← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 208 OF 215

Sashe 208

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

JADDA'S VILLA shine sunan dake rubuce b'aro b'aro daga tsororuwa babban ginin gidan. Rubutun an yishi ne da ruwan GOLD jikin wani qawataccen allon qarfe da aka yiwa wani irin design me azabar kyau da daukan hankali. Wani irin shimfideden gida ne,wanda a qalla ya qunshi maka makan mansions a cikinsa guda shida. Kusan komai na gidajen iri daya ne,saidai banbancin girma da wani gidan yafi wani yawan dakuna da kuma qawatuwa da kayan alatu na rayuwa,daidai da yadda mamallakan gidan suke da buqata. Idan ka kira JADDA VILLA da aljannar duniya sam sam bakayi laifi ba,don inda akwai sunan da yafi haka nuna tsananin tsari da cikar suffa da haibar gida ya cancanci ka bashi. Gidane daya mamaye jadda street gaba daya daga hannun dama,sai hannun hagun dake dauke da qawatattun gidajen hamshaqai masu fada aji cikin unguwar da sai ka isa wane zaka mallaki gida a cikinta cikin birnin tarayyar abuja. Ba gidan kawai ba,unguwar kanta sai kabi matakai daya bayan daya kafin ka samu nasarar shigarta,bayan kuma ka shiga din zai zame maka barazana hanyar shiga JADDA VILLA. Birnin da ya shiga bakunan manyan masu kudin da suke ganin wuyansu yayi kauri a duniyar naira.....birnin daya girgiza zukatan al'umma da dama ciki harda manya manyan masu kudi na qasata dama qasashen duniya gaba daya. Manyan gate gate guda biyu da matsakaici guda daya dukka saika wucesu kafin kakai ga shiga BIRNIN JADDA kaman yadda aka rubuta daga cikin gidan gate din farko. Daga can cikin daya daga cikin gidajen dake cikin jaddas villa din,cikin tsakiyar wani qawataccen courtyard da aka shimfida hikima wajen gini da tsarinsa. Qawatattun shuke shuke ne masu dauke da mabanbantan furanni masu launikan dake kiran butterflies zuwa garesu,daga qarqashin shukokin wata 'yar qwarya qwaryar qorama ce ta zamani da aka qirqireta saboda wucewar wani ruwa me tsananin hasken da kake iya hangen wasu irin mulmulallun stones masu daraja da tsada dake zuwa a oval shape,amma suna da nau'in kaloli daban daban,kaman yadda madaidaita da qananun kifayen dake yawo a ciki suke da wadannan launikan. Wasu irin Kujeru ne sirara masu taushi aka qawata courtyard din dashi,wadanda suke farare qal,kaman ba'a tsoron kai kawon yaran da gidajen suka mallaka,yaran da suka tasamma rai ashirin da shida. Zafin rana ko sanyi duka basa rabar wajen,guri ne na musamman da kowanne gida daka cikin gidajen jadda villa aka tanadar dashi bisa tsari na musamman dake iya daidait weather na wajen. Idan zafi ne weather wajen na fidda iska me kyau da dadi,idan sanyi ne weather din wajen na bada temperature da zata dace da yanayin da mutum yakeso. Saman daya daga cikin kujerun dattijuwa anni ce,sanye da wata sassauqar riga mara nauyi ruwan madara,wadda take hade da hijabinta asalin saqar qasar Indonesia. Daga gabanta kuwa yara ne matasa maza da mata kusan guda biyar,masu kamanceceniya da juna,wasu kamanninsu sun fita sosai......wasu kuma kamanni ne na baya baya. Daga gefan daman annin wasu yara ne guda biyu da duka duka shekarunsu ba zasu haura takwas da tara ba,dukkansu share hawaye sukeyi fararen fuskokinsu sunyi jajur. "Kowa ya gama bayaninsa?"ta fada tana duban fuskokin su daya bayan daya. Da fari gurin shiru ya dauka kafin daga bi sani,ta sake bin fuskokinsu da kallo tana sake maimaita tambayarta. Kai suka gyada daya bayan daya. "Da kyau" Ta fada cikin cikakkiyar nutsuwarta dinnan tana ajiye littafin hallul masa'eel dake hannunta a gefe. "Ameen" Ta kira