Sashe 200
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wani company.........mafarkina nakeso na cika na gina mana gida guda daya amma me gidaje sassa daban daban a ciki,wanda zai qunshi duk wani jinin jadda......ina mana sha'awar mu rayu tare yadda yaranmu zasu tashi da zumunci fiye da namu in sha Allah". Kai farouq ya jijjiga,sai ya maida file din ya rufe. "Wannan burina ne.....ni na tanadar mana wannan filin,bazan kuma bari ka rigani ba......kayi haquri ayi amfani da nawa" Kai fu'ad ya girgiza yana dage glass din motarsa "Is too late dude........saidai ka dauki wani abun daban........amma wannan kam na riga na gama dashi,already ma yau nayi requesting ma wani company daga china zasu zo su fidda komai yadda nakeso ya kasance......idan ka saka hannun ka ajjiye documents din a hannunka,saida safe" Ya fada duka a dunqule yana jan murfin motar ya rufe abinsa sannan ya tashi motar da gudu yana fita a gidan. Da kallo farouq ya bishi har ga bace masa,sai kawai ya jinjina kai yana maida dubansa ga file din,sannan ya fara takawa yana wucewa cikin gidan. Ko sanda yaje lagos baiyi baccin wahalar da yayi ba a daren. Lagos yasan baqon guri yake,gurin da ba iyalin nashi,amma anan gurin a yanzun yasan cikin gidanshi yake,saidai ya kasance shi daya,don haka tunda asuba ya lalubi pilot nashi yace ya nema musu izinin tashi zuwa abuja a yau din. Sai wajen bakwai na safe ya kirashi,a lokacin yana cikin gym,ya sauko daga saman machine din da yake kai ya dauki wayar yana duba kiran. Zama yayi yana goge gumin jikinsa da qaramin towel. "Sir......mun samu izini,amma qarfe biyu daidai na rana suka bayar" "Good.....hakan yayi,zan kasance a airport din one din in sha Allah" "Yes sir" Ya amsa masa suna ajiye wayar gaba dayansu. Cikin wani baqin lafiyayyen yadi me tsada da aka yiwa dinkin kaftan ya shirya. Hularsa zuwa takalminsa dukkaninsu gray color ne,sosai yayi wani wani irin azababben kyau,kalar baqin kayan saman farar fatarsa ta zama wani abun kallo na musamman. Haibarsa da kwarjininsa sun ninka na koda yaushe saboda rashin walwalar dake shimfide saman fuskarsa. S hi da saddiq kawai suka tafiyar,sai jordan daya zama kaman aljihunsa saboda jajircewarsa da kuma qwarewarsa a aikinsa da kuma kula dame gidan nasa. Kasancewar juma'a ce,sai daya tsaya central mosque sukayi sallan juma'a. Yadan samu delay kafin subar masallacin,har la'asar saboda a ranar ana wani taro a nan a buja daya shafi qasa,kuma manyan mutanen daya jima basu hadu ba suka tsareshi a wajen. Daya daga cikin drivers dinsa ne ya iso da daya daga cikin motocinsa dake ajjiye a katafaren mansion dinsa na nan abujan qirar Lamborghini. Kai tsaye jordan ya karbi driving din daga hannunsa suka qarasa zuwa cikin maitama. Plate number dake jikin motarsa kadai ya sanya me gadin bude musu qofa,Kai tsaye jordan ya qarasa parking space na gidan ya ajiye motar. Bai fita a motan ba,har sai da daya daga cikin ma'aikatan gidan ya sanar da safuura matar uncle din sabreen zuwan fu'ad din. Tana kitchen tana hada abincin daren me gidan,tuni ta saki girkin tana cewa. "Ku bude masa seating room maza akai masa drinks da abinci,me gidan baya kusa,bari nazo mu gaisa". Fu'ad sunanshi kirkinsa dama kamanninsa duka ba baqinsu bane,wannan ya sanya suke matuqar girmamashi da yadda kuma ya riqe sabreen dama 'yan uwanta da kyau,duk da ba gazawa sukayi wajen riqesu ba. Daidai lokacin fitowar sabreen kenan daga wanka bayan