← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 215

Sashe 3

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

rabbul arshil azeem" Ya furta a nutse,take taji zuciyarsa tana sake samun nutsuwa da aminci. Komai ya tattare yana duba lokaci,cikin jikinsa yake jin ya gaji,yana buqatar cikakken hutu kafin gobe,so samu yabar qasar nan da kwanaki biyar,to amma ya fahimci zai wahala dama ta bashi hakan. Sanda suke takawa da guard dinsa zuwa mazaunin motocinsa guda biyu kira ya shigo wayarsa. A gajiye ya zura hannunsa a side pocket dinsa ya zaluqota. Taku biyu baya sukayi dukkaninsu,wanda wannan kuma sabonsu ne,don basu tsaiwa a waje muddin zai amsa waya,saidai idan shine ya buqaci hakan. Sosai ya zubawa sunan ido yana kallonsa,yayin da zuciyarsa ta cika da wasi wasi da saqe saqen abinda kunnuwansa zasu iya jiye masa daga bakinta. Yaci gaba da irga bugawar da wayar keyi,wanda yake jinsa kamar daidai da bugawar numfashinsa. Ko a tarihi,ko kuma a labari yana kyautata zaton shi din yana cikin mutane sahun farko da idan labarinsu zai fita a kundin littafin al'ajabi zai ja hankalin mutane da dama. Kiran uwa na daya daga cikin kiran dake sanya dukkanin yaro alfahari.......kiran uwa na daga cikin kiran da kowanne yaro ke fatan gani a kowacce rana.....kiran uwa kira ne dake iya juya zuciyar kowanne yaro daga baqinciki zuwa farinciki.....amma banda su......banda tasu mahaifiyar......banda kuma nasu kiran wanda ba komai a cikinsa face zallar ko kwanto da didibniya tsakanin lalubo alkhairi ko sharrinsa. Yana daga cikin motor qafafunsa suna waje ya zauna,yana qoqarin lalubo nutsuwarsa da yakan rasa a duk sanda kiranta ya riskeshi ya daga wayar. Alamun daga kiran ya sanyata sake hada nutsuwarta waje daya,gami da dagawa hajja furaira hannu wadda ke lissafo mata tsare tsare na abubuwan da suka shirya gudanarwa a wata shimfidaddiyar farar takarda. Tsit wajen yayi,bakajin motsin komai da kowa,abinda zai sanya wanda ke nesa irin fu'ad din xaya dauka ita kadai ce wanze a dakin. "Barka da warhaka" Ya furta da muryar nan tasa dake da tasirin kwarjini me yawa da haiba a ciki. "Barka kade.....ina fata kana lafiya?" Ta masa tambayar data zamo abu mafi dadewa baiji ba daga bakinta. Duk da zuciyarsa ta kasa yarda haka siddan tayi kiransa amma ya hadiye wannan.....ko yaya yaji dadin tambayar cikin ransa koda kuwa da manufa aka yita "Alhamdulillah.....Allah yasa kuma hakan" Dan murmushi ta saki,zuciyarta tana ayyano nesanta zuwa kusa da ita. "Lafiyarmu qalau,sai shirye shirye da muke yi gadan gadan". Bai wani fahimci shirye shiryen da take magana a kansu tashin farko ba......har sai data dora da nata bayanin. " Na kiraka ne don na shaida maka.....ina buqatar wasu kudade da zan qarasa duk hidimomin da suka ragen.....ta bangaranka da kuma bangaren ita kanta amaryarka......don kasan hidimar biki ba qaramin abu bane,......bare ni da zan aurar da dan fari......kuma ita kanta yarinyar ya kamata ace ita,danginta da dukkan wani dage da jibi da ita yasan cewa tabbas da gaske mamallakin diamond company zata aura.......banason harkar qaranta......ya kamata duniya kanta ta shaida d'ana zaiyi auren fari". Kusan koda yaushe fitar kalmomin bakinta suna zame masa tamkar makaranta ne......ya jima da sanin maamah din macace me son izza da nuna isa.......ya dauka wani tsohuwar dabi'a ce a tattare da ita.....amma xuwa yanzun ya sake amanna mutuwa ce kadai zata iya samun nasarar rabata da wannan halin. "Me ake buqata?" Ya tambayeta kai