sunansa kai tsaye. Yaro da yaci sunan muhammadun ta hanyar fadin gaskiya akan komai da aka tambayeshi,koda hakan zai ja masa duka......yaron da kusan halayensu suke kamanni iri daya dana MUHAMMAD SAUBAN(Ku ajiye wannan sunan a next novel nawa idan rai yakai mana ). Sauban din da shike binsu muhammad ameen da ahmad amaan.......amma halayensa sak irin na mahaifinsa......halayensa sak irin na ameen......shekarunsa duka duka basu wuce goma sha biyu ba......amma wani irin girma da dattako gareshi. "Me ya faru ameen?" Anni ya qarasa tambayarta. Bayani yayi mata na iya abinda ya sani,ya qara da cewa. "Amma a gaban sauban akayi.....ki tambayeshi". A nutse ta waiwaya ga sauban din,wanda yake zaune shi daya saman kujerar da babu kowa kusa dashi. Ita kanta kujerar tayi dan nesa kadan dasu,kunnuwansa manne da headphones wanda ko daga nan kana iya jin sautin qira'ar qur'ani na fitaccen shaik dinnan wato maheer almu'aiqaly. Duk wanda yasan sauban ya sanshi da yawan sauraren karatun shaik maheer duk sanda yake kebe shi kadai,wannan ne anni take kyautata zaton sanyashi ya zama na daban cikin 'yan uwansa......hasken alqur'ani kuma take tunanin ya qara sanyashi me tsananin nutsuwa,duk da tarin zuciya da yaron yake dashi. "Sauban" Ta kirashi tana yafitoshi da hannu. Kallo daya ya yiwa annin ya saka hannunsa ya cire headphones dinsa sannan ya taso ya qaraso wajen *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 __________________________ *_NACE BA......._* *_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._* *_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_* *_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada munga ingancinsa_* *_Da yardar Allah saikin godemin_* *_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR GASKIYA KENAN AHTO_* Golden oud Hawi Sandal balls Sandal flakes Cotton bakhoor Kabbasine mix Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk) Deep crush (luxury khumra). Signature oil Kuleccham Kabbasine spray *_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_* *_PRIME SCENTS(the scents of royalty_* *KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN HANKALI* *SUNA NAN A* *_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road kano_* *BA'A KANO KIKE BA?* *_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a duk inda kike cikin aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_* *DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE* wa.me/+2348103155915 KO KI KIRATA TA NAN 08103155915 _Zafafabiyar_ 172 *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX "Me ya hada arham da ahsan?". A nutse ya zube kyawawan idanunsa masu girma kaman na mamanshi akan dukkaninsu,sai ya matsa a hankali ya zauna gefen anni. Baiji tsoron idanun kowa ba ya zauna ya yiwa anni bayani filla filla har yakai qarshe. " Haka akayi?" Ta sake tambaya,dukka wajen ba wanda ya musa banda hilal da yayi shuru. Maida dubanta tayi ga hilal. "Allah yana cewa cikin qur'aninsa,yaku wadanda kuka bada imani da Allah.....idan fasiqi(mutum)yazo muku da labari,to kuyi bincike,gudun kada ku afkawa wasu mutane bisa jahilci(rashin sani dalilin rashin bincikenku).saiku wayi gari kuna masu nadama.......a duk sanda wani mutum yazo maka da labarin anyimin kaza,ko wane yayi maka kaza,ko kaza ya faru,dole ne akan musulmi ya nemi hujja ko dalili na abunnan ya faru,dole ne......muna da wata dabi'a ta saurin yanke hukunci,da daukan zance daga bakin mutumin daya fara zuwa mana da labarin wane yayimin kaza,wane ya batamin ko yayimin ba daidai ba.....nan da nan wannan daya fara zuwa da labarin