Sashe 162
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
qaryata ba shine yaci din bama qular da ita yakeyi. "Dama kai dinne ko?" Ta fada tana watsa masa harara da jiqaqqun idanunta,sai ta sake fashewa da kuka sosai kaman wadda aka yiwa dukan tsiya harda shashsheqa. Ya rude sosai don ta maida abun serious matter. Ya sulale ya tsugunna a gabanta yana cewa. "Am really sorry my world......taso muje ki gayamin a inda aka siyo a sake nemo wani". Sai data galla masa harara sannan tace. "Kaduna.....kaduna ne wajen maman ummi". "Kaduna?" Ya maimaita. "Eh" Ta fada cikin son jiran mutum yayi wani abun ta sake barke masa. Kansa ya daga ya kalli agogo yana duba lokaci. Qarfe goma na dare,wa zaya tasa zuwa kaduna yanzu. Idonsa ya mayar kanta,saiya taras ta zuba masa ido tana kallonsa,dukkan alamu kuma sun nuna rigima ce a kwance idan ya musa. "Is alright.....bani details na masu abun". "0803 049 9555,wallahi tunda ummee ta haifeni ban taba cin doughnuts me dadin nata ba" Ta fada bilhaqqi da gaske har zuciyarta tana jin tun kafin ya kawl ma yawunta ya tsinke. Idanu warwaje yake kallonta. Tashin hankali!,ya fadi saboda yadda yaga tsaf ta haddace number,yaushe hakan ta faru oho shima bai sani ba. "Ina zuwa" Yace mata yana takawa a hankali yana sauka qasan. Shi kam yasam yanzu ba lallai a bawa jadda wings daman tashi ba,kafin ma su nemo umarni,pilot din ya isa su tashi ai asuba yayi,saidai duk da haka bai fasa kiran number din ba. Ainihin sunan daya fito ameena sai yaji kimar me number ya qaru a idonsa tun ba'a daga kiran ba. Bugu na uku aka dauka da cikakkiyar sallama ya amsa shima. "Am sorry,na kira late at night......i don't know ko matar aurece.....am sorry idan hakanne" "Ba komai" Matar me kirki ta fada. Bayanin dalilin kiran yayi sannan ya dora. "If possible goben zan aiko a taho dake,kizo kiyi mata sai a maidaki.....kiyi naming price dinki,kada ki damu ko nawa ne ki zaba i will pay it". Murmushi tayi. "Ba matsala.....ko goben da safen ma ana iya samun ko pieces nawa takeso.....akai akai sai a dinga zuwa ana karba mata,Allah ya raba lafiya,kowanne ciki da yadda yake zuwa ma mace,sai haquri". Yaji dadin magananta sosai,don daga yanayinta ya fahimci ba yarinya qarama bace,yayi godiya sannan ya kashe ya kira farouq. Bugu daya ya samu farouq,da alama bacci ya fara daukansa ma. "Farouq akwai matsala fa" Maganan da ta saka farouq miqewa ya zauna "Me ya faru?" Ya tambaya. Ajiyar zuciya ya saki ya masa bayani a nutse. "I don't know ina zan samu doughnuts?.....kune masu zuwa irin guraren nan". "Ba damuwa......bari na duba wani guri kusa damu......sun iya sosai zataji dadinsa". "Thank you dude.....you save me" Ya fada yana dan dafe goshinsa sannan suka yanke kiran. Lallabata ya dinga yi har aka gaya masa ga saqo daga bakin gate. Sanda yaje har farouq din ya aje saqon ya juya,ya yaba masa sosai irin saurin da yayi don duka duka mintuna talatin ya iso,ya tabbatar wannan gudun nasa ya zuba. "Ga doughnuts din" Ya fada da murmushi yana aje box din a gabanta. Da zumudi ta jawo ledar ta bude. Tun a yanayin packaging din ta tabbatar akwai matsala,banbamce babance take gani iri iri da wancan,ta danne tana bude doughnuts din. Kanta ta daga ta kalleshi,ya dage mata gira yana qoqarin lallabata,can qasan ransa yana fatan kada ta ballo rigima kuma. Kanta ta mayar kai,ta gutsira tana kaiwa bakinta. Taunawa daya biyu ta furzar,muryarta tana rawa ta kalleshi "Wannan bashi bane.....Allah bashi bane". " I know sabrrrr.........kiyi haquri kici wannan din,i promise you da safe wancan din zakici as breakfast" "Really?" Ta tambaya tana tsareshi da idanu. "In sha Allah" Ya fada yana bata assurance. Hankalinta taji ya kwanta,amma duk da haka ta ture wancan din "Banasonshi....nata yafi dadi yafi madara" Dariyarsa ya boye,yana mamaki ashe da gaske masu juna biyu suna haka?,idan madara takeso suna da ita kala kala har sai ta ture,amma ya tabbatar yace tasha din ba sha zatayi ba.