← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 215

Sashe 129

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A tausashe yake riqr da tafin hannunta sanda suke saukowa daga cikin jirgin har suka kammala saukowar. Batasan kallonta yake ba sai daya matsa hannunta,tadan daga kanta ta dubi idanunsa. Haka kawai takejin wani farinciki yana shigarta duk da rashin dadin da jikinta da takeji.......farincikin sauka a birnin madina......birnin da ba birni kamarsa,wanda yake qunshe da baiwawwaki masu tarin ni'imomi da falala. Saukarta a garin kadai ya tuna mata labarin madeena da ummensu tasha basu. "Gari ne dake da wani irin nutsuwa a cikinsa,kana sauka zakasan yasha banban da duk wani guri da kuka taba zuwa a duniya". Ta sake samun tabbaci yanzu haka,ta kuma sake gamsuwa da hakan dari bisa dari. " Zuciyata tanata rayamin baby zaki haifomin sabrrrrr......ki daure ki cikamin wannan mafarkin nawa......ni kuma zan fansar miki da ko mene na mallaka a rayuwata" Ya qarasa maganar yana kallon gabansa sanda suke dab da isa arrival hall. Idonta ta zare a kansa,ta jima bataga wani mutum me jarabar son yara ba irinsa,batasan me zata ce masa ba,don haka ta zabi yin shuru. "Zaki bani baby my world?" Ya sake tambaya yana dan matsa hannunta kadan na tare daya kalleta ba. Shuru ta sake yi sai shima bai qara tambaya ba har suka qarasa gurin. Hannu taga yadan daga,saita maida dubanta ta gurin. Saddiq ya hango,sanye da baqar jallabiyya ta maza da baqin hiram. Quruciyarsa da kyansan nan da suka gada daga gurin anni ya sake fita sosai. Kaman giftawar walqiya,kaman kuma cikin majigi idanunta ya subuce zuwa gefansa. Farar matashiya ce,sanye da baqar abaya itama,hannunta dauke da welcome board dake dauke da sunan ADDA SABREEN AHMAD. Ta kasa ganin fuskar matashiyar don ta kare fuskartata da board din. Jinin jikinta taji ya harba da gaske da wani irin gudu,saita soma leqawa ta hagu da dama tanason ta tabbatar abinda take zargi ne ko kuwa kawai hasashe ne irin na zuciya?. Ta leqa ta sake leqawa amma bataga fuskar ba,sai kawai ta maida dubanta ga fu'ad don ta tambayeshi yana ganin abinda take gani kuwa?. Gani tayi hankalinsa baya wajen,don haka ta sake maida dubanta gurin,saidai kuma a yanzu alluna uku take gani maimakon daya,kuma kowanne dauke da sunanta,hakanan kowanne me riqe dashi ba'a iya ganin fuskarta. Cak ta tsaya tana qare musu kallo,tana jin bugun zuciyarta yana qaruwa. Bataso ya zamanto gizo idanunta suke mata,ta laluba kuma ya zamana ba abinda take muradi ba,bataso ta saka rai akan abinda daga qarshe zai zamanto ba haka yake ba,ta daga yatsunta tana sake irga allon daya bayan daya,a hankali ta samu bakinta da furta. "Huda.....nadra.....haneefa" Murmushi me sauti ya subuce masa ganin yadda ta fadi sunansu a jere a yadda suke. Sautin murmushinsa ya tabbatar mata yana ankare da komai,ya latsa wayarsa ya aike saqo a gaggauce ga saddiq wani irin ruhin soyayya da 'yan uwantaka yana ratsashi. Yaso musaddiq tamkar haka a duniya......a sanda ya tabbatar bashi da wani gata daya rage masa saishi daya......ashe akwai wata halitta daban a gefe dake tsananin kulawa da rayuka har guda uku a matsayinta na diya mace?. Daya bayan daya suka sauke board din,su dinne.....huda nadra da haneefa......sune amma fuskokinsu sun canza daga su hudan data sani watannin baya sun koma wasu mutane na daban da kamanninsu ke nuna zallar jin dadi nutsuwa da kwanciyar hankali. Jikinta duka ya dauki rawa,fuskarta ta gauraya da kalolin emotions har guda