← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 215

Sashe 119

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

fada yana juya hannun cikin tafin hannunsa. Ya mata wani irin kyau kaman saboda ita aka qirqireshi,ya zuba idon hannu yana jujjuyashi kafin a hankali yace. "Our latest wrist watch...2025,kin masa kyau duniyata.....nayi accepting wannan design din saboda ke,koda baiyi daidai da ra'ayin dealers dinmu ba,i love it for the sake of you" Ya qarasa maganar a tausashe yana kai hannunsa yayi kissing hannun nata,still idanunsa a kanshi,ya zura hannunsa a aljihunsa ya fiddo wayarsa ya laluba wata number ya kira. Bugu daya aka dauka,da hausa taji yana magana. "Mun siya design dinnan......sannan madam ta ninka price din da wasu dollars din akai ainihin price din". Ya fada a nutse da alama yana magana da wasu ne " Alright " Taji ya sake fadi yana katse kiran,yana maida wayar aljihunsa tana dubansa idanunta a warwaje,sai daya daga kai sannan suka hada ido,fuska ta narke "Wacce madam din?" Ta tambaya da siririyar muryarta dinnan,miskilin murmushi ya sake mata "Akwai wata bayan ke?" Saita sake fidda idanun "Ban da kudin siya fa....thought dai bansan nawa bane" "Amma kina da muhammad jadda ko?" Ya furta yana ja baya kadan idanunsa a kanta. Yana jin dadin kallonta sosai,sai yakejin duk wata tsohuwar kewa ta rayuwarshi tana sulalewa,yana jinsa wani sabon mutum na daban. Duban hannun nata tayi,haka kawai taji kaman ya saka mata wani abu me daraja da yawa,sai takejin hannun ya mata nauyi. "Na gode.....na gode sosai" Ta samu kanta da furtawa a sanyaye. Wani tsadajjen qaramin murmushi ya saki yana girgiza kansa. "No.....no need duniyata.......ba irin wannan godiyar nakeso ba.....the only one i want........" Sai bai qarasa ba ya mata nuni da shimfidadden gadon. Da sauri ta juya masa bayanta tana kasa hada ido dashi,ta fahimci yana bawa abunnan muhimmanci tamkar baisan kayan kunya bane?. A nutse taji ana yafa mata abu ta baya,ta daga kanta sai taga wata baqar sassalkar abaya ce,manal alhammadi shine tambarin da yake maqale a hannun rigar,ta fidda idanunta tana jin wani abu yana girmamarta,ta taba jin company din,wanda dukka abayas da yake fitarwa luxury ne masu tsada da aji sosai,ta sansu ne saboda ita din masoyiyar abayar ce. "Ba wani kunya tsakanin muhammad fu'ad da duniyarsa......ba kunya tsakanin muhammad fu'ad da matarsa......abinda kawai yake buqata......madawwamiyar soyayya da zata mamaye rayuwarsa.....ta bashi wani farinciki da nutsuwa daya rasa a rayuwarsa.....duk da cewa ina zaqewa da yawa.......amma wannan abun nake bara" Ya rigata fada kafin ita ta fada. Boyayyen murmushi ya subuce mata,wato daga jiya zuwa yau ya fara haddace irin kalmominta kenan da take yawan maimaita masa?. Juyo da ita yayi yana zura mata hannayen rigar ya furta "Fatabarakallahu ahsanul khaliqeen.....komai saikin masa kyau?" Yayi maganar yana dage girarsa. "Komai saina masa kyau?.....ko komai sai yamin kyau?" Ta tambayeshi tana mamakin yadda yake juya maganar daga qarshe ta koma farko. "Kece kike musu kyau basu keyi miki ba.....don dama kedin me kyau ce.....you're not ordinary duniyata" Yayi maganar sanda ya dago daga tsugunnan balle mata button din da yayi har qasa. Mayafin ya warware yayi mata lafiyayyen rolling tana tsaye tana kallon ikon Allah,ya kama hannunta zuwa gaban mirror yayi tsaye a bayanta. "Duk wani abu me daraja rufeshi akeyi a killaceshi" Ya furta a nutse yana duban kyakkyawar fuskarta ta cikin madubin,yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa saboda ita,kishinta yana sake ratsashi da kyau,yana sake jin tabbas......lallai ba wanda zaisha ba kuma wanda zaici bulus daga cikin mutanen dake hannunsa a yanxu.......tun daga kansu mashkur har zuwa kan zuwaira da bibo. "Ga aro nan na baki.....idan munci abinci mun dawo zaki bani kayata" Ya fadi wannan karon yana dan sanya seriousness saman fuskarsa. Dan dubansa tayi kadan,sai ya gyada mata kai alamun tabbatarwa. Yanaso ne yayita kallonta,yanason wucewar kowacce daqiqa tayishi bisa idanunsa,yanaso yaci gaba da kallon baiwa da ni'imar da Allah yayi masa,yanaso su kasance a haka shi da