Sashe 7
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ita,hakan kuwa ta sani baya rasa nasaba da qauracewa abinci da tayi akan yadda ta saba cin abinci,duk da dama can ita din ba ma'abociyar cin abincin bace. Ta samu huda ta dafa shinkafa da wake,sai miya da soyayyen kifi daban. Goshinta ta dafe tana zama,kanta tun jiya yake sara mata bayan data jiyo mamma bahijja na magana da qannen mahaifiyarta da kuma kawu Abdul Hakeem,tana shaida masa jibi gobe kenan shine ranar daurin aurenta bayan sallar juma'a. "A zuba miki adda?" Huda ta tambayeta cike da fatan ta amsa cewa zataci din. Hannuwan huda da sukasha lalle tabi da kallo. Ko nata hannuwan farare suke sidik da zara zaran yatsunta dake dauke da dan baqin lalle dan kadan saman farcenta,ragowar lallen data yiwa adon yatsunta wata biyu baya da suka shude. "Zuba......amma kada kisa miya.....mai zaki saka da dan maggi kadan" Ta yiwa huda bayani a taqaice tana zare idanunta daga sashen da suke. Sauka idonta yayi kan wayarta dake ajiye wadda a qalla ta kusa kwana biyu a wajen. Sam bata da sha'awarta ma don batajin zuwa yanzu tana da wani uzuri da ita. Jib,ayshatu,qannenta da sauran mutanen da takejin sun Ta'allaqa a wuyanta kadai zuciyarta ke mata amsa kuwwar ta nemesu.......tayi sallama da kowannensu.....saidai kuma wani sashen daban yana bata qwarin gwiwar bata da buqatar hakan!. Tana ji a rai zuciya dama jikinta tamkar wani gajeran balaguro ne kawai zatayi daga tata duniyar zuwa wata duniyar,balaguron da bai wuce misalin qifatawar idanu daga rufewar zuwa budewar ba. Bataji kwata kwata cewa wai auren zai zama wani dogon aiki da zata kasa yakiceshi cikin qanqanin lokaci. A yanzun zata zubawa komai da kowa idanu.....kwadin me kwadayi......burin me buri......da tsarin me tsari a kanta ya kwanta.....sannan ne ita kuma zata aiwatar da nata shirin hankali kwance( nikam nace uhmmm....qaddara dai ta rigayi fata Da plate huda ta dawo,wanda tsara zuba abincin gwanin sha'awa. Sabreen tasan duka tayi ne don taci,ta jera soyayyen kifin saman shinkafa da waken,sannan ta mata roban yaji da magi daban. Da kallo kawai tabi plate din,don tasan yafi qarfinta koda duniya ma tana kwance bare yanzu da wani abu waishi abinci baya burgeta. Sallamar kawu rufa'i da sautin muryarsa kadai ya sanya abincin data sanya a bakinta ya tsaya mata cak a maqogaronta,sauran na bakinta kuma taste dinsa ya canza mata,har tana jin ba zata iya taunawashi ba,har sai data tattara dukkan juriyarta sannan ta tauna ta turashi zuwa maqogaronta wanda ta samu ya wuce da qyar,sai kawai ta yanke hukuncin ajiye abincin. Idanunta ya sauka kan kawun sanda take ajiye plate din a qasa,wanda yake jaye da wata mini luxury luggage me azabar kyau da kuma daukan idanu. Koda bakasan me duniya ke ciki ba,koda bakasan darajar abinda yake janye dashi ba tabbas zata fahimci luggage ne me tsada da madaukakiyar daraja. Wajen zama mamma bahijja tayi masa tana sanya nadra ta ajiye masa drink da ruwa. "Ya hidima ya kuma shirye shirye?" Kawun ya furta da muryar dake nuni da zallar farincikin da yake ciki "Alhamdulillah.......ai kune da hidima,tunda mu nan ba abinda zamuyi" Kai kawu rufa'i ya girgiza yana satar kallon sabreen da tunda ta gaidashi bata sake koda kallon sashen da yake ba. "Allah ya yiwa yarinyar nan taurin kai bahijja......idan kinga abubuwan da sukaso gabatarwa zakisha mamaki......har yanzu quruciya ke dawainiya da ita,inda tasan girman matsayi da darajar mutumin da zata aura,na rantse miki saita