← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 215

Sashe 32

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

fita ko sai na kira masu fiddamin dake?" Ya kuma fada yana ware mata idanunsa da suke da wani irin kyau me jan hankali wanda suka sake fusgar hankalinta. Bai ankara ba bai kuma taba kawo haka zata kasance ba ya tsinceta ta fada cikin faffadan qirjinsa tana neman kai masa kyakkyawar runguma. Baiyi wata wata ba bai kuma sake bata koda minti biyar a jikinsa ya yakiceta ya watsar gefe. Wani irin tafasa zuciyarsa keyi,wanna shine karo na farko da wata mace ta rungumeshi irin haka. "Tashi ki fita thn ranki bai qarasa baci ba,stupid!" Ya fadi a tsawace yana nuna mata qofa. Miqewa tayi tana kade jikinta,duk da ba wani baci tayi ko datti ba saboda gurin fes yake da wata irin tsafta da take ta'ammali da ita a komai nasa,cikin borin kunya tace "Yakice ni daga jikinka baya nufin fidda soyayyarka daga zuciyata......zan tafi,amma kuma zan dawo,zan kuma ci gaba da kasancewa dakai,zan zama cikin kowanne motsi naka har sai na cimma nasara na samu abinda nakeso". Daga wannan ta dauki jakarta tana nufar qofa da dan sauri,qasan zuciyarta da tsoron yadda mode dinsa ya koma,amma abinda takeji a kansa ya danne komai. Iska me zafi ya furzar yana shafa sumarsa da tafin hannunsa. Kwata kwata yaqi jinin mace maras jan aji........yana matuqar son mace me aji.....mace me dan wani tasiri kadan na girman kai,wanda girman kai a wajen mace yana alamta alamu na kamun kai,girman kai yana cikin siffar da akeson mace dashi.....amma a mu'amalarta da maza kamar haka. Komawa yayi saman kujera ya zauna yana fidda numfashi me huci. Yana daya daga cikin abinda yasa ya rasa interest akan mata,yana daya daga cikin abinda ya sanya har yanzu ya kasa gano macen da zata sace zuciyarsa kwata kwata.......saboda yanzun mata yana hangen sun rasa dabi'un nan guda biyu zuwa uku masu tsananin tsada fiye da diamond...... Masu tsananin zame musu ado fiye da adon gold a jikinsu,wato KUNYA da kuma KAMUN KAI. Wayarsa ya dauka ya kira abdus_samad yana qoqarin danne fushinsa,bugu daya tak ya daga "Who gave her permission to enter?" Tambayar da yayi kenan a taqaice. "Am sir......" Ya fada adan daburce don jikinsa yana bashi laifi yayi "Did someone invite her in?" Tambayar ta qarasa daburtashi gaba daya,ya kuma fahimci laifi yayi. "Am sorry sir......am sorry,naga diyan ambassador....." "Keep quite......are you out of your sense?,don diyar ambassador ce?,meye alaqana da ita?,dama akwai wannan tsarin na ku barmin mutane suna shigomin guri anyhow?,meye amfaninku idan haka zata ci gaba da kasancewa?" Ya kasa magana kawai sai haquri da yake faman jera bashi,don tunda yake dashi irin fada irin haka bai taba hadasu dashi ba. Bai jira cewarsa ba ya yanke wayar yana ajiye wani tsaki. Ji yayi sam zaman parlor din ya isheshi,bama parlor din bama,abujan gaba daya,ya miqe yana wucewa bedroom dinsa,cikin jikinsa gaba daya yana jin kamar ya yanke inda nata jikin ya tabashi. Bacin rai sosai yakeji a qirjinsa,duk wani nau'i na sabo ya tsaneshi,sai yau gashi ta sakashi abinda yake matuqar gudu da kaucewa. Yasha shiga harkoki da abubuwan dake cakude da mata,amma yanayin kamewarsa da kuma miskilancinsa yasa suke tsoronsa matuqa,ba wadda take zuwa masa da zancan banza,tun daga secondary school university da tafiyansa service,duka Allah ya tsareshi ya kuma tsare imaninsa,duk da irin farkamakin da yake samu. Yana gaban wardrobe yana sauya kayan jikinsa yaji ana masa knocking,muryarsa can qasa da sauran tasirin bacin rai a ciki ya tambaya "Waye?" "Saddiq ne hamma". "Come in" Ya bashi dama lokacin da yake sanya rigar jikinsa. Yanayin yadda yaji sadiq din ya shigo ya tilasta juyawa yana duban fuskarsa. Sai yabi hannunsa da kallo wanda yake dauke da system "What's wrong with you?" Ya tambayeshi yana tsareshi da idanu. Kasa amsa masa yayi,sai daya samu waje ya zauna daga saman carpet ya ajjiye system din sannan yace "We got the announcement........ana zargin an samu muggan qwayoyi cikin jewelry company dinmu". Ya qarasa fada yana buda masa saqonnin da suka samu daga dukkan kafofin dake da alaqa dasu daya nabin daya. Hannuwansa kawai ya zube cikin aljihunsa yana kallon system din. Yanajin wani yanayi yana zagayashi,hankalinsa nason tashi amma yana gayawa kansa da kansa "All is well" A irin wannan lokutan na tsanani,lokutan da jarabawa irin wannan ke tunkararsa rauni yakan rugo da gudu ya mamayeshi.....a irin wannan lokacin yakanji yana da buqatar wata halittar a gefe da zata same masa qwarin gwiwa......banda qannensa banda farouq da yawan daukan mas'alolinsa yake ganin suna masa yawa,ya kamata ya rage masa daukan matsalolinsa haka.....tun daga quruciya kunnuwan farouq