Sashe 198
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Sannu a hankali kwanaki suka dinga tafiya,abubuwa da yawa sun lafa kuma sunyi sanyi,kaman darajar haihuwan yaran yazo musu da abubuwa ne masu yawa.
Amna da fannah harma da huda dukkaninsu goyon ciki sukeyi,amma hakan bai rage musu kwadayi ko sha'awar yaran ba. Babu wanda ke iya kwana biyu cikakke ba tare daya kira yaji lafiyar yaran ba. Farouq kuwa da aka jarabceshi da son takwararsa gidan ya zame masa kaman hanyar wucewa,sai aiki yayi mugun cude masa yake kwana uku bai shigo gidan yaga yaran nashi ba,ya kuma kebe takwaransa sunyi ganawa ta daban da sauran.
Ta bangaren maamah kuwa.....tun ranar daya kai mata yaran suka kasa bacewa daga idanu da kunnenta. Cikin awanni ashirin da hudu na yininta kowanne awa bata rufewa ba tare data tunasu ba. Sannu sannu sai takejin kamar tanason ta sake ganin yaran,kaman tana kewarsu,idan tana dakin bata da aiki sai kallon muhallin da ya kwantar dasu a waccan ranar. Wani abu takejin kamar yana shirin kamata me kama da hauka hauka akan yaran,tana yawan jin irin kukan da sukayi a waccar ranar,tana yawan jin muryoyinsu kaman suna wajen.
Daga qarshe dai ta fahimci son ganinsu takeyi,saita ta rasa kuma yadda zata fahimtar dasu saratu tanason ta sake ganin yaran,don iyasu kadai kawai takeson gani banda mahaifiyar tasu.
A hankali sabreen din cikin salo da hikima ta soma gyaran jikinta ta hannun dattijuwar matar nan da tasan jiya tasan yau kuma har gobe ake tafiya da ita wato Bgawos kitchen and aphrodisiac. Ingantattun kayan gyara natural na matan da suka jima a duniya kusan shekaru hamsin.08127084190/08104553105(tasan sirrin gyara sosai,gyara irin na dauri na tsaffin mata bana zamani ba,bana gama garin masu magungunan matan yanzu ba,bama gyaran kadai ba,hadda duk wani nau'in abinciccika,na biki ne suna taron sauka walima da sauransu,ko kuma kawai akwai ranar da zaki tashi bakya sha'awar shiga kitchen?,kinaso kuma abincin gidan ki ya zama ready a tsaftace kaman ke kika shiga kitchen din kikayi da kanki?,karki tsallake wannan).
A jikinta kawai taji canji me matuqar yawa,ta sake jinta tana sake kintsuwa tako ina. Har ta soma gyaran jiki ta watsar,don ta tsorata sosai ranar da fu'ad ya rutsata,da qyar tasha,amma daga qarshe ya gaya mata yana lissafe da satittikan da suka rage.
Tunani ta shiga sosai na yadda zata kubce masa,tanaso ta sake warkewa sosai,uwa uba kuma sunyi hira da fannah,har suka gangaro kan tsarin iyali.
"Muddin period dinki ya dawo to duk sanda kuka kasance tare xaki iya daukan wani cikin" Idanu sabreen ta waro waje.
"Ciki fannah......" Ta danyi dariya.
"Satinsu fauzan nawa?" Dariya fannah tayi.
"Shi ba ruwansa da satin yaranki nawa......indai har period ya dawo daidai shikenan magana ya qare"
"Fannan BB...." Sabreen ta fada tana cin serious.
"Adda sabreen" Ta amsa mata tana dariya qasa qasa.
"Kibar zancan nan tukunna......me zaki bani na gyara tsarabar bare bari" Gyara zama fannah tayi.
"Kamar kuwa kinsan mu bare bari ba wasa bane" Sai suka saki dariya a tare.
"Bari na gutsira miki kadan.....ki samu 'ya'yan habbatussauda da dabino ki dinga ki tsaga dabinon ki cire qwallon ki zuba yayan habba din ki dinga taunawa kullum safe da dare". Da daya da daya ta dinga bata sirrikan da na barebari ne,ita kanta ta qaru ta kuma sallama (sai damu wallahi
A tsorace take har zuwa sanda suka cika sati shida,ganin sun tsallake ranar baice mata komai ba,don washegari qaramar tafiya ta kamashi zuwa branch dinsa na lagos,don haka kawai tayi amfanin da wannan damar ta tayar da yawon arba'in.
Dabara tayi,ta kira anni tace mata tana son zuwa din,amma bata samu hamman ba,tunda tasan wani lokaci idan tafiya me muhimmanci wadda take ta gaggawa irin haka ta taso masa yakan saka layinsa a flight mode ne
"Yana da kyau ai,ko don a sake ganin 'yan uwa,zan gaya masa da kaina" .
Hankali kwance tahau shirinta,so samu ma ta wuce mali wajen mommanta,to amma mali din tasan tayi nisa ta tsallake zuwa can,don haka kawai saita shirya zuwa abuja gidan yayan ummeenta da bai jima da dawowa Nigeria ba,ta shirya su fauzan duka da masu aikinta,ta siya musu ticket suka wuce abinsu.
Sanda anni ta gaya masa harda 'yar mitarsa,yana tunanin cikin kano ne zasuyi ziyaransu gidan kawu rufai da gidansu da sauran wajen 'yan uwa su dawo gida su kwana.
"Anni kina ganin ba zata debowa yaran nan iska ba?,40 days fa kawai sukayi,nima kwana uku kawai zanyi fa na dawo,meye na fitan?" Ya kasa boyewa sai daya furta.
"Banda abinka fu'ad ai sada zumunci ne,kuma a al'ada ai dama ana yin wannan zagayen,kaman ba gajiya ne da kuma nunawa dangi lafiya kuke ne" Shuru ya danyi,dondai anni ce,yana kuma kunyar jayayya da ita.
"Shikenan,Allah ya kiyaye hanya"
"Ameen ameen" Anni ta amsashi suka dan sake tattaunawa sannan suka shiga wani maganan na daban.
_Yawon arba'in ko?....hmmmm
......._
_get ready muna pages din qarshe ne fa in sha Allah_