← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 149 OF 215

Sashe 149

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da yadda yake iqirarin nashi yafi nata. "Kina tantama ko?" Ya tambayeta da murmushi,kafin wani ya sake cewa komai a cikinsu an sake shigowa. Anni ce da musaddiq saddiq abba da farouq gaba daya,kunya ta lullubeta,tayi qasa da kanta tana niyyar tashi a wajen anni tace "Yi zamanki" Suka koma saman ragowar sofas din dake dakin suka zauna. Duk budurinnan gogan idanunsa yana kanta bai iya dauke idanunsa ba sam sam. Sabuwar gaisuwa da jaje suka sake yiwa juna,dakin yayi shuru sanda farouq yake bada labarin yadda abun ya kasance. "Kaman gawa mukazo dashi abba......dazu da safe ya farka......amma ko jiya da daddare bayan an gama wasu test likitan ya sake jaddada mana abinda suka shaqa masan guba ce me qarfi....kuma idan ya wuce yau bai farka ba ICU zasu maidashi.....cikin hukuncin Allah sai gashi ya farka da yake yaji a jikinsa duniyarsa tana hanyar zuwa gareshi". Kunya sosai ta sake kama sabreen,tayi qas da kanta tana jan mayafinta. Abba da annin duka dariya kawai sukayi,saddiq ya bude abincin da sukayi takeaway da complete set da plate da spoons ya soma zubawa kowa ma'u tana tayashi. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ 128 *_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_* *_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_* *_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_* *_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_* *_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_* *_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_* *_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_* *_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_* *_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_* *_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_* *_HAIHUWA KIKAYI?_* *_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_* *_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_* _Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_ 08104553105 08127084190 *_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_* *_BGAWO'S KITCHEN_* *MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU* ___________________________ 128 ma'u tana tayashi. Parlor abba ya fita don amsa waya,sai sukaci gaba da tattaunawa a tsakaninsu. Zukata sunyi sanyi sun kuma samu nutsuwa daidai gwargwado,sauran abinda ke cikinsu bashi da yawa,godiya kawai sukema Allah daya tsallakar dasu daga fuskantar wannan bala'in. Idanunsa yake saukewa a kansu,kowa cikin walwala yake da farincikin samun kubutarsa.....kowa kuma a cikinsu soyayya da qauna ce irin ta fil'azal tsakaninsu,amma abu guda dake taba zuciyarsa shine sam ba MAAMAH ba dalilinta. Maman daya kamata itace a gaba kafin kowa?,maman daya dace a bisa mizani na hankali dacewa da kamata ace itace damuwarta ta dara ta kowa.....ta d'ara ta babarsa anni.....ta d'ara ta 'yan uwansa,ta kuma d'ara ta matarsa......saidai sabanin hakan maamah din itace halittar da tafi kowacce halitta rashin damuwa da yanayin nasa,sai ya maida idonsa ya rufe yana jin wannan zafin har tsakiyar zuciyarsa. Saddiq ya gama da kowa farouq ya dubi musaddi "Zubawa dude ka bashi ko kadanne ko zai karba". Harara fu'ad ya zubawa farouq,yaso ace su anni basu wajen da ya bashi amsa daidai dashi. Idanunsa ya juya a hankali inda sabreen ke zaune tana juya zoben dake yatsanta,don ita ba kowanne abinci take iya ci ba. "Ke ba