ta murje hadin dilka dana gyaran jiki da akayi mata,tun daga ranar da tazo mummy safuura ta soma gyarata ta ciki da waje. Idanunta kan babbar TV plasma dake maqale a bangon dakin tana kallon waqar dani kake kama. Sosai waqar ke shiga ranta da wani irin yanayi daya sanya zuciyarta tayi wani irin laushi,zuciyar kuma ta fada wani matsanancin kewa da begen mamallakinta wato muhammad fu'ad jadda. Ajiye towel din hannunta tayi ta taka zuwa gaban mirror tana duban wayarta dake ajiye a kai. Yawancin lokuta tunda tazo a kashe take barin wayar,saboda tana tsoron ya kirata yaji inda take yace ta dawo gida. Tanason tadan sake samun lokaci kadan,duk da tayi kewar komai daya shafesa kewa bana wasa ba,amma a yau din sai take jin haqurinta ya gaza,koda muryarsa tana da buqatar taji. Kunna wayar tayi sannan ta zuba numbers dinsa da tuni ta jima da haddacesu,kiran ya fara gangarawa yana shiga wayarsa dake hannunsa a daidai wannan lokacin da suke gaisawa da mummy safuura. Fuskar wayar kawai ya kalla,yadan zubawa kiran idanu yana mamakin ya akayi ta kirashi a daidai irin wannan lokacin?. Yasan tabbas batasan yazo ba,don ga mummy din a zaune a gabansu ballantana yayi tunanin itace data shiga ciki ta gaya mata. Kife fuskar wayar yayi,har ta gama rurinta ta katse ba tare ma daya sani ba. Da dan mamaki ta sake daukan wayar tana sake kira,ta saka a handsfree ta ajiye tana jin yadda bugun zuciyarta ke daduwa. Still bai daga ba,abinda bai taba faruwa ba kenan a tsakaninsu. Komai yawan aiki ko uzurin dake gabansa kiranta na dabanne,to amma batasan wanne irin aiki ya samu da yawa haka a lagos din ba,don haka sai ta ajiye wayar ta miqe da nufin shiryawa,idanunta kan su fauzan dake bacci dukkaninsu su ukun abinsu. Tana bude luggage dinta hamra diyar mummy safuura ta tura qofar dakin da sallama ta shigo. "A tashi HAMFAAL(hamza/farouq/almustapha)". A marairaice Sabrina ta dakata da daukan kayan da take shirin yi ta dubi hamra,don tunda taji tace hamfaal to dukkaninsu take nufi. "Amma dai antynsu fawad ayimin rai don Allah......ina shirin karance littafin girke girken nan yau duka gaba dayanshi zaki jiqamin aiki?" Dariya sosai hamra tayi,don ita sam bata ma qaunar yaran suyi bacci. Bata gajiya da rainonsu,zuwansu ne yasa ta fara jin gidan nasu a mazaunin gida sosai. "Ayyah.....yau ba laifina bane......daddynsu ne yazo ganinsu". Dum!,taji qirjinta ya buga,gabanta yayi wani wawar faduwa,tsoro kuma taji ya saukar mata. Ta fidda idanu waje tana tambayar hamra. " Please hamra......banason wasa" "Serious adda......yana seating room,yanzun suka gama gaisawa da mummy" Ta fadi tana takowa ciki saboda shigowar me aikinsu da zata tayata daukan yaran. "Gasunan.......ga abun daukansu can" Sabreen ta fadi tana nuna mata tattausan abun daukan guda uku farare qal dake ajiye a gefe. Tsaf suka nadesu suka fice dasu,saita bisu da kallo har suka bacewa ganinta sannan ta maido dubanta cikin dakin tana sauke nannauyan ajiyan zuciya. Tsoron yadda zata tunkareshi takeji sosai,amma dole haka ta qarfafa gwiwarta ta som shiryawa cikin mutuwar jiki da rashin kasala. Dukkanin yaran ya aza saman qirjinsa ya rungumesu yana shaqar daddadan qamshinsu daya cakude dana mamarsu da yake iya jiyowa cikin jikkunansu (Shi yasa wannan yake zama babban abun kaico ga macen da take jego amma wai don wani kayan takaici da baqinciki ka rasa qamshi a jikinta,to wannan qarnin da qarin da kikeyi haka jikin yaronki zai