tsaye.....don shima da nashi plan din. Zuwa yanzu yana kallon komai ne tamkar a tafin hannunsa ake shiryashi,abinda ya rage masa ya sani kuma kadanne da bayajin zai zame masa me wahalar riska. "Kudi nakeso ka sakamin......sannan ka sakawa amaryarka......kamar million......." "Kiwa saddiq magana......zan gaya masa ya saka miki adadin abinda kike buqata" Ya yanke bayanin da taso yi masa da adadin kudaden da duk da yasan ya jima da fin qarfinsu........amma kuma ana nemansu ne a muhalli da gurbin da babu buqatar yawan wannan adadin. Murmushi ta saki tana jin wani dadi yana ratsa zuciyarta,tun a yanzu tana sake samun tabbacin nasarar dake bibiyarta,tana kuma fara jin qamshi da dadin da uwa keji a yayin da take gwada girman izzarta akan yaranta suke kuma bibiyarta sau da qafa akan duk wani buri ko quduri nata "Allah yayi maka albarka" Ta fada tana murmushi. Kalmar ta dinga masa amsa kuwwa cikin kunnuwansa,sai ya dinga jin kamar ba daga bakin maamah ta fito ba. Idan yace bazai iya tuna ranar data fadi wannan kalmar a kansa baiyi qarya ba. A hankali sai yaji kaman zuciyarsa tana rugujewa. Inama ace ta fadi kalmar ne domin cancanta da kamatar ta fadeta a kansa?,bawai don duniya ko wani abu dake cikinta ba?,bawai don son rai ko biyan buqatar rai ba. Da wannan murmushin dake sake yalwata saman fuskarta a kowacce rana ta ajjiye wayar saman table din gabanta. Qasaitaccen table ne da yazo cikin set na kayan furniture din da aka qawata sabon gidan nata data riga kowa tarewa a ciki. Gida ne datake jin zata kece biki na alfarma a ciki......zata daga sunanta da kuma martabarta a idanun qewaye dama duniya gaba daya. "Kowanne motsinsa sai ya dangantani da saddiq hamza kibiya" Ta fadi tana duban idanun hajja,har cikin ranta tana jin wata wuta tana ruruwa tare dason gaggautowar ranar da zata saka kakkaifar wuqarta ta yanke wannan alaqar da tafi mata kama da baqar alaqa. "Hanzarin na mene mariya?,saurin me kikeyi ne?,saura kwanaki nawa duka duka?" Hajja ta bata qwarin gwiwa tana cike da kwadayi da son jin abinda ya faru tsakaninta da fuad din. Kai maamah din ta jinjina tana son dawo da walwalarta kaman daxun. "Bai tsaya jin koma nawa nake buqata ba......kawai yace nayi magana da saddiq,shima zai masa magana na karbi abinda zan karba din......kinga zan karbi kaso biyu kenan......da nawa dana yarinyar can,zan san mata wani abu a ciki ne kawai.....sai na cire abinda zan cira a ciki.......zan ware na boka donshi kansa yawan kudin dana qara masa akan wanda ya buqata na fahimci ya qara masa azamar aikin nan.....hajja" Ta qarash da kiran sunanta da wani irin sauti dake nuna gajiya da zallar zaquwa. "Inaso yayimin aiki irin aikin da bai taba yin irinsa ba tunda ya fara harkan nan......inason yayimin kalar aikin da ba fuad ba......ko tsuntsun gidan fu'ad sai ya zama me biyayya a gareni........inason yayimin aikin da sabreena zata koma tamkar bawa da ubangidansa a hannuna........bansan me yasa yarinyar ke yimin kwarjini ba,bansan me yasa nakeji wani abu daban ba idan ta kalleni......inason dukka wadannan abubuwan su shafe daga idanuna". Wani murmushi dake dauke da tarin boyayyun ma'anoni da rufaffun qudurori dake amsa kuwwa da amon nawa burin yana sama da naki hajja tayi,sannan ta harde qafarta tana cewa. "Dukka wannan qanqanin aiki ne a wajensa,kuma ko iya haka aka tsaya zaki bawa wani labarin zafin aikinsa......isassun mata kawai ke iya aiki dashi,matan manya da iyayen manyan mutane irinki,saboda daga sadakin aikinsa