Sashe 73
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mana" Sai data gyara zamanta tana maida mata murmushin sannan tace "Yaaa saddiq yana bani labarin hamma......duk da na fisu sanin hamma ta wasu abubuwan.......amma ya saddiq kuma zai iya fina saboda shi din PA dinsa ne.....duk inda zai saka qafa a gida ko a office suna tare.......kinsan waye hamma kuwa?,ya yake?" Tayi tambayar da murmushin daya kusa zama dariya akan fuskarta. Numfashi taja a boye tana jin sunansa kawai da amna ta kira yana qara yawaita bugun zuciyarta,inda zata iya zata dakatar da amna daga yi mata duk wata hira data shafeshi......kwanaki kaddan suka rage masa cikin rayuwarta.......tana jiran kawai ranar da zata samu tabbacin su huda sun isa mali lafiya hannun momma bahijja.......a wannan lokacin komai zai tarwatse. "Saikin fada amna" Ta fadi bawai don ranta yana so ba,sake gyara zama sosai tayi ta riqo hannun sabreen "He's a loving and caring partner.he wants a deeply romantic connection with his wife" Ta fada murya can qasa,kaman tana tunanin yana kusa dasu kuma tana tsoron kada ya jiyota. Dukka idanunta sabreen ta fiddo waje tana kallon amna,yadda amna din tayi maganar da wani confidence da qwarin gwiwa ya bawa sabreen mamaki.....can qasan zuciyarta kuma sai taji kaman tanason taja hira kadan da amna din. Abu daya dai tayi amanna fuskar fuad ta gida daban......fuskarta ta gidansa daban.....kamar yadda fuskarsa ta mu'amalarsa ta waje daban,banda haka mutum kaman fuad dinne zata siffanta haka?. "Kina da ja ko adda?......" Ta tambayi sabreen kai tsaye,tana jin tanason tayi hira da ita.......tanaso ta fadi mata abinda ta fuskanta ko ita ta fahimci ba daidai ba "I swear adda........He envisions a future where he and his wife grow old together,hand in hand......ko a gabana wannan yasha fadinsa......musamman idan suna hira na sako da sako shi da BB farouq.......hamma na yana son soyayya,ya kuma cancanceta......hammana yana son kulawa......that's why yakeji dani,komai na hammana daban yake a wajena.....tausayin hamma nakeji coz....He suffered a lot in his life He had a rough past" Ta fada dukka a jere tana riqe da hannun sabreen kaman hakan shine zai saka ta fahimta abinda takeji a zuciyarta na tausayin hamman nata. Baki da idanu kawai sabreen ta sake tana kallon amna,tana sake gasgatawa da imanin cewa eh lallai da gaske wannan mugun yana da muhalli me girma da fadi a rayuwarta......amma wanne irin hardness ne haka ya fuskanta?,mutumin da ya rayu tsakanin iyaye biyu 'yan uwa hudu?,mutumin dake cikin daula da dukiya?. "Believe me adda......please,ki qara akan kulawan da kike bawa hamma,He's passionate about building a strong loving relationship with his wife.......na dade da sanin duk wadda ta samu hamma fuad.....She's the luckiest woman alive and she's incredible fortunate" Murmushi ta samu kanta da subucewa dashi,saita miqa hannu ta riqe amna din sosai bawai don maganganu da yabo a kansa sun burgeta ba,aah......sai don ita din mutum ce me girmama 'yan uwantaka,saboda tasan girman soyayya da qaunar dake tsakanin 'yan uwa me girma ce......itace babbar shaida ta farko akan hakan akan kanta ma. "Duka wannan yabon amna......anya baki fiya son kanki da yawa ba kuwa da wannan birkitaccen hamman naki?" . Murmushi amnan ta saki itama,har qasan ranta taji dadin yadda sabreen ta karba maganganunta,amma har ga Allah tana son matar hammanta ta zama dream wife nashi kaman yadda dukkaninsu suka fahimta "Ki budewa hammana zuciyarki da kyau.....zaki sha mamaki adda.......inajin tukuicin