zuciyarsa dama gangar jikinsa suke fama da matsalolinsa.....zuwa yanzu ya kamata ace ya huta.....anni,wata irin rumfa ce sha shirgi ita da abban gaba daya,ya kamata kunnuwansu su samu sassaucin jin damuwoyinsu a yanzu haka da girma yazowa kowannensu.......akwai personal mutum da yake buqata daga gefe da zai zauna a wannan matsayin. "Hamma wannan saqonnin barazanar basa da alaqa da faruwar wannan abun kuwa?". Kai yake jinjinawa sanda yake takawa a hankali yana matsawa daga wajen "Definitely......but I'll make it clear im not Intimidated" Ya fada da wani irin qwarin gwiwa yana dora top saman rigar t.shirt din jikinsa. "Let's go.....ka kira William kace ya samemu a can....." "Amma hamma.....flight isn't ready" "We'll take the road" Ya furta yana riga saddiq yin gaba. Kafin sukai ga isa lagos ya gama shirya dukkan abinda ya kamata ace ya tsara din. Suna dab da shiga garin har a sannan idanunshi biyu,ko daya baiji wani buqatar bacci ko kuma ya huta ba. Yaja qaramin tsaki sanda suka dauki hanyar kamfanonin. Ya fahimci ita kalmar SO ko a meye ta shiga wahala ce kawai da walagigi da ruhi,wannan ya sanya banda soyayyar family dinsa bai taba saka soyayyar komai cikin ranshi ba,sai yanzu gashi kwatsam......kamfanin ya shiga ransa har baisan adadi ba......gashi kuma ya zama abu na farko da son nasa keson zame masa wahala,da wannan ya qara ji a zuciyarsa lallai tabbas ya kamata ya nisanci soyayya iyakar iyawarsa. Duk da sun nuna matsayinsa yafi ya taso da kansa amma ya kauda wannan. Ya karbi duk wani bincike nasu ya dora da nashi. Da gaske an samu wani dan qaramin store cikin kamfaninsa cike da qwayoyin da inda wani me qaramin matsayinne ba shakka sai ya tafi dauri gidan gyaran hali,amma da yake a nigeria muke.....kuma kura ma tasan gidan me babban sanda sai ya zamana dakatar da kamfanin kawai akayi sai bincike ya kammala. Bayajin zai iya bari maqiyansa su kalli faduwarsa da wurwuri haka,wannan ya qara masa qaimin shiga binciken da kansa gadan gadan. Ya fuskanci tarin abubuwa masu yawa cikin case din,wannna ya qara masa qaimi,bai kuma yarda yayi handling case din ma kowa ba. Duka da bacci da cin abincinsa qalilan ne. Amintattun experts investigators din daya aminta dasu kawai suke aiki ka'in da na'in,ba dare ba rana. Bai gayawa kowa abinda ake ciki ba banda anni da yace ta tayashi da addu'a,akwai matsala amma qarama ce ba wata babba ba,haka ya gayawa abba da farouq. Saidai sam hankalin farouq ya gaza kwanciya,don yana dawowa daga seminar dinsa ya biyo bayasa a washegari. Yadda ya ganshi ya tabbatar abun ba qarami bane,don ya nuna har a jikinsa don kuwa ya dan rame kadan saboda rashin bawa abinci muhimmanci. Ya sake sallamawa da miqa wuya kan muhamnadun yaci sunan muhammad din,namijin gaske ne da gaske......daga yadda ya tunkari komai yake gabatar dashi da dukka qarfin gwiwarsa da jarumtarsa kadai ya qara tabbatarwa NAMIJIN DUNIYA NE. Yanata qoqarin dodging komai farouq ya dubeshi. "4weeks without me dude.......have you noticed your appearance?.....check your reflection" Ya fada yana kama hannunsa zuwa gaban concealed mirror din dake wajen. Ya kalli fuskar tasa kaman yadda farouq ya buqata,sai ya saki murmushi ya miqa hannu yana shafa fuskarsa. "Chill out mana dude,nayi settling komai,It's come to an end......My evidence supports my claim....and it speaks for itself,all the fact are on my side,na gama komai gobe zasu saki kamfanin.....abu daya ya rage na gano shine,who's pulling the string" Hannunsa farouq ya riqo yana girmama qarfin jarumtarsa,yana jin inama ya samu irin wannan jarumtar tasa "We'll leave no stone unturned,we'll find him together" Rungume kafadar farouq yayi,yana sake jin qaunarsa cikin ransa. A gaba ya sakashi ranar,yasa ya ajiye komai tunda bincike ya kammala. Da kansa ya zauna ya masa gyaran fuska da sauran wasu abubuwa,yana masa suna hira yana bashi labarin nasa progress din da aka samu bayan seminar din. Duk duniya da farouq kadai yake irin wannan sakewar. Ranar duka tare suka qarar da ita,sai dare sannan kowa ya wuce makwancinsa,da zummar gobe da kamfani yaci gaba da aiki jibi tabbas dole su wuce gida,wanda sam bai fahimci meye ma'anar matsawar da farouq din yayi bama. Ya dauki wayar da zummar kashewa ya tarar da tarin miscalls da kuma saqonni,guda daya ya duba ya fahimci wacece. Fareeda ce....saqo bayan saqo kamar bata da wani sauran aikinyi sai tura masa da saqon. "How did she get ahold of my number?" Ya tambayi kansa da kansa. Tunawa da yayi da mahaifinta ya sauqaqe masa wahala,yasan samun numbersa zai zame mata wani abu kenan me sauqi. Tsaki yaja ba tare da yabi takai ba,ya kashe wayar ya kwanta. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _ZAFAFABIYAR_ 29
Chapter 32 · 0% Book details