Sashe 211
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
fitilun suna watsuwa a kansu,lokaci guda kuma muryoyin zuria'ar yara na jadda din ta hadu wajen fadin "Happy wedding anniversary" Sai a sannan suka ankara da komai da tsananin mamaki. Ameen,Amaan,hilal dan huda na fari,naseem dan amna na fari,sai yaron wajen farouq na farko shima Aleem,sai tagwayen sabreen na biyun masu bin su ameen Aabid da Aadil,sai wasu twins din masu binsu Aadil din,irfan da farhan wadda ameenatu iffa ita ta zama cikon ta gomansu. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 *_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_* *_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_* *_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_* *_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_* *_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_* *_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_* *_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_* *_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_* *_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_* *_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_* *_HAIHUWA KIKAYI?_* *_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_* *_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_* _Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_ 08104553105 08127084190 *_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_* *_BGAWO'S KITCHEN_* *MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU* 174 *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX Yara ashirin da daya ne idan ka dauke mutum biyar dasu nadra suka fita siyayya dasu.......sai fannah da huda dake tsaye a bayan yaran da alama su suka tayasu hada wannan surprise din. Inda Allah ya kawo ma sauqin abun amna bata nan,tare suka fita siyayyar dasu nadra tabbas da abun sai yafi haka. Kasa magana sabreen tayi,harga Allah tana sane da yau dinne suka cika shekara goma sha shida da aurensu,amma bata kawo zatayi wani abu da wani zai gane ba illa tsakaninsu ita dashi,sai gashi yaran sun rigata aiwatar da komai. "Ku ko?" Sabreen ta fada tana nuna fannah da huda,fanna din da amnar da dukkaninsu zuwa yanzu tana jinsu tamkar uwa daya uba daya suke. Tana nunasun da yatsa tana murmushi sai kuma kukan farinciki ya barke mata,ta aza kanta saman kafadar fu'ad din tana matsar qwalla. Irin wannan soyayya da suke gwada mata batasan wacce iri bace,bama ita ba.....kusan dukkaninsu ba zaka tantance wane da wane ga daga inda suka fito ba. Rankatakaf jikokin gidan dama iyayensu kallon uwa suke mata,kuma hakan baya rasa nasaba da yadda ta riqesu kaman ciki dayan suma fito. A cikin yaran ba wanda bata taba rainonsa ba,duk itama tata bataliyar,duk kuma da cewa kusan kowanne yaro yana da nanny dinsa a gidan,sai wanda suka kai shekarun girma irinsu ameen sannan ake barinsu su koyi rayuwa da hidimar rayuwar data zamewa kowa ya koyi yiwa kansa. Idanun yara kawai ya hana ya rungumeta,amma qasa qasa yake fadin. "Karki bata fuskarki,karki kashe mana farincikin yau" Ya fada yana dan bubbuga bayanta. "Kita fatan muci gaba da irga wadannan shekarun tare" Abinda ya rada mata kenan. Qaramin walima akayi a gurin da kayan maqulashe kala kala,kuma abunda ya bata mamakin shine,koda autar gidan iffa wadda tare suka shigo gidan sun tanadar mata gift din da zata bawa daddy jadda (yadda gidan suke kiransa kenan in general idan ba'a sassansa bane). Farinciki da walwala ne kawai ya wanzu a gurin,inda daga qarshe dai bata haura samanta ba kota wuce sassanta ta lalace a nan tana tsakiyar family din nata suka zarce da hirarrakin bikin da zaa fara jibi jibi. Wayarta ta ciro da zummar kiransu nadra taji inda suka dade haka da yawa sai taci karo da tarin miscal din jadda. Ta zaro ido tana mamakin tun yaushe yaketa kira bataji ba?,saiga shigowar wani kiran nasa. "Sabrrrr" Kawai ya fada a narke,take ta fahimci yana buqatarta a kusa dashi. "Banda abun hamma.....awa daya kawai ya rage ayi magriba fa?" Ta fada cikin mita tana tura katafariyar qofan master bedroom dinshi. Bata gama ajiye qafarta taji an