Sashe 201
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta dauki waya ta kira sabreen. "Dawo ciki ina parlor" Bata ko iya amsawa mummy ba,ta kashe kiran kawai ta miqa bata ko bi takan furar data ajjiye ba ta fice. '"Zauna a nan" Mummy safuura tace da sabreen tana nuna mata gefanta. Sam fuskarta ba alamun wasa a ciki. "Sabreen" Ta kirata a tsanake. "Na'am mummy" Ta amsa mata kowacce hanta dake cikinta tana kadawa. "Ki gayamin gaskiya,da iznin mijinki kikazo nan koba da izininsa ba?" Shuru tayi tana juya maganar mummy,nadama da tsoro suna cikata. "Ki fadamin gaskiya,don kinfi kowa sanin halina bani da sauqi,ba ruwana da wai kedin 'yar 'yar uwar mijina ce.....bata yadda za'ayi baban yarannan yayi tattaki yazo har nan,ya kuma dauke yara ba tare da sanin mahaifiyarsu ba" . Wannan abun wani baqon abune wajen sabreen din,ballantana ita din da sam sam bata son tashin hankali ko kadan. "Da saninsa,saidai baisan nan zamuzo ba,kuma har mu kwana" Take ran mummy safuura ya baci sosai,ta zubawa sabreen idanu tana jin kaman ta rufeta da duka. "Me yasa?" Ta tambayeta a taqaice,irin taqaicewar data nuna mata batason wani dogon sharhi ko dogewa. "Mummy tsoro nakeji". " Wani irin tsoro kuma?" Ta fada tana zare mata idanu waje. "Ciki mummy,inaso na huta......shi kuma haihuwa yakeso akai akai". "Haihuwarce ke bakiso saboda mamarki kuda yawa ta haifa?". Kai ta girgiza saboda tasan magana mummy ta gaya mata a fakaice. "Hutawa kawai nakeso na danyi mummy sab....." "Gafara can dalla ki rufemin baki malama,"Amma ban taba raina wayonki ba irin yau sabreen......ni'imar da Allah yayi miki kika sanya qafa kike shureta?.......ashe baki da hankali ban sani ba?,idan muhammad jadda beso haihuwa a dukiya da lafiyar da Allah ya bashi ba......ki gayamin me zaiso?,sometimes mata ku kuke kirawa kanku kishiya wallahi" Idanu a waje ta daga kai tana duban mummy jin ta ambaci kishiya. "Yes....kishiya,ga abinda mijinki yakeso amma ke kullum kina opposition party nasa.....me zai hana ya nemo wadda ra'ayinsu da komai nasu yake daidai?......to wallahi bari na rantse miki,nima yau dinnan basai gobe abbanku ya dawo ba,ba zaki sake kwanar mana a gida ba.......sauqinki daya na sakaki a jirgi na maidaki gida a ranar yau,muddin kika sake ya dawo yaji abinda ya faru saikin gwammace bakizo abuja ba....zan rufa miki asiri bazan gaya masa ba,shine kawai abinda zan iyayi miki" Kuka sosai ya qwacewa sabreen,komai ya dagule mata cikin lokaci qanqani. Kafin mummy ta nema musu ticket a gama komai nononta duka ya ciko yanata damunta,alamun dake nuna mata tabbas su fawwad sun tashi. "Me zai basu idan sun farka suna jin yunwa?,ta yaya zai iya kulawa dasu?" Tambayar data dinga yiwa kanta kenan,harta kasa jurewa ta tambayi.mummy safuura. Duk da yadda tayi laushi lokaci guda ta bata tausayi amma saita jefa mata harara sanda take hada mata sauran kayanta. "Ke kika sani,ban sani ba" Ta fada cikin jin haushi. Haushin kuma bai hanata ta hadawa sabreen din komai ba "Idan kinje kin nutsu kinwa kanki fada na miki bayani". Abinda kawai tace da ita kenan. Da kanta ta dauketa a motarta har airport,bata kuma dawo ba sai data tabbatar da jirginsu ya tashi qarfe takwas na daren ranar. K'arfe tara da minti ashirin da uku daidai na dare cave din airport ya saukesu a qofar gidan muhammad fuad jadda. Karon farko da taji tana fargabar shiga gidan,abinda