biyu,dariya da kuma kuka,ta soma qoqarin kwasa da gudu don ta cimmasu,tana ganin kamar tafiya tayi kadan ta kaita garesu. Caraf yayi ya riqe hannunta. "Bi a hankali......mrs muhammad jadda......bani da tabbacin babu baby ne a jikin ki,still baki da cikakken lafiya......muje na rakaki.....su dinne,zaki cimmasu cikin salama da nutsuwa". " Kai....kain...." Bakinta yana rawa tanason tambaya da samun tabbaci. "Shshssh..... Muje" Ya fada yana mata nuni da lumsassun idanunsa. _Allah sarki....dan uwa rabin jiki_ *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ 111 111 Tun kafin ta qarasa garesu hawaye sun gama wanke mata fuskarta,taqi dauke idanunta daga kansu koda na second guda,tana ganin kamar idan tayi hakan zasu bace mata kafin ta sake bude idanun nata. Suma basu iya jira ta qaraso garesu ba,da wani irin sauri suka tunkarota kowa yana qoqarin fara isa wajenta. Gudun nan daya hanata batasan ta yishi ba sai da ta jita cikin jikinsu,dukkaninsu su ukun qoqari take a lokaci guda ta samu damar rungume kowa. Bata fahimci kuka sukeyi ba sai da suka zube duka a jikinta suka sulale qasa duka har ita din. Sheshsheqa sosai sukeyi kowanne da sunanta a bakinsa. Wani irin sautin kuka ne me taba zukata,kukan dake cike da kewa da qaunar juna irin wadda asalin soyayyar 'yan uwantaka take bayarwa. Ko fu'ad a wannan karon baya yaja ya tsaya yana rungume da hannayensa,kallonsu kawai yakeyi baiyi yunqurin yi ko cewa komai ba,saboda yasan wanne irin ciwo ne zukata sukeji a irin wannan lokacin. Ta rasa sunan wa zata fara ambata?,sai kuma ta saka hannu ta fara dago haneefa auta. Fuskar autan ta sake cika sosai,duk wani kamanninta da ita sun sake bayyana,tayi wani irin haske wanda da alama shine asalin color din fatarta. "Auta......auta kece?" Ta fada wani kukan farinciki yana sake tsinke mata. Kai haneefa ta gyada tana dariya da maqalallun hawaye akan fuskarta. "Nice adda......adda kin qara girma.....adda kin zama balarabiya" Haneefa ta fadi tana shafa hannun sabreen dake riqe da nata hannun. Qaramin dariya daya taho da hawaye ta saki tana maida kallonta ga huda. Hudanta ta sake zama budurwa sosai,abun abun mamaki kaman wadanda aka saka famfo ake hurasu. Kamarsu itama ya sake fita,duk da baikai kamannin dake fuskar haneefa ba. "Adda......ban zaci zamu sake ganinki da wuri ba" "Nima haka adda......" Muryar nadra ta sanyata waiwayawa. Itama nadra din kaman sauran,saidai nata kamannin da ummenta ne suka fito sak kaman an tsaga kara,abinda ya raunata zuciyar sabreen sosai ta miqawa nadra hannu. Ba musu ta dora nata hannun akan na sabreen din suna duban juna. "Nadra?....ya akayi kukayi irin wannan girman?,me kuke ci?" "Komai me kyau adda.....komai mai dadi hamma ya tanadar mana,komai da zamuyi amfani dashi muci ko musha yasha banban dana dubban mutane adda" "Hamma?" Ta tambaya a mamakance,sai huda ta gyada mata kai tana duban fu'ad dake nesa kadan dasu. Kanta ta daga ta waiwaya zuwa inda yake tsayen,zuwa sannan tare da saddiq suke tsaye,batasan maganar da sukeyi ba amma taga yana miqawa saddiq din wani card. "Hammanki adda" Haneefa ta bata tabbaci. Maganan data sanyata dauke dubanta daga kanshi zuwa kansu. Kai huda ta gyada mata still tana qara tabbatar mata. "Ya Allahu ya salamu.....when......and how?" Ta tambayi kanta. Duka yaushe yayi hakan?,duka yaushe yasan da yaran?,yaushe yasan inda suke?,yaushe ya shirya komai?. Ko yawan using da wannan na'urar da yake sanda suna muraaka suit yana da alaqa da shirinsa akan haka?,take taji amsar