qare rayuwarta tana godemin.....attajirin matashin da babu irinsa a wannan qarnin da muke ciki?" Dan murmushi kasan momma bahijja tayi,adan zamanta ta fahimci kawun yana sa son abun duniya "Duk bama wannan ba rufa'i,indai har bincikenku ya tabbatar da nagartarsa ai magana ta qare.....dukiya wannan wani abune na daban ai" "Habawa.....idan ana batun nagarta ma da dattako har ayi magana wadannan dattijan?" "To alhamdulillah.....haka akeson ji...." "Yanzu haka ma aike ne......saqo ne na musamman daga surukarta......kaya ne tace a kawo mata da zata sanya a gobe kenan" "Tofa.....ikon Allah,kuma dai?,basa gajiya?"Momma bahijja ta fada duba da irin kudaden da aka narkar,tun daga dukiyar aure har izuwa batun lefen dasu kansu har yanzu basu gama sanin komai da komai dake cikin akwatunan ba. Tana qara ganin girman qaunar da suke gwadawa sabreen din,a gefe guda har ranta tana jin tamkar sabreen din tayi sa'ar inda zata rayu cikin qauna da kulawa. "Wai wai.....ma sha Allah" Momma bahijja ta furta tana daga lafiyayyen applique lace da kudi suka koka qwarai wajen siyensa. Daga qasanshi kuma wata bazin ce data amsa sunanta sai super Sheraton da iya ado da gayu da kashema kai kudi irin na momma bahijja bata taba katarin ganin irinta ba. Daga qarshe set ne na banguls earrings da sarqa da zobensu duka na danyen gold me matuqar daraja(nikam nace masu abu da abinsu). Ko qwaqwqqwaran motsi sabreen batayi ba ballanta ta daga kanta ko zata nuna alamun tasan bidirin da akeyi,har sanda hadiyya tayi sallama tana shigowa falon da guntuwar fara'arta. Sunan kayan kawai ya gaya mata darajar abinda aka sako a ciki saidai hakan bai dadata da qasa harta daga kai ta basu darajar kallo ba,don batajin zata iya rabasu a jikinta. Komai daya fito daga hannunsu duhu yake mata,baya mata haske ko kadan.....musamman da take kyautata zaton kayan sun fito ne daga hannun waccar matar maras daraja. Still shigowar hadiyya bata sakata daga kai ta dubeta. Can qarshen zuciyarta danqare da mamaki,yadda kudi ke iya sauya dabi'un mutanen duniya cikin qanqanin lokaci,duk da wannan karatun ta jima da haddaceshi......kusan shi ya zama sila na sauyawar DUNIYARTA. Hadiyyan ta sauya kamar ba ita ba,abinda bata taba tsammanin zaya faru nan kusa ba. Bata zaqe da yawa ba wanda tasa tasirin karatu ne wala'alla da salon gogewa......hakanan kowanne taku kadan tana yunqurin kutsa kai jikinsu ne. Hadiyya ita ta qarasa daga kayan matsanancin mamaki yana sake kasheta. Hidima sosai suke gwadawa sabreen din kaman rijiyar kudi garesu. Ba wanda yakai me kudi sanin darajar kudi,saidai ga wadannan bataga alamun hakan sam daga garesu ba. "Gashi zakiyi magana da surukarki" Momma bahijja ta fada tana sauke wayarta daga kunne gami da miqawa sabreen. Dan turus tayi tana sauke fararen idanunta akan fuskar momma bahijja din. Muddin wannan matar ce sam bata da sha'awar wata magana da ita. Komai nata bisa gadara ne iko izza da kuma nuna qarfin dukiya,don me zata zauna tana gwada mata tata izzar bayan ba ita ta gayyaceta cikin rayuwarta ba. Idanu sunyi yawa a kanta,don haka ta sanya hannu ta karba tana kauda fuskarta daga kallon idanuwan. Sallamarta kadai ya gaya mata ba wadda take zato bace,cikakkiyar sallamar data saukar da duk wani zafi da zuciya da kuma halshenta suka dauka,saita amsa mata a nutse matuqa "Kina yini lafiya diyata?" Anni ta fada daga nata bangaren jin sabreen din tayi shuru. Karon farko sai taji nauyin matar ya saukar mata,batasan me yasa a iya waya kawai