ita......da zaiyiwu su qare rayuwarsu cikin irin wannan yanayin na dagashi sai ita. Yana maqale da hannunta suke sauka zuwa bangaren cin abinci,private ne wanda ya dauko musu cook dinne musamman saboda iya su biyun. Sun samu dining room din cike da cima kala kala,abincin Africa da wasu na Nigeria. Macace da batace ga daga qasar da take ba,ta tarbesu cikin haba haba sannan ta fara serving nasu cikin kulawa,lokaci lokaci tana magana da fu'ad da hankalinsa ke waya cikin yaren Dhivehi,har ta kammala ta juya ta fita tana basu guri. Juya spoon din take kawai a plate din tana hadiye wani abu a qirjinta. Batasan meye ba amma ya tsaye mata a wuya. Bai ankara ba,sai daya gama uzurinsa da waya sannan. A mamakance yake dubanta. "Start mana madam....banason wasa da abinci fa?". "Itama fareedan ce?" Ta tambayeshi da wani salo daya sanyashi karantar zallar kishin dake kwance a idanunta,saidai kuma a sarari qwalla ce kwance saman oily eyes dinsa,sai suka qara wani sheqi. Dariya yakeson mata saboda wani irin farinciki yaji yana lullubeshi,tun daga saman zuciyarsa yana sauka ta kowanne sashe na gangar jikinsa. Har ya fara winning haka da wuri? Ya tambayi kansa yana taya kanshi murna,amma a bayyane sai ya lanqwasa fuskarsa alamun tausayi. "Me kuma nayi?". Muryarta na rawa kadan tace. "Kunata magana da yaren da banaji.....tanata maka hira kana amsawa?". Wannan karon kam kasa boyuwa dariyarsa tayi,abinda ya tunzurata kenan. " Karki wuce gona da iri sabreen,karki rudu ki fada soyayyar abinda ba yafi qarfin ajinki.....abinda yafi qarfinki,abinda baki da tabbas a kansa.....shin kin Manta maamah tana nan?". Tambayar data tarwatsa duk wani qwarin gwiwa da take qoqarin tattarawa kanta,taji kuma komai ya tsaya mata cak. Dab da ita ya dawo ya zauna,ya kama hannayenta ya saka cikin nasa yana matsawa a hankali. "Kin taba ganin mutum ya canza DUNIYARSA?" ya mata tambayar kai tsaye,qasa tayi da kanta don sai takejin tana son jefa rayuwarta cikin hadari ne kawai,muddin ta sakewa zuciyarta ta fada sonshi to ba shakka ta fada babban tarko......babban tarkon da zai bawa maamah daman walagigi da rayuwarta yadda taga dama. "Amsar itace aah......ke duniyata ce,babu daman na sauyaki ko na hadaki da wata ko wani abun......ni muhammad jadda naki ne ke kadai,don ke kadai aka halicceni.....ki rubuta wannan ki ajiye" _to zamu gani,anya hajiya maamah zata qyale kuwa???_ *ANNI* Tun a jam'in sallar asuba da sukazo yi taga bata ga fu'ad ba.....still da tace farouq ya turo mata shi komin dare baizo ba,har suka gama waya da abba Alhaji hamza kibiya dake tashi umrar ta kwanta amma ba fu'ad din ba dalilinsa. Sanda suka kammala sallar sai tayi zaune kawai tana lazimi,tunaninta yana rarrabuwa,bataga fu'ad ba......bataga sabreen ba,duka ina suka shiga?. Ta wata fuskar sai takejin relief na rashin ganinsu su duka biyun,don zuciyarta na qissima mata wani abu,ta wani bangaren kuma bataso ta sake jikinta akan hakan,saboda tasan wace mariya din. Takwas saura farouq ya shigo gaidata. Yana daga zaune gabanta ya dan dubi amna dake kwance tana shirin komawa bacci "Ta duba qur'aninta kuwa?". Kai anni ta daga masa " Ta duba" Sai ya jinjina kai. Wani sabo ne da raino data musu dukkansu,dole kowacce safiya....komai uzurinka ko meye kakeyi ka fara duba qur'ani kafin komai. "Kiramin fu'ad.....ka gwadamin dukka layukansa" Anni ta fadi tana gyara zamanta. "Na gwada wani tun jiya a kashe,amma bari na gwada sauran" Farouq ya fada hankalinsa kwance,don shi kam ya gama hasashen inda aka haihu a ragaya ma. Baya tunanin ko maamah ta yiwa fu'ad farin sanin da shi yayi masa. Daya bayan daya yabi layukansa yana kira amma kowanne gaya masa ake a kashe yake,sai ya daga ido kawai yana duban anni da fuskarta ta shiga damuwa. "To ina ya shiga?,ina kuma sabreen?". Dariyarsa ya danne yana dan saka alhini a saman tasa fuskar shima "Karki damu anni in sha Allah jikina yana bani suna tare,bari na tura masa email da SMS duka" Ya fada yana fara rubuta saqonnin ya kuma aike masan kaman yadda yace,duk da yasan zai wahala ya gani a kwanakin nan,lallai indai ya samu nasarar dauke sabreen ne tofa sai baaba ta gani.
Chapter 119 · 0% Book details