zama,kada kiji haushi kada kuma kiyi mamaki idan kikaga yaronki sam baida farinjini duk da kuwa kyakkyawa ne,hakanan kada kiyi mamakin ganin ana rububin daukan yaron wata kuma bayan baikai yaronki kyau ko saka sutura me tsada ba,don Allah mu kula da wannan,qamshi rahama ne,koda kuwa iya keda hancinki ne ma 'yar uwa Bugawar zuciyarsa ya canza sosai daga dumin yaran kawai,sai a lokacin ya sake fahimtar yayi kewarsu bata wasa ba. Ajiyar zuciya a jejjere ya dinga saki kafin daga bisani ya saukosu. Saddiq ya karbi abbanshi hamza. Da fuskarsa da tasu ya manne guri guda,ya basu tattausan kiss a goshinsu. Cikin wani tattausan milk material ta shirya,tayi wani irin sassanyan kyau,jikinta na fitar da tattausan qamshin nan nata na incense by kabo daughter da yafi qauna. Glowing kawai skin dinta yakeyi na masu danyan jego,ga cikakken hutu ga kuma gyara da takesha,wanda hatta da abun shanta mummy safuura na daban take bata na gyaran mata. Kanta ba dankwali sai qaramin mayafin material din data yafa saman kan nata,wannan ya bawa sumar kanta me sulbi daman fitowa ta gaban goshinta. A parlor ta samu mummy safuura,saita nuna mata wani kyakkyawan glass bowl me murfi "Dauki wannan ki tafi masa dashi......." "To" Kawai tace da mummy a sanyaye. Tun daga qofar setting room din ta lura ba alamun takalmin mutum ko daya,saidai duk da haka bata kawo komai a ranta ba ta taka a hankali ta shiga parlor din. Wayam ba kowa cikin setting room din,sai tattausan mayataccen qamshin nan nasa. Bugawa zuciyarta ta dinga yi d'ai da d'ai d'ai,indai batayi kuskure ba a nan din hamra ta fadi mata an saukesu,to amma ina suka shiga?. Mugun sanyi jikinta yayi,tayi taku biyu tana isa saman daya daga cikin kujerun ta zauna sannan ta ajiye bowl din hannunta. Wayarta data fito da ita ta zaro ta soma kiran mummy safuura. Bugu biyu ta dauka "Ya akayi sabreen?". " Mummy.....banga kowa a seating room din ba.....ba kowa" Ta qarasa fada a sanyaye. "Kaman yaaya?,yanzun hamra ta baro parlor din fa" Mummy safuura ta fadi da dan mamaki a muryarta. "Alla ba kowa mummy" Ta sake fada tana dora tafin hannunta saman goshinta,tsoro yana kai kawo a zuciyarta bayan wani hasashe da zuciyarta tayi mata. "Bari ina zuwa" Mummy ta fadi tana cike da kokwanton abinda sabreen ta fada. Wayar ta ajiye,tana shirin miqewa daya daga cikin yaran gidan ya shigo. Fuskarsa washe da madaukakiyar fara'a,hannunsa riqe da rafas na dubu daya sabbi kar a miqe. "Mummy.....baqonku ya tafi.......yace a baki haquri sauri yake,lokacin tashin jirginsu yana dab da qwacewa,yana gaidaki da kyau,ya mana kyakkyawar sallama,yau duka mu masu aikinki muna cikin alheri dumu dumu,yace a baki wannan" Ya fada yana miqa mata envelope din dake daya hannun nashi. "Waya bawa yaran ya dawo dasu?" Ta tambayeshi tana miqa hannunta. "Gaskiya dasu naga sun fita......ba da mamarsu suka tafi ba?" Batasan amsar da zata bashi ba,sai kawai tace dashi "Madalla.....ka dubamin idan uba ya gama wanke motarnan" Ta fada tana karbar envelope din. Budeta tayi a hankali,saiga sabbin dollars a ciki miqaqqu. Ido tadan fitar cikin mamaki,me yasa sam mutumin nan bai iya qaramar kyauta ba?. Komawa tayi ta zauna tana ajiye envelope din a gefanta,mamaki yana cikata. Ya zaiyi da yaran daya tafi dasu?,bai tsaya koda ganin mamansu ba?,bai kuma gaya mata zaije dasu ba?,kada dai ya zamana sabreen yaji tayi ita ta amsheta bata sani ba,ko kuma wasa takeyi da aurenta?. Kai tsaye