kawai zaki fahimci ba gama garin boka bane.....don haka ki rubuta ki ajjiye.....dukkanin wadannan burirrika naki tamkar sun gama cika ne......saidai banji share dita a wannan kasafin naki ba". Rausayar da kai maamah tayi tana sakin murmushin jin dadi. A qasan ranta tana mamakin son kudi tsantsa irin na hajja din,duk kuwa da cewa lullube take cikin wadata me tarin yawa.......saidai wadatar yaranta idan kaf idan aka hadesu batakai kaso daya cikin ukun abinda fuad ya mallaka ba shi kadai......amman duk da hakan bata raina kudi komai qanqantarsu(tabbacin zuciya ta zarme da yawa dason abun duniya,Allah ka kiyashemu). "Baki da dukkan wata damuwa hajja,kina da million uku a ciki,kafin alqalami ne kawai......kuma somin tabi,nan gaba kadan ke zaki dinga bada wannan adadin a matsayin taki kyautar" "Qwarai da gaske kuwa mariya" Hajjan ta fada kanta tsaye tana duban idanun maamah da wani irin confidence daya sanya maida hankalin maama duka a kanta. Wannan ya sanya ta sassauta kaifafa harshenta da nuna dukkanin qwarin gwiwar dake kan fuskarta. "Yaronki ai yarona ne mariya...ni nasan bani da haufi....ba zaki taba butulcemin ba" Ta sake yiwa kalamanta ado da wasu kalmomin "In sha Allahu" Maamah ta amsa tana rausayar dakai har yanzu murmushin na saman fuskarta,ta kuma jawo wayarta tana fadin "Bari na nemi musaddiq ya nemo yaron can,don da zafi zafi ake dukan qarfe......gobe nakeso muyi sammakon tafiya hado dukka ayyukan dama sauran bayanai......bikin nan da gaske tahowa yakeyi,kwana shida kacal ya rage......inason tasan da zaman kowacce doka qa'ida dama sharadi kafin ta samu lasisin karbar igiyoyin auren d'ana a kanta". Da wani kallo hajja ta bita kawai ba tare da tace komai ba.....saidai kuma can cikin wani saqo na zuciyar magana ce me yawa nauyi da kuma dogon xangon da bazai yiwu baki ya furtata ba. Daure da babban towol da kuma da kuma wani babba data lullufe jikinta kirif tun daga saman kanta take takowa daga cikin toilet din dake manne da falon tana dawowa cikin ainihin falon daya zama sansaninta a yanzu. Nan din wani kebantaccen guri ne cikin gidan nasu,da asalinsa ya zama muhalli ne na mahaifinsu,wanda tun bayan shudewarsa ba wanda yake ta'ammali da wajen,don gidan nasu ya wadaci kowa,kawai sai saman inda falon nasa yake ya zama wajen da akan bude ne kawai a share,sai idan wani taro ya tashi kuma cikin gidan sannan akan zauna a ciki har ayi a gama. A yanzun saman ya zama kusan nata,tunda aka fara mata aikin gyaran jikin ko qasan gidan bata saukowa. An killace muhallin da komai da zata buqata,kaman yadda aka ajiye mata cima kala kala wanda sam basu taba birgeta ba koda qanqani. Hasalima ita a yanzu cin abinci ya zame mata daya daga cikin horon da mamma bahijja keyi mata. Koda kuwa ta kauda kai ta kuma kafe akan ba zataci ba,mamman bahijjan data tsaya a bigiren da akan buqaci uwa saita nemo wani abu daban ta bata,takance "Aure zakiyi fa sabreena,gidan miji zakije,anata gyaran fata amma can cikin ko oho?,kinsan yadda yunwa ke kassara ni'imar mace kuwa?" A duk sanda ta furta hakan sai sabreen taji kaman wani abu ya shaqe mata wuya. Wai halan basu kula kuma basu lura da dukkan komai?,sunata magana akan auren da ba komai a cikinsa face zallar rudani?,rarrabuwar burika da kuma tarin biyan buqatar rayuka masu yawa a cikinsa?. A yanxun data dawo daga dauraye jikinta da tayi daga gyaran jikin da kullum kwanan duniya takeji kaman ana mannawa fatarta wuta.....duk inda ta gifta kota zauna
Chapter 3 · 0% Book details