takejin girma da kwarjininta ba......shin itace asalin mahaifiyarsa ko yaya?.....itadin wacece a wajensa?,waccan ma wacece a wajensa?. Iya wannan tambayoyin da bata da amsa kadai suna sakata a jikinta tana jin tabbas akwai wani gagarumin abu birne a qasa.....duk da zuciyarta tana gaya mata ba wani babban abu bane da zai gagari sarrafawarta ba. "Barka da yamma.....lafiya alhamdulillah" Ta hade gaisuwar da amsar tambayarta. "Ma sha Allah" "Naga saqo,na gode" Tayi hanzarin fada,don a cikin ranta takejin bai kyautu ba har sai ta magantu. "Ba komai......inaso ne kawai kiyimin alfarmar sanyasu a duk sanda zaki shigo ahalinmu" Tayi maganar a tausashe cikin kuma nuna kulawa,kulawar data bayyana kanta sosai cikin sautin muryarta "In sha Allah" Ta sake amsa mata "Ina fatan hakan ba takura?" "Ba komai....in sha Allah" "To alhamdulillah......ina roqon ubangiji ya tattara dukkan alkhairanku ga junanku......ya kauda kowacce irin fitina da abunqi a tsakaninku". Batasan me yasa ma......amma har tsakiyar qirjinta taji saukar addu'ar......batayi kuskure ba idan tace kunnuwanta itace mutum ta farko data fara jin addu'ar daga bakinta,sai taji labbanta sunyi nauyi bare su tallafeta ta amsa.....yayin da anni tayi zaton kunya da kawaici suka hanata amsawar......a haka tace ya baiwa momma din wayar. Zuciyarta tayi nisa qwarai da zurfi wajen tunani,har batajin ma meke wakana cikin falon,sai kawai ta yanke nesanta kanta dasu ta hanyar komawa daki kaman yadda ta maida hakan dabi'arta. Bata jima cikin duniyar dakin data maida mazauninta ha nadra ta shigo dauke da wayarta a hannu. "Ana kiranki" Ta fada tana miqa mata wayar. Kamar tace mata ta koma da ita sai ta fasa,ta saka hannu ta karba tana daga kwancen tana duba me kiran. Sunan data gani ya sanyata miqewa ta zauna sosai babu shiri,hannunta na gaggawa wajen amsa kiran ta sakashi a kunnenta "Kicemin kun dawo titi don Allah,kicemin ayshatu ta warke" "Na warke adda......na samu sauqi" Muryar yarinyar ya saukar mata a kunne. Wani hawaye me sanyi ne ya kubce mata,kullum da lamarin yarinyar take kwana take kuma tashi,daga yadda taji muryarta tasan cewa tabbas lafiya cikakkiya ta samu a gareta "Muna cikin sabon gidanmu yanzu aunty.....na gayawa titi bazan yarda na fara ganin kowa ba sai ke". "Yanzu kuwa zaki ganni ayshatu" Ta bata amsa kai tsaye kaman ta manta a wanne yanayi ita din take.....kaman ta manta rabonta da taka qasar waje wasu kwanaki ne masu yawa. Da wani irin excitement ta ajiye wayar,ta zura qafafunta qasan gadon da hanzari zara miqe da nufin shiryawa,sai kuma ta dakata cak saboda dawowa hayyacinta da tayi. Tayi imanin wadannan mutum mutumin har yanzu suna tsaye a qofar gidansu suna gadinta,yawan mutanen dake kai kawo a gidan bai sanyasu sun tafi ba......don ko dazu ita iya jiyo baqin tsagin abbansu suna tambaya a kansu. "Saina fita kota halin qaqa wannan karon......ko meye zai faru saidai ya faru" Ta fadi tana qarasa saukowa,ta kuma fito kai tsaye zuwa ga falon tana nufar doguwar veranda din dake saman wanda tacan zata samu hanyar gangarawa qasa ta koma ainihin dakinsu. _DUNIYA TA na kudi ne_ 08187255862 Page 06 Batasan gidan ya fara daukan mutane ba sam sai data sauko din. Gomayyar idanuwa sukayi kanta caaa ana qare mata kallo. Kowa da nashi tunanin cikin ranshi,wasu na kallon tsantsra kyan data qara saboda gyaran jiki na musamman data samu tsahon kwanaki daga wajen qaararriyar me gyaran jiki......wasu kuma na mata kallon sha'awa suna fadin inama su ko 'ya'yansu