya wargaje mata daga hannunta. "Zan iya barinsa kuwa?" Ta tambayi kanta sanda wata zuciyar ta fara mata saqa da mugun zare.....zuciyar ta fara ayyana mata daukan BAQAR FANSA da kowanne irin hukunci daya kamata ta zartar kawai a kansa. _uhmmmm,nidai nace wanda baiji bari ba yaji hoho_ Ido farouq ya zuba masa sanda yake dawowa wajen. Sai a sannna hankalinsa ya kawo abinda fu'ad din yayi masa. Cikin dakewa da kuma basarwa yace yana zama. "Sarkin noma.....na dawo" Sarai yasan magana ya gaya masa,amma ganin ma ya zaro wayarsa ya soma lalubar wata number sai kawai ya qyaleshi da duk abinda zaice dashi,illa dai yace masa. "Ina fatan baka rabata da numfashinta ba" "Ta samu wannan tsiran saboda batayi musu ko gardama ba" Yana kaiwa nan ya saka wayar a kunnensa yana magana da daya bangren. Ya kusa mintuna talatin yana amsa wayar kafin daga qarshe ya rufe da "Aikinka na kyau CP.....good job,akwai zuwaira......akwai harira ko something hajja......yes......yes" Daga haka sukayi sallama. Zazzafar numfashi ya sauke yana aje wayara a gabansa gami da watsa idanunsa saman glowing beach din da ruwansa ya fara komawa sea of stars,hakanan yashin dake kwance a wajen ya soma glowing sosai kaman an warwatsa taurari a qasan wajen. "Wai wanne irin kame kake ne dude?.....har mutum nawa zaka saka a kulle maka?". Idanunsa da suka masa nauyi saboda tunanin daya cika zuciyarsa ya janye ya maida kan farouq,ya kafeshi da idanu sosai saboda tunaninsa ba'a wajen yake ba. Gaba daya tunaninsa ya ta'allaqa a kanta,yana jin a yadda yanayin wajen ya masa kyau da dadi kamata yayi ace tana tare dashi yanzu haka a gefansa,ya shaqi daddadan qamshin jikinta.....lallausar fatar nan tata me wani irin dumi me bawa zuciya da gangar jiki nutsuwa. "Duk wanda ya taba kiranta da karuwa......duk wanda ya taba yi mata sharri ko qazafin zina ko neman maza......bazan qyale kowa ba farouq". Kallonshi sosai farouq yakeyi yana kallon yadda idanunsa suka jirkice da wani irin giyar soyayya me qarfin gaske. Ya karanci wani muguwar kwankwada fu'ad ya yiwa giyar soyayyar sabreen din,ta kuma bugar dashi fiye da yadda ya kamata. "To amma ai sai ka hada da kanka da kanka a kullewar ko?" Ya fada yana dage masa girarsa duka biyun sama. Kallon days jefeshi dashi ya tabbatar masa b'arna fu'ad zai masa,ya sanshi yasan abinda zai iya aikatawa,don haka yaja kujerarsa baya da sauri yana dariya. Qwafa yaja yana gyada kai,baisan abinda yakeji ba tabbas farouq da bai qara masa ciwo akan ciwo ba. Barinsa yayi yaci dariyarsa me isarsa kafin ya kira sunansa. "Yes sir" Ya amsa masa har yanzun lamarin fu'ad da gaske yana bashi dariya. Yana sassauta masa ne kadai saboda yasan bashi da wani gurin samun sassaucin sai wajensa. Sai daya ware idanunsa a kansa sosai sannan ya tashi ya zauna yana dubansa. "Me yasa soyayya take haka ne?" Yayi tambayar sounding serious......saidai kuma abun ya bawa farouq dariya amma ya danneta. "Me tayi maka kuma?" Ya tambayeshi yana matse dariyarsa da kyau. Kasa magana yayi don baisan ma yadda zai kwatanta masa ba,sai kawai ya dora hannunsa akan qirjinsa da yakeji zuciyarsa na azalzalarsa akanta. Ya dauki wasu sakanni kafin ya iya buda bakinsa a hankali da wani irin calmness. "Bansan adadin Lokacin da na dauka ina sonta ba......amma inaji a jikina ba sai bayan abun nan ya faru ba na fara sonta.....kaman wani dadadden so ne daya saba dashi.....na taso dashi,aka kuma haifeni dashi". Sosai maganganunsa ke ratsa farouq......da gaske ne fu'ad din yana sawun mutanen da suke iya boye so ba ko su daukeshi da sauqi ba. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ 88 "Kayi qoqarin koya mata yadda zata soka........ta fahimceka.......tasan ainihin waye kai da kuma rayuwarka,daga nan komai zaizo da sauqi......zan baka kowanne kalan goyon baya da kakeso.....nayi maka alqawari......amma nima kayimin uzuri daya alfarma daya" Ya fada yana kama hannun fu'ad din. "Fadi muji dude" Ya fada yana sake jin qaunar farouq da kimarsa tana ratsashi. "Duk sanda naga taka kalar haukan soyayyar ka yiwa Allah karka hanani inyi dariya......i swear wallahi kai babanmu ne ta nan.....nayi imani da gaske irinku masu shuru shurun nan kunfi kowa zurmawa da iya rikita mata". Danawa bayan hannun farouq dake cikin nasa duka yayi yana zame hannunsa sannna ya miqe. "Ka lallabani farouq......kasan Allah zan daga aurenka?". "Iyeeee.....eh ai kayi haka mana,tunda kai ka samu kanka ka zazzage lalurarka ta shekara da shekaru...." "Idan bata haukatani ba farouq kai zaka haukatani" Kawai yace dashi yana yin gaba abinsa. Da sauri farouq din ya tashi yabi bayansa,don yasan tsaf zai iya tafiya ya barshi a wajen. Tuni suka gaya masa an biya kudin komai da komai tun kafin suzo ma,harda qarin wasu kudin spare da yayi ragowa idan suna buqatar qarin wani abun.