bata taba ji ba tun bayan data amsa cikakkiyar sunan matar muhammad fu'ad jadda. Bata sake fahimtar waye take aure ba......bata sake fahimtar girman matsayin da Allah ya bata ba sai da suka tasamma shiga unguwar. Tun a main get na shigowa unguwar suka fara fama da tambayoyi na securities dake tsaron kowanne gate na unguwar. Yawancin gurare saita laqo tayi magana sannan suyi salute nata su dage musu su wuce,abinda bai taba faruwa ba kenan,don duk inda zasu plate number din motocinsu ne kadai amsarsu,amma yau din sai da tasha bayani kafin su samu su iso qofar gidan. Gaba daya masu gadin gidan mamaki ya kamasu ganin madam guda a cab. Cikin rawar jiki da kuma girmamawa suka bude motan suka shiga fidda luggage dinsu zuwa cikin gidan. Tun a veranda ta sallami nannies dinsu fawwaz,cikin fargaba ta dinga takawa zuwa cikin gidan,tana jin kamar ta kirasu su tayata bawa fu'ad din haquri. "Barka da dawowa......tun daxu nake zuba idanun ganin fitowarki ai" Muryar ma'u ta sauka a kunnenta. Dukka dauriyarta ta tattaro ta sakar mata murmushi "Yauwa ma'u......ashe kina ciki" "Eh na shigo ne na zare socket na freezer dincan,kayan ciki duka sun qanqare,kada mu tashi girki gobe qanqara ta hana ciro komai......ya hanya?,dazun na dan jiyo qushin qushin din mutanen nawa". Dan murmushin yaqe ta saki,ta san tana nufin su fauzan ne. "Kinsan basa rabo da rigima idan sukaso,duka su ukun saisun hade maka kai" Dariya ma'u tayi. '"Ai inajin sai wajen gobe zamu hadu dasu,Allah ya huta gajiya uwar dakina" "To ma'u na gode". "Ba'a buqatar komai ko?" Ma'u ta tambaya. "Babu ma'u,bari na qarasa ciki" Da haka sukayi sallama ta wuce parlor na biyu kai tsaye ya doshi hallway dinta. Wata matsananciyar kewar yaran takeji tana damunta,tanajin kaman ba awanni kadai ta dauka bata gansu ba,ji take kaman shekara bata gansu ba,wani qaunarsu tana sake taso mata kaman ba zata iya qara minti daya cikakke bata gansu ba. Kai tsaye dakinsu dake hallway din ta bude,bata gansu ba a ciki,hakan ya bata tabbacin suna samanshi kenan. Kaman ta wuce dakinta amma sai taji ba zata iya ba,ta soma takawa zuwa saman nasa tana qoqarin dake zuciyarta.. Ta kusa minti uku bakin smart door din sannna ta matsa inda tayi scanning nata,kai tsaye kuma ta bude kanta da kanta tana bata daman shiga. Scenes din watannin baya da suka shude ne suka shiga dawo kata kanta sanda ta hangeshi zaune saman minotti sofa dinsa.......watannin da take a matsayin sabreen dinta ta ainihin,wannan sabreen din wadda babu qaunar Muhammad fu'ad ko qanqani cikin rai da zuciyarta. Yana zaune gabansa ya bude apple system dinshi har guda biyu,da alama kuma aiki yakeyi sosai,koma ya jima a zaune a wajen,don ya saye idanunshi da farin glass din nan nasa dake bada kalan light blue sama sama wani lokaci wanda ke taimaka masa wajen zuqe hasken screen din. Kansa ya daga a nutse yana gyara zaman glass din a fuskarsa,lokaci guda kuma ya dauke idonsa daga inda take a tsaye ya maida idanun kan screen din yana taba Bluetooth din kunnensa "Am hearing you" Daya fada shi ya alamta mata cewa waya yake amsawa. Duk da haka bata fasa sallama ba don tasan ita din me laifi ce,ta taka a nutse tana shiga ciki idanunta nakan wani irin gado dake wani shiyya daban na parlor din. Kaman gado kama lilo haka aka tsarashi,amma idan kakalli cikinsa sosai zaka fahimci gado ne na 'ya'yan gata wanda