zakici abincin ba?" Ya fadi da wata murya can qasa yana mata kallon qurilla. Sau daya ta dago kai ta kalleshi ta mayar qasa tana ci gaba da juya zoben hannun nata. "Na qoshi". Motsawa yayi kadan yana son gyara zamanshi. "Zubo kizo nan" Ya sake fada ba tare daya dubi inda anni take ba. "Yauwa....gwara ka tilastata taci,ko ba yawa aizai zauna,ta yaya kina da lalura amma cin abinci ya zama yaqi ameenatu?". Idanunsa ya sake maidawa kanta,sunan ameenatu yana masa dadi sosai,idan ya kalli fuskarta yakuma ambaci sunan sai yaji tayi bala'in dacewa da sunan,musamman idan ya tuna tarihin asalin me sunan. A kunyace ta miqe,ta zuba komai dan kadan kadan sannan ta dawo. "Zauna a nan" Ya nuna mata gefansa. Dan satar kallon anni tayi kafin ta zauna din tana bada tazara kadan tsakaninsu sannan ta ajiye plate din a tsakiyarsu. Spoon ta zura masa a ciki ta kalleshi,sai ya langabe kai yana bata fuska. "Bazan iya ci ba.....aikinsan bani da lafiya ko?" Sai kuma yayi qasa qasa da muryarsa yana satar kallon farouq. "Idan kuma so kike farouq yayi mana dariya ya yadda da gaske ba zaki iya bani kulawa ba to". "Anni muffin.....anni a gurin" "Kada ki damu,ita hirartama take dasu saddiq,ita kanta zatafison taga kina kula dani......oya bani abinci" Ya fada yana lumshe idanu saboda yadda yakejin wani yanayi yana ratsashi. A d'arare ta debo abincin ta taho dashi bakinsa,sai ya kauda kai yana kallonta. "Eat first" Ya fadi yana tsareta da ido. Fuska ta bata,batasan ta shagwabe masa ba tace "Hamma.....bazan iya ci ba". "Zaki iya.....zakici in sha Allah,kada kiji tsoro" Ya bata tabbaci yana kallonta. Da kadan da kadan ta dinga miqa cokalin bakinta har ta juye abincin,ta soma taunawa tana rolling idanunta cikin tsoron kada amai ya biyo baya,sai taji zuciyarta ko cikinta basu wani hautsine ko juya ba yadda suka saba ta hadiyeshi tsaf. "Good girl.....am next" Ya fada yana gyaran zamanshi. Debowa tayi ta miqa masa,ya bude baki ya amshe kaman qaramin yaro. "Hmmmm........dadin abincin daya fito daga hannunki daban yake......ban taba jin abincin da yayi dadin wannan ba......Allah ya qarawa hannuwanki da rayuwarki albarka". Ya fada yana lumshe ido a kanta. "Ameen" Ta amsa tana sadda kai tana satar kallon dakin. Wayam ta gani,ba wanda ta samu a dakin duka sun fice ba tare da tasan sanda suka fice ba,saita dawo da dubanta kan fuskarsa idanunta a warwaje. Dariya me qaramin sauti ya saki "Sun gudu......they can't wait to see" Fuska ta tabe ta kyabe baki kaman zata saki kuka "Kaga irinta ko?" "Wayyo Allah hannuna" Ya fada shima yana karyar dakai gami da riqe hannun da daya hannun. Tuni ta watsar da komai tayi wajen tana riqe masa a rude. "Sannu.....da zafi ko?,fama maka nayi?,yi haquri.....ko a kira Doctor" Yadda ta fadi doctor din sai labbanta suka masa wani mugun kyau. Lallausan kiss ya saukar mata saman lips din yana dariyar yadda ya cita wasan,ya samu hanya mafi sauqi na sake kusantar da kanshi da ita. Sai kusan dare can sosai sannan su anni sukayi niyyar wucewa masaukinsu. Ya tsareta da ido ganin tana hada jakarta da tarkacenta,a ransa yakejin muddin tace zata wuce tabi su anni saidai su tafi tare,don kuwa bazai zauna ba shima tana wani gurin yana wani muhallin na daban. Kamar anni tasan abinda yake tsarawa,ta ciro wani babban envelope ta aje mata a gefanta. "Ga magungunanki nan.....kada ki kwanta baki sha ba.....mun wuce gida mu,sai gobe idan Allah ya kaimu.....saiki kula dashi....muhammad Allah ya qara afuwa,sai da safe". Har