Sashe 19
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read
Zai zamana kome xasu fitar ko su samar asara ce a garesu,dole su saidashi a qasa da farashin da aka tsara za'a fiddashi. Saqonnin da aka yita turo masa suka dawo masa akai,ya lumshe idonsa ya kuma budesu yana kiran sunan Allah,sai ya sake maida hannunsa kan system din. Kusan duk wani ma'aikaci dake aiki qarqashinsa na kusa dana nesa sai daya nemeshi. Ya bata lokaci sosai yana urgent meeting dasu,wanda hakan ya daukeshi aqalla a wanni masu dan dama. Baisan kuma ya jima din a zaune ba sai da cikinsa ya fara qara. System din ya rufe yana furzar da iska daga bakinsa. Ya tabbata babu abinda zasu iya sakeyi......dole su rungumi dukka hasarar data tunkarosu lokaci guda...... Akwai manufa.......kuma anyi ne da gayya,kuma hakan ya sake bashi tabbacin dukkanin saqonnin da aka aike masa da gaske suke.....sun shirya shiga yaqin tare dashi.....sun shirya jan daga shi dasu. Sai ya saki wani qaramin murmushi. Sunyi gangancin fara tsiro irin wannan abun dashi......ya tabbatar basu gama sanin ainihin waye muhammad a kasuwancinsa ba.......wannan abun koma waninsa bazai sauyashi ba......bazai kuma sakashi ya tsaida kowacce harka tashi ba. Har a jikinsa yakejin a baqon guri yake,banda haka zuwa yanzu da tuni Ameh ya dameshi da batun abinci. Hannunsa ya miqa ya dauki wayarsa ya kunnata daga kashetan da yayi "Subhanallah" Ya furta da hanzari ganin har azahar ta sanyo jiki. Bai kira anni ba.....bai kira farouq ba,baima kira kowa ba wanda aqalla ya dace ya yiwa kowa bangajiya koda kuwa ba shine ya gayyatosun ba,amma aqalla sabodashi suka zo. Anni ya fara kira amma sai yaji wayar a kashe,yasan har yanzu gidan akwai sauran baqi don haka yafi kyautata zaton uzurin daya sakata kashe wayar kenan. Yayi zaton zai samu saqon farouq amma sai ba tarar ba. Ya danji ba dadi,don haka kai tsaye ya fara kiransa. Bugu daya ya daga kamar dai dama wayar tana hannunsa yana jiran kiran nasa ne. A nutse ya masa sallama,daga can background yana dan jin muryar mutane. "Kaji muryar ango......so fresh" Farouq din ya fada kansa tsaye. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE_* 08187255862 _zafafabiyar_