tambayar tazo mata. Wani kakkaifan abu a kansa taji ya huda zuciyarta,ta lumshe idanunta tana jin yadda yake kwarara cikin kowanne sashe na zuciyarta dama gangar jikinta. "Muhammad fu'ad jadda" Sunansa kadai ya dinga amsa kuwa cikin kunnuwanta. "Amma kun saba alqawari.....kun karya yarjejeniya sister" Muryar nan tasa dake cike da tarin nutsuwa ta ratsa rufaffun idanunta,sanda ta budesu sautin murmushin huda ya sauka a kunnenta. "Wallahi hamma itace.....adda ne ta fara sakamu kuka" Ta amsa masa tana miqewa gami da riqe dariyarta. Idanunta ta bude fes saita samu tattausan tafin hannunsa gaban fuskarta yana miqo mata shi. "Next time sai naci tararku idan kuka sake sanyamin mata kuka......get up my world" Ya fada yana duqawa kadan yasa hannuwansa yana daga kafadarta. Wani sanyi taji yana ratsa sannan jikinta,ta ware idonta a kansa sanda yake miqar da ita tsaye. Fuskarsa fresh kuma normal kaman baiyi wani abu ba,ta laluba labbanta zuciyarta dama kwanyarta gaba daya,tanason zaqulo kalaman da suka dace tace dashi wani abu amma ta rasa. Gyara mata veil dinta yakeyi yana sake rufe mata jikinta gami da jan hannun abayarnata "Wannan kallon.......bakison zuciyata ta huta hala?" Ya tambayeta yana balle mata button guda daya daya zame na abayarta. Idanunta sunyi raurau sosai sun cika da hawaye,ko sau daya so take ya kalleta......koda na second daya ne wataqila zaifi fahimtar girma da martabar abinda yayi mata,don ta tabbatar kalaman baki sunyi qanqanta su isar da abinda takeson isarwar,saidai yaqi ya kalletan har sai daya gama sannan ya zube mata fararen idanunsa. Wani abune da yake yawan bata mamaki,a iya mazan data taba kallon idanunsu ba zata iya tuna mutum daya da idanunshi suke da haske haka ba......koda kwatankwacin nasa kuwa. "Akwai wani abun?" Ya sake tambayarta yana kallonta. Labbanta ta motsa amma sai ya saka yatsunsa biyu ya b'ame mata su. "No need......bana son godiyarki ko kadan......it's my duty......aikina ne na baki duk wani abu da zai baki farinciki......haqqina ne samar miki da duk wani abu da zai baki nutsuwar zuciya data gangar jiki......aikina ne.....dole na ne na matso miki da dukka farincikinki kusa dake.....har yanzu jikinki da dumi,mu qarasa" Ya fadi yana riqe hannunta cikin nasa sannan ya kira haneefa ya saka mata ita a gefenta,ya kira huda ya sakata a daya gefen,yaja nadra baya sukabisu a baya yana mata magana qasa qasa wadda sabreen batasan me yake tambayarta ba. Tuni ta kame a owners corner,tanason ta sake tabbatar da duk wani motsi da xai gayawa kowa ita din isashiya ce. A bude tasa abar mata qofofin lafiyayyar motar,tana shaqar iska d'ai d'ai tana ratsata,tana jin qofofin abubuwan daya kamata ta aiwatar kaman suna bude mata. Tana jin tsaiwar anni a daura da ita,ita da amna da musaddiq da take jira su samu xama sosai tayi masa iyakoki da lamuran annin. Batason duk wani abu da zai ci gaba da sanya kusanci tsakaninsa da yarinyar can me kama da uwarta,zata iya kowanne kalar hauka xata kuma iya cinye komai ta daure har ta gama da matsalar amma banda alaqa tsakaninsa da amna din,don yanzun haka sautin dariyarsa da yarinyar tana jinsa har tsakiyar kanta. "Musaddiq" Ta kirayeshi tana leqo fuskarta daga motar. Sam yana mancewa da wani warning na maamah din,kiranta ya dawo dashi cikin hayyacinsa,ya amsa mata a nutse sannan ya dubi anni. Da ido ta masa alaman yaje ya amsa kiran mamarshi "Ina zuwa" Ya fadi qasa qasa yana takawa zuwa inda take. Kallo take qare masa tun daga
Chapter 129 · 0% Book details