Sashe 194
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
ko yaushe ya zama available duk sanda aka kirashi. Ba jimawa ya iso,ya kuma bata dukka taimakon da zai bata aka samu ta dawo da qyar,saidai danci gaban da ake sanya ran samu komai ya dagule ya koma baya. Shi mamaki matar take bashi,ba abinda ta rasa na kulawa daga 'ya'yanta,jin dadin rayuwa iya jin dadi,amma taqi kwantar da hankalinta ta warke. Guri yasa aka basu daga shi sai ita,da zuciya daya yakeson mata fada wala'alla zataji. "Hajiya.....kiyiwa Allah ki rufawa kanki asiri kaman yadda Allah ya rufa miki......ko kinaso kikai kanki lahira ne?,kina sha'awar kwanan kabari da maqabarta?,wacce irin damuwa kike da ita haka a zuciyarki data hanaki sukuni?,anya ba ciwon hassada bane silar damuwarki?,to amma idan hassadar ce ma waye zaki yiwa ita?,mutum nawa kikafi a rayuwa amma ke baki gani ba?,to na rantse da Allah muddin baki sassautawa wannan zuciyar taki ba zakita shan wahala ne,ana aiki yana dawowa baya ba wani ci gaba" Ya fada cikin jin haushinta da takaicinta ya miqe yana barin parlor din bayan ya ajiye duka magungunan da zasu bata. Idanunta suna kan likitan har zuwa sanda ya kammala ficewa. Numfashi taja sosai tana saukeshi,wani bacin rai yana qoqarin taso mata amma tana danneshi. "Ba yanzu ba mariya......ba yanzu ba,ki danneshi don ki samu lafiya......ki danneshi don jikinki ya daidaita,akwai abubuwa da dama da kike buqatar aiwatarwa,lafiyarki kuma ita ce jagora,idan babu ita ba abinda zaki iyayi" Ta yarda da wannan sashen zuciyar dake mata wannan bayanin,ta aminta da abinda yake gaya mata. Maganganun likitan sun tsaye mata a rai,lallai ne baisan wacece ita ba.....baisan wacece mariya ba,wato kawai idan baka da lafiya sai abinda ka gani?,idan ba zaka iya yiwa kanka komai ba......idan ba zaka iya cewa komai ba kawai sai abinda ka gani?. Maganar da take nanatawa kanta kenan tana tuhumar wannan ciwon.....ciwon da yayi mata dirar mikiya a sanda ya kasance takun taqi kadanne tsakaninta da arziqinta,takun taqi kadanne tsakaninta da cikar burinta fa......to kuwa me zai hana su kasa fahimtar asiri akayi mata ba hawan jini bane. Duk inda ta juya ya waiwaya fuskokin yaran take gani,ba daman ta rufe idanunta sai taga yaran guda uku sak masu kama da fu'ad,ajiyar zuciya ta dinga saukewa tana jin wani razana yana kamata. Fu'ad ya riga daya samu magada,ko mutuwa yayi a yanzu ba a abinda mutuwarsa zata qara mata illa tsira da kaso daya bisa shida na dukiyarsa.......babban sake da kuskuren shine barin yaran suka iso duniya.....kuma duniyarma ta shaida. Ko sanda ta samu bacci yayi awon gaba da ita su ta dinga mafarki,a mafarkinma su shida suka koma,wani akan qafarta wani a bayanta,wani a zaune saman kanta,wani a gefenta haka dai,na saman kan nata ne ya sheqo mata kashi daya rufe fuskarta da jikinta gaba daya,abinda ya sakata farkawa kenan. Jikinta rawa yakeyi sosai,ta jiqe da gumi cikin tashin hankali,takai idanunta inda su sahura ke bacci,tanason tashinsu amma bata da wannan ikon. "Meye fassarar kashi a jiki?,anya ba ajalina aka haifo yaran nan suyi ba?" Ta tambayi kanta da kanta can qasan zuciyarta. Juya mafarkin taci gaba dayi da ma'anoni daban daban,hankalinta kuma yana sake tashi,har sanda Allah ya tashi sahurar ta dubata ta bata ruwa ta sake gyara mata kwanciya. Tanata kallon sahurar,tanaso ta tambayeta fassarar mafarkin kashi,amma ba bakin magana,haka ta maida idanunta ta kulle tana jin zuciyarta tana mata quna,tana Allah wadarai da rashin damar yin magana da bata dashi. "Mafarkin kashi fa arziqi ne....alheri ne" Wata zuciyar ta gaya mata tana tunasar da ita shekarun baya can sanda fu'ad yana yaro. Tasha yin wannna mafarkin a kanshi,duk sanda ta farka kuwa an yita tafka tsiya kenan ita da abbansu. "Ni wannan yaron bansan meye tattare dashi ba......kai baka da aiki saidai ayita mafarkin ka shafe jikinka da kashi koka shafeni?,inda Alla yake taimakona wankewa nake zuwa ni nayi a mafarkin ina dalili?,kai kuwa kaida Musaddiq duk yadda zan jaku ku wanke qi kukeyi.....kashi ai masifa ne qazanta ne". Tofa a ranar haka zata yita maganganu,hantara da kyara kuwa ranar fu'ad ya gamu dashi kenan har sai ya fita a gidan ya wuni a layi sannan hankalinta yake kwanciya. Ba fadan da abban baiyi mata ba amma bata ji ba,dole ya kawo idanu ya zuba mata,shi kuma bai taba gaya mata cewa ana tunanin arziqi bane. Abun ya tsaye mata akan jariran,tanason gasgatawa amma kuma tana qaryata hasashen nata.