Sashe 46
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
duba waiko ya zauna cin abincin?. Bataso yadda tashin farko suka hada idanu ba don zaya dauka ne kawai kallonshi takeyi,take tata izzar itama ta motsa,ta dauke kai sosai tana takawa zuwa qofar kitchen. "Hey.....com here" Ya fada da matsakaiciyar murya. Tanason gwada masa tsiwar amma tana tsoron abinda zai biyo baya,dole ta dawo din fuskarta shimfide da kalar nata miskilancin. "Serve me" Ya fada cikin basarwa yana bude wayarsa. Cak ta tsaya,tana jin kamar kunnuwanta ne suke jiye mata ba daidai ba. Ta zuba masa abincin fa ya buqata?,ta tambayi kanta tana neman qarin haske. "Zuba abincin nace" Ya sake maimaita mata ba tare daya dubeta ba. Wani irin abu taji ya tsargawa sassan jikinta. Ta dade tana fatan zuwan wannan ranar,ta dauka duk sanda taxo din zata kasance mutum da tafi kowa murna a duniya,amma kuma sabanin murnar mutuwar jiki taji. Matsawa tayi sosai gaban table din,ta ware qananun luxury table mat din ta sake shimfidasu,sannan ya zari plate da bowl ta soma zuba komai tsaka tsakin quantity sannan ta jera masa a gabansa. Wayar ya ajiye a gefansa,ya miqa hannu da kanshi ya ciro spoons guda biyu ya saka cikin abincin sannan ya dubeta "Oya.... Let's eat together" Ya furta yana matso da drinks din da aka aje a wajen duk da ba abun shansa bane sam sam duk wani drink da company ta sarrafa. Ba shiri ta bude idanunta a kansa,ji tayi kaman an dauko guduma an shirga mata. Cikin qasa da minti daya tayi qoqarin daidaita nutsuwarta dukka a qoqarinta na daidaita komai,ta girgiza kai tana fadin "Na qoshi". Sake ware idanunshi sosai yayi a kanta yana dubanta,abinda ya sake sanyata kenan a tsilla tsilla,tana kyautata zaton akwai wani abu me nauyi da idanunsa ke dauke dashi,wanda muddin ya kama zuzzurfan kallo irin wannan sai kajishi har qashinka. "I think kin fito ne ke debi abincin right?" Daburcewa tayi yanda ya kama abinda ya fito da ita din kansa tsaye kamar me gani har hanji. Bata saba qarya ba koda wanne irin hukunci aka tanadar mata,wannan ya sanya kai tsaye ta bashi amsa da eh. "Good.....kinga wannan shi yafi kamata muci tare ko?" Ya fada cikin sigar saukar dakai yana turo abincin gabanta. Kanta ta sake kadawa,gaba daya yana birkitata ganin yadda yake matsantawa saita zauna sunci abincin "Seat down!" Ya fada da wani irin husky voice yana buga hannunsa saman table din har abincin dake cikin plate din yana watsewa saman table din. Batasan sanda ta zauna ba kaman yadda ya buqata tana qoqarin kaucewa kallon fuskarsa da har hancinsa ya fara yin ja alamun tsananin bacin rai wajen farin mutum kenan. "Kinsan abinda zan gaya miki guda daya?" Yayi maganar qasa qasa kamar ba shine yanzu ya buga wannan tsawar ba,bai jira ta amsa ba ya dora da fadin "Duk sanda kika qara yimin girki a gidan nan saikin cinyeshi tsaf!". Gigicewa ta sakeyi da abinda yace,maganar daya fada kawai ta sanya hasashenta ya tsaya daidai inda take zatonsa "Be warned!" Ya furta yana ranqwafowa sosai saman kanta har tana iya sheqar dumin numfashinsa da yake futarwa daga hancinsa. Baya yaja ga kwashe wayoyinsa,zuciyarsa na masa wani irin zafi ya soma sauka daga wajen yana dosar hanyar da zata sadashi da stair dinsa. Maamah uwarsa ce,ba yadda zaiyi da ita,amma zaiyi dukkan abinda zai iya ya toshe kowacce qofa da zata samu nasarar budeta a kansa ko kuma waninsa muddin yana da iko da masaniya. Koda ya koma saman duk yadda yaso yayi keeping kanshi busy ya manta da komai sai ya kasa. Mahaifiyarsa......macen daya biya kudade aka daura mata igiyarsa..... A duniya idan akwai wasu mata da sukafi kowa kusanci dakai suna sama da wadannan ne?. Me suke nema a tare dashi?,amsar daya kasa laluba kenan. Sosai abun ya dinga masa ciwo,shi yasa ko sau daya bai taba aminta da ita ba,ko sau daya bai taba jin ya gamsu da ita ba......takowacce fuska tana da qatuwar lam'a da tabon da shi shine babbar shaida......bayan tarin shaidun da ya samu har abinda be nema bama an bashi,ta yaya zai iya kallonta a matsayin wankakkiya?,ta yaya zai iya yafe mata?. Yanason ya zame mata lesson me girma a rayuwarta,zai kuma ganar da ita kuskurenta na shiga rayuwarsa hakanan kai tsaye. Daga qarshe dai dole ya kunna karatun qur'ani daya karade ilahirin sassan nasa,yayi kwance kawai idanunsa a lumshe sautin yana shiga kunnensa,sannu a hankali kuma nutsuwa ta fara samuwa a jikinsa. Ko qwaqwaran motsi kasa yinsa tayi ballantana ta tashi daga wajen,batasan adadin lokutan data shafe zaune a wajen ba,har sai data daga idanu taga agogo yana gaya mata qarfe goma da rabi saura mintina biyar sannan ta iya miqewa. Zuwa sannan hatta da qafafunta sunyi wani irin nauyi da sanyi,saita gaza shiga kitchen din ta zarce hallway din sannan ta fada dakinta. Rasa abinda ya kamata ta tuna tayi,ganinta yayi kenan koko yaya?. Karon farko da taji wata irin nadama na saukar mata. Ya akayi ta biyewa mamah din ta yarda ta ciyar dashi gubar da batasan ranar yankewarta ba?,wacece maamah din?,me kuma take qullawa?,me take buqata ne a rayuwarta sama da rayuwar da take ciki?. Zafi sosai takeji cikin ruhinta,tunda take bata taba sha'awar ciyar da wani ko shayar d wani wani abu me illa irin wannan ba,koda sanda take shirya gyara zaman mazan da suka zabi harka da mata kuwa. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ _Daba abu hurairah RA yace,manzon Allah S A W yace "mafi falalar sallah bayan sallar farilla itace sallar dare_ *_ga falala ga kaifi,biyan buqata kaman yankan wuqa ,Allah ya bada ikon jurewa_* ____________________________