← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 206 OF 215

Sashe 206

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Cikin lokacin wani kulawa yake bata data ninka ta baya,yana gida ko yana office dukka yana kula da motsinta. Ya sake qaro mata aminttatun masu aiki da suka sanya komai ya sake zame mata da sauqi,goyon ciki me 'yanci,kuma Allah ya bata da sassauci akan nasu fauzan,duk da cewa har a lokacin tana shayar da yaran,yace bai yarda ta yaye masa yara ba,idanma biyanta ne shi zaiyi a barsu susha nono su qoshi ko don saboda ginuwar kwanyarsu yadda akeso.
To shi ciki dai d'an duma ne inji hausawa,a hankali jikinta da dabi'unta suka fara nunata,duk da yadda take gocewa shiga cikin mutane don kada su fahimci cikin. Kunyar cikin take sosai,sau tari idan shagwabarta ta motsa sai tayita masa rigimar banza akai.
"Hamma don Allah kada ka gayawa kowa.....don Allah hamma kada ka fada,yayi wuri fa hamma.......duka duka watansu fawad nawa ne?,Allah kunya nakeji"
"Sabrrrr" Ya kirata kai tsaye a lokacin tana saman cinyarsa yana raba mata doguwar sumarta biyu hagu da dama don ta dameta.
"Wallahi wallahi ko cikin shege nayi miki bazan boye samuwarsa ba.....kuma zanso abina fiye da tunaninki,ballantana 'ya'yan halaliya 'ya'yan so". Yadda yace 'ya'yan so din har tsakiyar zuciyarta,tun daga ranar saita daina cewa komai akai,ta kuma tayashi da duk yadda yakeso.
Tasha tsokana sosai wajen fannah wadda itama nata cikin ya fara girma,amna da huda kuwa dukkaninsu yaya take a Wajensu,ba tsokana sai gulmarta a boye,uwa uba suma duk ta kansu sukeyi don cikinsu ya tsufa sosai.
Wata tara da bikinsu amna amna din ta dire nata yaron namiji. Maamah bata sanu ba sai bayan kwanaki bakwai,tana zaune saman wheelchair dinta sanda musaddiq ya ajiye mata goro da alewar radin suna. Hamza ya saka shima still saboda nuna yabawa bisa hidimar abban a kansu,sun masa laqabi da HILAL. Ba wani feeling data samu zuciyarta a ciki akan haihuwar,so ko qi itama bata san wanne layi take kai ba,saidai bata wani dorawa kanta tsananin tunani akan komai ba ta ajiye maganan,duk da lokaci lokaci idan aka kawo mata su fauzan yaron yana fado mata a rai.
Tsakaninsu da huda wata biyu kacal itama ta dire nata sojan. Saddiq ya nuna kara sosai,ya sanya masa sunan mahaifinsu sabreen wato ahmad,suna masa alkunya da NASEEM.
Ta kowacce fuska anni jinta take cikin alkhairin ubangiji,saidai a yanzun kwadayinta a samu 'yanmata kuma,don tana fatan samun garabasar nan na wanda ya raini diya mace biyu ya aurar dasu na alqawarin aljanna kai tsaye.
Irin girman da nauyin cikin ya sanya fu'ad wucewa da ita a wata tafiya da yayi zuwa spain ya tafi da ita. Bawai don yana da nufin tayi anti natal nata a can ba,saidon kawai a duba mishi ita duk da bata da matsalan komai,saina wani irin cin abinci da takeyi,abinda shi kuma yakeyi masa dadi sosai,har yakan zauna yana kallonta abinsa.
Scan din farko ya nuna twins ne a cikin nata. Wani iri ya dinga ji,tsoron Allahnsa yana sake kamashi. Dukka cikin addu'arsa ba wadda bai gani ta tabbata ba.....shin cikin ni'imomin Allah wanne ne a ciki zaiyi inkari?.
_Allah ka wadatamu da dukka ni'imominka na zahiri dana badini,ya Allah karka jarabcemu da gushewar ni'imominka a kanmu_
_on our way to the last episode's in sha Allah_
Tattalinta ya dinga yi,nan nan da ita yakeyi,baya yarda komai ya taba walwalarta ko kuma jin dadinta.
Duk wani abu da yasan zata iya buqata ya ajiyeshi......komai da yasan zata iya nema kafin ma takai ga tambaya ya tabbatar da samuwarsa.