baisan sanda murmushi ya kubce masa ba,yasa hannunsa me lafiya ya shafi kansa. "Ameen anni,na gode sosai,Allah ya qara girma" Ita kanta annin tasan godiyar da biyu ake mata ita,batace komai ba dai ta shanye,har sunkai qofa ta waiwayo. "Ki kula da kanki da kyau,kada ki manta da abinda likita ya fada" Ta qarasa maganar tana sauke dubanta kan fuskar fu'ad. Ko batayi maganan kai tsaye ba ya fahimci shi anni ke ajiyewa saqon,saboda haka suna fita ya jawota jikinsa yana cewa. "Ni za'a yiwa gulma?,wai anaso ana kaiwa kasuwa......kinsa anni ta tsareni da warning,wannan maganar da biyu aka yita,kuma dani ake nasan......ita anni ta jikokinta kawai take bata ta d'anta" Ya fadi yana sansana kunnenta,abinda ya sanya tsigar jikinta xubawa,ta yunqura da niyyar gocewa a jikinsa,sai ya fake kaman yadda ya saba. "Wayyo hannuna" Dawowa tayi da sauri ta zauna tana masa sannu. "Muga hannun.....idan yana ciwo a kira likita mana" Ido daya ya kashe mata yana kallonta. "Kece likitan ai.....jeki kulle qofan da key ki dawo na nuna miki abinda zakimin ya rage zugin da nakeji" Ya fada yana karya wuya kaman da gaske zugin yake. Da zuciya daya taje ta rufe din ta dawo,saidai kafin ta ankara ya jawota jikinsa ya matseta da kyau,kota ciwon ma bayayi. "Kada ka fama ciwonka fa.....hannunka muffin" Taketa fada cikin damuwa,bata kula sam da yanayinsa ba sai daya riqe fuskarta da hannunsa daya,sannan ta maida dubanta fuskarsa. Gaba daya idanunsa sun canza launi zuwa kalan ja,kaman yadda numfashinsa yake fita a wani hautsine,take ta fahimci inda lamarin ya dosa. "Sabrrrrr" Yadda sautin ya fita saida tsigar jikinta ya tashi,ta runtse idanunta tana jin ya saukar mata da wani azababben yanayi a dukka sassan jikinta. Sunan da muddin ya kirata dashi tabbas akwai wani abu me girma akanta cikin zuciyarsa kenan. Idanunta da sukayi laushi ta zuba masa tana kallonsa itama,tana jin wani abu yana tasiri sosai a jikinta da ruhinta "I can't hear you,you have too many clothes on" Ya fada muryarsa can qasan maqoshi. Idanunta ta maida ta lumshe,ta gani rigima ce fal idanunsa,ta yaya kuma zai nema rigima irin haka a irin wannan yanayin da suke ciki?. "Please ki rage wannan kayan.....hutawa nakeso nayi". Maganan ya sake mata nauyi,ta bude idanunta a kansa. "Hamma......asibiti muke fa?" Ta fada a narke da wata irin shagwaba data sake kunnashi. "Shshshsh" Ya fada yana dora yatsansa akan lips dinsa,idanunsa suna sake narkewa. Sake zuba masa ido tayi har sai daya karya lagonta,a hankali ta motsa labbanta. "Me kakeso?" Tafin hannunta ya kama sosai ya saka cikin nasa yana murzawa,laushin tafin hannuwansu ya ratsa juna da wani irin dumi da jikkunansu sukayi. "A lot things duniyata...i missed you badly.....but ukunnan....long hug....deep looks....slow kisses,i want you in the worst way...." Can qasa yayi da muryarsa cikin salo na rad'a "Your taste....scent,and feel of your skin next to mine,Duniyata......our bodies could be skin on skin.....i want it all tonight,karki hanani yin komai.....if not" Sai ya girgiza mata kai yana kada mata yatsansa. Gaba daya kalamansa sun gama tsumata,sun gama tafiya da tunaninta da nutsuwarta,sai ta zame hannayenta a hankali daga nasa,ta fara tafiya da baya da baya kafin ta juya tana fadawa toilet. Tsaiwa tayi na wasu sakanni tana maida numfashi......tana sake ji da gaske fu'ad DUNIYARTA NE. "Nothing is hotter than a romantic man" Ta furta tana sakin murmushi ita daya gami da rungume hannayenta
Chapter 149 · 0% Book details