zuwa dubai zakimin duk sati.....nayita zuwa ina ganin burj" Murmushi ta sakeyi kawai batace komai ba......abinda ya bawa amna daman sake cewa "Adda.......na baki kadan daga tarihin hammana dana samu tun kafin a haifeni.....wannan ne kadai zai zame miki jagora wajen sake fahimtar waye.....ya kuma.baki qwarin gwiwan tallafarsa" Zame hannuwanta tayi daga cikin na amna tana girgiza kai "Zaki bani.....amma ba yanzu ba amna.....kinga bana jin dadi sosai" Itama tayi maganar tana narkewa amna kaman yadda amnan keyi. Murmushi ta saki tana tuna warning nata da anni tayi akan ta kula da ita,kuma kada ta matsa mata da yawa,don haka sai tace "Mu barshi pending......har sai kin samu lafiya" Kai ta gyada tana lumshe ido kadan "Na gode" Har qasan zuciyarta tana jin dadin yadda amna ta fahimceta ta qyaleta. Sam bata son jin komai daya shafeshi,saboda tasan zasu fadi kirkinsa ne kawai bawai don haka yake ba,zasu fadi kirkinsa ne don haka yake nuna musu a fuska da mu'amalarsa da su,amma a waje kuwa.....babban azzalumi ne a wajenta mugu kuma. Maida dubanta tayi kan maamah "Ban taba kiran wani d'a namiji da adadi me yawa ba irin wannan sai d'anki......na masa kiran qarshe......inaso naga naki qoqarin" Abinda fareeda ta fada kenan ranta yana motsuwa hadi da qara baci akan lamarin. Bata taba daukan plan dinta bazaiyi wani aiki ba,kudade ta kashe masu nauyi don a buga ninkin adadin news paper din da aka saba bugawa a kowacce rana......sannan a fiddata tituna a kuma rabata kyauta ga kowa basai kowa ya siya news paper ba a ranar. Guri daya maamah ta zubawa idanu tana murza tafin hannunta,tana ji a jikinta lokaci yayi da zata koma wajen boka ta zube masa komai.......ta gaya masa buqatarta ta gaba,ta zube masa ruwan kudin da ko bai shirya ba dole yayi aikin nan......daga can wani loko na zuciyarta tana fargaba.......tana fargabar kalamansa na can watannin baya......kalamansa na qarshe a haduwarsu ta qarshe dashi. _taurarinta nada tsananin haske da wahalar cusa kai a cikinsu.......tabata abune da zai iya zuwa da nasara da kuma akasinta.........KINYI KUSKUREN ZABINTA......amma itace mahadin masarrafin b'arin nasa tauraron..........taurarinta sune abokan tafiyar nasa taurarin.........kusan komai nasu suna kamanceceniya da juna.......ITACE TA DACE DA CIKAR BURINKI MUDDIN AKA SAMU GUSHEWAR AKASIN DA NAKE HANGOWA_ Gumi ne taji yana tsatsatsafo mata......a take sai taji ai kaman ta fara shiga matsalar daya ambata mata. Sai yanzu kwanyarta ta fara aikin da a wancan lokacin bata yishi ba wato na fahimtar ma'anonin maganganunsa. Kenan aikin banza takeyi?,kenan ba wadda zata iya cika mata burinta akan faud sai sabreen din da take kokawar fitarwa a gidan?,wannan wanne AKASI NE da boka ke magana a kai wanda yace muddin ya gushe ita zata iya cika mata burinta......wanne akasi ne?. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ _ko kisan manzan Allah S A W da kansa ya kasance yana neman tsari daga sharrin abinda ya aikata da wanda bai aikata ba? Yakan ce"Allahumma inni a'uzu bika min sharri ma amiltu wamin sharri ma lam a'amal"_ _shi daya kasance Allah ya gafarta masa duk wani abu da zaiyi da wanda ma yayi,ina gake?