ficikota ciki,a zafafe ya manne bakinsu guri daya ba tare daya jira komai ba. Har kullum har ko yaushe har kuma abada mantawa takeyi da shekarun dake wuyansu idan suna tare da jadda din. Wani irin mutum ne dake da baiwar narkar da zuciyar diya mace ya kuma mantar da ita komai. Abinda yayi imani dashi shine,yadda kowacce diya mace a kullum take fadi tashin neman hanyoyin faranta ran namiji da burgeshi,haka ya kamata kowanne namiji shima ya kasance cikin sanin hanyoyi da salon mallake zuciyar matarsa......wannan dabi'ar tasa ta sanya yayi zarra a zuciyar sabreen din. Sai data tabbatar ta samar masa da nutsuwa sannan ta baiwa kanta hutu tana aje numfashi,ya birkitota yana maqaleta a jikinsa bayan sunyi alwala sun dawo. Shuru ne ya ratsa tsakaninsu,kafin daga bisani taji saukar numfashinsa a hankali bacci me cike da nutsuwa yayi awon gaba dashi. Sai bayan sallar isha'i ta samu saukowa daga wajensa,a lokacin ya fita sallar isha'i,da wannan damar ta samu tayi wanka tayi kwalliya kuma cikin atamfa kaman yadda ta saba idan zasuci abinci nasu duka. D'as d'as take takawa kaman ba wannan jikin bane ya fidda rai goma ba,har ta iso babban parlor din da anan aka gina katafaren dakin cin abinci. Ta samu kowa yana gurin,kowa kuma yasan mazauninsa yana kai a zaune,sauran wadanda basu hadu ba sai a sannan irin musaddiq saddiq da farouq duka a nan suka gaisa suna tayata murnar ci gaban da aketa samu. Kowa ya hallara kuma faud din ake jira,shine qarshen shigowa,yana takowa a nutse da wata irin haiba da kwarjinin da ya qara yawa sanadin shekaru da kuma riqo da addini da yake dashi,kwarjinin da yake hana mutum musu dashi ko yin abu ba daidai ba,kwarjinin da hatta sabreen a yawancin lokuta yakan daketa duk kuwa da cewa dazu dazu suka rabu a daki cikin wani sirrintaccen yanayi,amma yanzun data kalleshi kwarjinin nan ya dawo fes saman fuskarsa. Kusan yara yaran a tare suka gaidashi,su sabreen huda fannah da amna suka fara serving na kowa da kowa a nutse ba wani hayaniya kaman ba taron mutum kusan talatin ba. Cikin qauna da tsabar sabo da juna suke cin abincin,hirarraki suna gudana a tsakaninsu. Har yau har kuma gobe yana maintaining class dinta a idanunsa,bata duba an dade tare.....an jima da juna ta dinga wasu abubuwa da babu aji sam cikinsa a wajen diya mace( mata yana da kyau ku kula da wannan,stay classy please,karki dinga abu gaban miji wargazaza koda shekara dubu kukayi ki tabbatar masa ajin nan fa akwaisa,idan ba haka ba ya hango wadda bata kaiki ba nata ajin ya dinga dibansa yana burgeshi). Shi dinma satar kallonta yakeyi,yanason gano meye ya banbantata da sabreen din shekaru goma sha baya?. Ya dade yana against in din maza da yawa akan suna da babban laifi da muhimmiyar rawa da suke takawa wajen wargajewar matansu,mace 'yar tattali ce.....'yar a bata kulawa ce,mace tamkar fure take,dole idan anaso aci gaba da ganinta sharshar a tsaya mata da ban ruwa,wato cima sutura muhalli abun sha me kyau,a debe mata damuwa daga zuciyarta. Ta samu daman zama da amaren nadra da haneefa har kusan sha daya na dare,don shima sun kebe dasu musaddiq suna tasu tattaunawar,har suka kammala ya dawo ta parlor din. Daga tsaye yake dubanta da lumsassun idanunsa,hannayensa cikin aljihun rigarsa. "Madame.....baa kammala bane?". "Saura kadan hamma" Agogo ya kalla sannan ya sauke dubansa. "Kubar addan nan ta huta mana.....da safe sai a qarasa" Dariya nadra da haneefa suka saki suna miqewa gami da tattare kayan da take dubawa,haneefa tace "Hamma babu ruwanmu fa,tun dazu mukace mata xamu qarasa gobe tace yau xaa gama.....saida safe" Ta shilla da dan qaramin gudunta tana bin bayan nadra da tuni ita ta fece. Ta dawo da idanunta daga kan haneefa tana murmushin wai auta itace yau da aure?,saiji tayi kawai anyi sama da ita. Wutsil wutsil ta fara yi da santala santalan qafafunta kamar qaramar yarinya. "Hamma......please mana,kada wani ya ganmu mana?". "Who cares?" Tunda taji ya fadi haka tasan zai wahala ya sauketa idan ba fita sukayi ba,don haka ta kwantar da kanta saman qirjin da duk duniya yafi mata ko ina dadi da samun cikakkiyar nutsuwa.