Bata aikin komai,ba aikin fari bare na baqi,komai nata dana yara tana da amintattun masu aikin da take jinsu kaman 'yan uwanta na jini,musamman da suka kasance kusan dukkaninsu marayu ne wadanda basu watsar da maraicinsu ba.
Duk wannan gatan data samu.....duk wannan kulawar bata sanya ta saki hidimarsa ki qwaya daya ba. Yayi yayi ta barshi amma ita kanta tasan ba abu bane me yiwuwa tabar kula da mijinta,sai ya qyaleta a bisa dole,amma duk wani motsi nata da zatayi shike tayata,shike kama mata. Misali wani lokacin yakan yi mata wayo ya rigata tashi da safe. A kitchen din sama zai hada breakfast abinsa ya aje mata nata,ya hada ruwan wankanshi da kanshi yayi,ya watsa undies dinsu cikin washing machine ya wanke musu,ya kwashe komai dake tsananin parlor zuwa Bedroom din da suka bata. Idan ta farka saidai ta taras da sauran aikin,wanda baya wuce shayar dasu fauzan da kuma qarasa kintsa saman nasa,sai tayi wanka shikenan ta zauna cikin masu aikinta.
Idan ta gaji tana buqatar fita shike katse komai nasa ya dawo ya fita da ita,idan ma qasar ko garin takeso su danyi balaguro daukanta yake ita da duk wanda takeso su wuce suyi iya kwanakin da takeso.
Irin gatan da yake gwada mata saita dinga jin kaman ya mata yawa,kaman bata cancanci tattali irin haka,ranar data fara magana a kai suna tsaye ne saman balcony na wani qawataccen madaidaicin gida daya siya a dubai a satin. Gidan yana area me tsada ne wanda yake da clear view na garin dubai da guraren kallo masu kyau.
Ta baya ya rungumeta yana dora hannunsa guda daya saman qaton cikinta. Ta miqa hannunta ta bayan itama ta shafo sajensa tana sakin murmushi.
"Tunanina kike?" Ya furta a tausashe,saita gyada masa kanta.
"Ya akayi kasan sirrin zuciyata".
"Ruhi daya......zuciya daya.....qwaqwalwa daya.....gangar jikince kawai guda biyu,to menene zai boye a wajena?" Ya qarasa maganar yana tura mata wani file ta gefan cikinta. Murmushi ta saki tana jin maganarsa ba wani kuskure ko gyara a ciki,ta karbi file din ta bude.
Takardar shaidar mallaka ce ta wannan gidan da suke ciki,wanda ya rubuta da sanya hannunsa da komai kan ya mallaka mata gidan. Ganin komai take kamar a mafarki,batasan adadin gidaje da estate nawa ya mallaka mata ba.......amma wannan ya zama na daban. Mallakar gida sukutum da guda a dubai?,abun sai kanta ya kasa dauka,don a satin a gabanta ya bada izinin tura Dirham's masu nauyin gaske ga kamfanin da sukayi cinikayyar gidan.
A nutse ta juyo suna fuskantar juna,hannunta yayi sanyi sosai ta riqe nasa hannun.
"Hamma.......wannan kyautar tayi girma da yawa,wannan gatan yayi yawa". Sassanyan murmushin nan nasa ya saki,ya kama qugunta ya riqe yana mata wani tattausan kallo kaman zai hadiyeta.
"Me akayi ma my world?,wannan gidan wai?,kinsan gidaje na nawa a qasar nan?,wannan din kuma dama tun asali saboda ke aka siyeshi.......sabreen" Ya kirata da wani sound yana kama fuskantarta cikin hannunsa.
"Na'am muffin" Ta amsa masa idanunta suna cika da hawayen farinciki.
"Komai na fu'ad naki ne.....komai na muhammad jadda kin cancanceshi.........gata kuma ban nuna miki komai ba sabrrrr.......bana buqatar komai a wajenki illa ki cikamin gida da yara......ki cikamin gida da zuri'ar da zasu zamemin ababen alfahari.....haihuwa nakeso kiyita yi......ni kuma nayi alqawarin bazan barki kisha wahalar komai ba banda ta basu tarbiyya". Rungumeshi ta matso zatayi amma cikin jikinta ya tokaresu,sai taja baya kadan,yana dariya ya nuna cikin da yatsarsa,sannan ya juyata yana baga kyakkyawar runguma ta baya.
Chapter 206 · 0% Book details