_ Dukka jikinta sai ya dauki wani irin dumi,tamkar ma ta manta da fareeda dake zaune gefanta,wani yalwataccen tashin hankali ya duro mata......cikin qasa da minti guda taji tana tsananin buqatar ganinsa. "Ke nake sauraro" Muryar fareeda ta yanke mata tunaninta. Idanu ta zubawa fareedan na wasu daqiqu kafin ta kammala tunani a kanta dukka cikin sakanni,murmushi ta sakar mata. "Mu da kikaga muna cimma nasara a rayuwarmu......ba da gaggawa muke tafi da komai ba......kibarmin komai a hannuna......indai kinga baki samu fu'ad ba.....to tabbas bani na haifeshi ba". Maganar ta faranta ran fareeda duk da ta xuba mata kokwanto me yawan gaske. Amma itama ta yarda da kanta......tasan kuma nata kalar takun,don haka ta miqe da nata murmushin tana ajiye mata bundle na dollars. "Ki qara da wannan......amma buqatata yazo ya ganni koda na minti talatinne kacal" Ta furta tana zuge zip din Jakarta,a qasan ranta kuma tana samun tabbacin da gaske ne fu'ad baya sakar mata zallar ruwan kudi.......abu na farko daya fara jefa mata shakka a zuciyarta akan matar. Matashin billionaire irin muhammad jadda......wanda tsananin yawan dukiya da arziqin daya mallaka a gefe guda quruciya da kyau su suka saka mata kwadayin mallakarsa......kudaden data bata din ya kamata ace a kullum a arziqinsa basufi kudin siyan wasu qananun abubuwa ba....amma ya zamana ita ke fara'a da samunsu?. A arziqin mahaifinta idan aka kasa arziqin fu'ad hamsin qwaya daya ne.....amma ace ita karan kanta tana da qarfin halin yin kyauta irin wannan?. TABBAS AKWAI MAGANA.....MAGANGANU MA,ta furta a sarari qasa qasa. Kudin kawai take juyawa a hannunta farinciki yana kamata. Ta samu kudin da zata tunkari aikinta,duk da tana baqincikin yadda kudin xasu salwanta,amma kuma idan ta tuna da ribanya ribarsu da zatayi sai taji koda ta salwantar da finsu ma ba komai bane. Saidai tana buqatar magana da yarinyar.......maganar da zata sake bata haske akan mataki na gaba da zata tabbatarwa boka shi take da buqata. Wa zara kira?zuwaira..... Kira daya biyu uku hudu har goma wayar zuwaira a kashe take. Tayi tsaki har batasan adadinsu ba,da waye zatayi magana ya hadata da yarinyar?. Tsam ta miqe data tuna daxun maganarsu ta qarshe zuwaira ta gaya mata yarinyar taje gidan ita da mamarta,saidai batasan ko tana can ko sun dawo ba. Ta qwalawa badawiyya kira "Ki tafi gidan hamza ki karbomin number wannan yarinyar" "To hajiya" Ta amsa mata a ladabce sannan ta juya tana ficewa ba tare data tsaya jiran komai ba. Hannunsa ya sanya saman labbansa kawai yana sauraren bayanin manager na gidan jarida na qarshe da yakeyi,wanda banbancinsa dana sauran qalilanne "Amma wallahi wallahi ranka ya dade kaman yadda 'yan uwana suka fada ne......wallahi bansan sadda aka buga labarin ba......ni dinma kamarsu gayyata na samu na taron 'yan jarida unexpected.......amma sanda na iso na samu jaridar ta fara fita hannun dealers na dakatar da saidata......waye zaiyi wasa da mutum kamar kai?,wanne gangancinne zai debi mutum......ko baya ga haka kana da mutunci da martabar da bai kamata mu bari a bata sunanka dana iyalinka ta wannan hanyar ba" Mutumin da aqalla ya kusa shekara sittin a duniya ya fada cikin matsanancin takaicin yadda duk karamci irin na jadda jaridarsa ta shiga sahun wadanda suka ci masa mutunci....duk da Allah ya taqaita an daqile fitar jaridar. Iska me zafi ya furzar daga bakinsa yana sauke qafafunsa qasa,kanshi yana sake daukan zafi da lamarin. "Inason list na dukka mutanen dake da aiki a ranar a dakin buga labarai.......da full details na kowa" Ya fadi a ransa yana jin zaiyi aikin daya jima baiyi ba. "Sir.......ai mun kammala wannan.....muna jira ne kawai ka gama ji daga bakinsu......dukkanin dealers din mun karbi copy na newspapers din daga hannunsu,yanzu haka ba wanda keda sample nata.....Allah yasa munyi abun da sauri basukai ga rarrabawa qananun 'yan kasuwa ba,mun samu dukkanin jerin mutane hamsin