aka yi masa lafiyayyar shimfida me tsananin taushi. Gaban gadon ta tsaya tana qare musu kallo,sai wani tausayinsu taji yana ratsata. Kayan jikinsu na dazun yanzun ba sune a jikinsu ba,an canza musu su zuwa kayan bacci masu taushi na jarirai farare qal dukka iri daya,hatta da socks na qafansu dana hannunsu,sai suka sakeyi mata kyau,taga kaman sun qara girma akan girman su na dazu. Kewarsu takeji sosai,don haka ta miqa hannu don fara daukan almustapha. A qirjinta ta sakashi,ta rungumeshi sosai tana shafa kan fawwaz. Ta jima a haka kafin ta sanya fawad a kafada daya,fawwaz a daya kafadar,ta fara takawa a hankali tana sauka dasu. Sai data kwantar dasu sannan ta dawo ta dauki fauzan. "Kinci darajar ma'aiki daya hana raba uwa da d'anta......banda hakan da daga yau ba zaki sake dora hannunki kan yara na ba" Maganar daya fada kenan wadda ta sanyata tsayawa cak. Batayi tunanin ya gama wayar da yakeyi ba,a sanyaye ta juyo zuciyarta na bugawa,saidai kafin ta gama ajiye kallonta a kansa tuni har ya wuce dakinsa abinsa. Jikinta a mace ta gama shirin kwanciya tana juya maganarsa a ranta. Tayi fakare tana jira taji ko zataji shigowarsa?,don ko dakin bata kulle ba,hakanan su fauzan duka akan gadajensu ta kwantar dasu,saidai harta gama zaman jiransa bacci yayi awon gaba da ita. Koda ta tashi har an gama sallar asuba. A gajiye ta miqe tana duba ko ina na dakin,ba alamun ya kwana a dakin,a haka taja jiki zuwa toilet tayi wanka sannan ta hada da alwala ta dawo ta bada farali. Shiryawa tayi cikin sassauqar doguwar riga data mata kyau ta fidda quruciyarta. Qarfe bakwai da ashirin ta wuce zuwa kitchen da nufin shirya masa breakfast,don bata da scheduled dinsa na satin gaba daya,amna ta tabbatar dole zai buqaci breakfast din. Kafin ta kammala har ma'u ta gyara su fauzan gaba dayansu,sai ta shiga wuce daki kawai ta gyara jikinta. Kwalliya tayi sosai data dace da safiyar,ta wadata jikinta da sassanyan qamshin nan da tasan yana masifar so. Bata ma dauki su fauzan ba kai tsaye ta wuce zuwa samanshi. Koda ta samu daman shiga parlor din bata wani ji motsinsa ba,don haka ta wuce zuwa master bedroom dinsa. Tun a nan ta fahimci tuni ya fita,don ga alamu nan sun nuna,comb dinsa da towel dinsa,da qaramin cup da yasha ruwan dumi duka saman mirror. Zama tayi gefan gadon tana maida numfashi,hakan yana nufin yayi fushi sosai da ita kenan?. Wayarta ta bude ta soma kiran numbers dinsa,saidai kowacce gaya mata akeyi a kashe take,dole ta haqura da neman nasa ta sauko qasa saboda kukansu fawwaz da yayi mata maraaba. Tana shayar da yaran amma duka hankalinta yana kan tunaninsa da tunanin abinda ya faru. Duk hankalinta a jagule yake gaba daya,ta dinga gwada kiran number dinsa amma bata shiga,tun tana sanya rai harta haqura ta daina neman nasa,sai gajeran saqo data tura masa,wanda shima har magariba tayi bata samu amsa ba. Magariba ta wuce,isha'i ta shigo itama ta wuce,shuru ba shi ba wayarsa ba dalilinsa. A haka ta samu su fauzan dukkaninsu sukayi bacci,don dama idan sun jima sukai bayan ishai'i,idan kuma suka kwanta matuqar sun tashi to yunwa ko qishirwa ya tashesu,basa farkawa yawanci da safen ma,sai sukai bakwai da rabi har takwas suna bacci abinsu. Baccinsu ya sake sakata ta dan qar samun nutsuwa. Wannan karon koda ta kirashi wayar yana shiga,amma haka ta qaraci b'urarinta ta katse bai amsa ba. Dole ta ajiye komai