saimu dauka shine me gaskiya,bisa jahilci irin namu na neman jin ba'asi daga bakin wani sashen,wanda muddin zaka kasance mutum irin wannan a rayuwarka,za'a yita sanyaka batawa da mutane masu daraja da kirki.....zaka yita fada da mutanen da basuyi maka komai ba.....za'a sanyaka ka yita yanke alaqa da mutanen da alaqarku keda matuqar amfani a duniyarku da lahirarku.......wannan ba halin musulmi na kirki bane a matsayinka na babba hilal.....ba kuma dabi'ar qwarai bace.....ba dattako sam a cikin ta,dukkaninku daga yau na horeku da zama masu bincike". "In sha Allah anni" Ya fada yana saukar da kansa qasa. Waiwayawa tayi ga yara biyun dake gefe tana dubansu. "Faarees da ra'ess ya tabbata kunyi qarya.....ku bawa Aadeel haquri,sakamakon qaryarku kuma wannan satin gaba daya kada naga uniform dinku a wash room,da kanku zaku wankesu duka satin nan.....sannan idan ummenku ta dawo......kune na qarshen zabar tsaraba har sai kowa ya dauka nashi" Ta fada tana nunasu da yatsa. Haqurin data buqata suka juya suna bawa wanda ake kira da Aadeel din haquri,ta kallesu daya bayan daya still tana cewa. "Ku kyautatawa junanku......kyakkyawar mu'amala itace mutum......girmankai na shashasha ne maras wayo.....hassada ta maras rabo ce,don tana cinye kyawawan ayyuka kaman yadda wuta takejin yayi.......shi kuwa sharri dan aike ne,daga inda aka aikashi duk daren dadewa nan zai dawo......alkhairi kuma danqo ne baya faduwa qasa banza.......komai dadewa ka shuka alkhairi shi zaka girba,kaman yadda komai dadewa idan ka shuka sharri cuta ko ha'ince sai ka girbeshi.....kyakkyawar dabi'a jari ce da babu kamarta,wadda duk dukiyar gidanku bata isa ta siya maka ita ba......hakanan duk talaucin gidanku idan ka sameta kaiba talaka bane har gaba da abada". Ire iren kalmomin kaka ta gari kenan a duk wani zama da zai hadata da yaran,bakinta sam sam baya gajiya da furta wadannan kalmomin a kansu,har sun fara haddacesu tun basusan ma'anarsu ba,zuwa yanzu kuma wadanda suka fara girma a cikinsu sun haddacesu tas a kansu. Basu fita a wajen ba saida kowa ya gaisa da kowa,kowa ya koma yanayinsa na dazun sannan. A sanda suke fita a lokacin sauban ya koma inda ya taso,ya maida headphone dinsa saman kansa yayi playing karatun yana ci gaba da ji hadi da lumshe ido. Kammaninsa da dabi'unsa kamar babansa,duk wani harka ta hayaniya ko fada babu shi a ciki,kaman ya yiwa kansa rigakafi daga fushi da zuciyar da yasan yana da ita. Dauke kanta anni tayi daga inda yake murmushi yana subuce mata. Tana ji a jikinta anya sauban din ba shine wannan HASKEN da take gani tsakanin iyalinta ba?,wannan mai riqon addinin ma'abocin cikakken ilimi daya haura na saura?. "Allah kayi mana zabi da mafita mafi alkhairi" Ta fada a nutse tana jawo hallul masa'il dinta tana dubawa. Tsaiwa Amaan yayi yana hango abokin tagwaitakarsa wato muhammad ameen dake fitowa daga sassansu. Sanye da fararen kayan da aka yiwa ratsin baqi sak irin kayan dake jikin Amaan din. Shima gunsa ya nufo kai tsaye yana dubansa. "Abbee fa ya shigo yanxun......kuma naga ya shirya.....ina kuma kyautata zaton ummee zaije daukowa daga airport......na tabbatar dukkaninsu sun manta da yaune wedding anniversary dinsu,15yrs" Ameen ya qarasa fada da faffadan murmushi daya qara masa kyau,yana kuma d'age dukka girarsa sama. "Na tuna......akwai wani abu ne?" "Yes" Ameen ya fada ya fada yana dariya. "Ya kamata muyi wani abu,yadda naga abbee yana wani shiryawa yanata duba mirror kaman wani dan saurayi,dolen saiya burge duniyarshi". Dariya suka saki lokaci daya,amaan yace. "Babu
Chapter 208 · 0% Book details