Sashe 155
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da ameenatu,a sannan zata gwadawa hajja yadda ake wasan kura da rayukan dan adam. "Hajja......karki tunkari.fadan da bazaki.iya qarasashi ba......ki lallaba masarautar cikin gidanki dake gareki,ki qarasa mulkinki sannu a hankali,ki kuma jirayi randa naga damar 'yanta miki d'iyarki" Wata dariya data saka numfashin maamah tsaiwa na wucin gadi ta saki,sai da tayi me isarta sannan tace. "A a'ah......mariyatul kibdiyya......wai ni bakisan abokin mutuwa nake nema ba?....,to bari kiji.......daga yau zuwa gobe na baki ki maidomin da d'iyata gaba na,ko kuma wannan boyayyar fuskar dake gefena a bugun shafin farko na jarida da kowa keson ganinta ta bayyana kanta da kanta.....aikin fahimta ko?" Daga wannan hajja bata jira komai ba ta kashe kiran. Daga zaunen da take amma sai taji tana jin jiri.......me yasa komai yake neman ya kwabe mata lokaci guda?,kowa adadin awanni yake deba mata cikin umarni da kuma gadara?,wai me yake faruwa ne?. Daidai nan taji muryar driver dinta yana fadin. "Mun iso gida.hajiya" Kanta ta daga tana kallon gidan,batasan sanda suka iso ba kaman yadda batasan sanda suka shigo gidan har ya iso parking lot ya tsaida motar ya kuma kasheta ba. Hannu ta saka ta bude murfin motar,a hankali taja jikinta tana fita a motar,saidai ko Cilakken tsaiwa batayi ba ta yanke jiki ta fadi a wajen hankalinta yana gushewa. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ 132 https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX Da sallama farouq ya shigo,sabreen dake tsugunne gaban fu'ad din tana gyara masa nails dinshi na qafa duk da fes suke.....amma tsabar bayason tayi nesa dashi ya tsiro mata aikin ta matsa kadan tana amsawa. "Sannu da aiki addanmu" Ya fada yana jawo kujera ya zauna yana dubanta. Murmushi tayi a kunyace tana amsawa. "Yauwa BB....sannu da qoqari....Allah y qara zumunci.....ya saka da alkhairi". " Ameen dai.....dama wani abun saboda ke akeyinsa ai ba don mutum ba" Ya qarasa fada yana jifan fu'ad da harara wanda yayi relax abinsa jikin kujera kaman badashi yake ba. Miqewa tayi da zummar basu guri. "Kin gama ne?" Ya fada muryarsa can qasan maqoshi. Kai ta girgiza tana satar kallon farouq tana masa alama dashi. Ya fahimci me take nufi amma ya basar,don haka ta buda baki. "Zanyi waya dasu huda kafin ku kammala". Agogo ya kalla da narkakkun idanunsa. " Minti goma ki dawo ki qarasamin" "Okay sir" Ta fada a girmame ta qarasa tana daukan wayarta ta fice. Farouq bai jira ta kammala fita din bama ya soma fesar da abinda ke ransa. "Zuwa nayi na maka sallama". Dariya ya taso ma fu'ad amma ya danneta,sai ya miqe sosai ya zauna yana ware idanunsa akan farouq "Ina zaka kuma?" "Gida zanje ayimin aure.....bazan zauna na mutu na tashi a gafiyar lahira ba". Wannan karon dariya ta gasken gaske ya bawa fu'ad,har wanda ke parlor din zai iya jin sautinta,kalan dariyar daya jima rabonshi da irinta. "Bafa inda zakaje dude.....ko zaka hadiyi zuciya saika gama jinyata ka cikasa ladanka". "Lada irin naka ne banaso......ina samun ladanka kaima kana samun naka ladan ko?....bazan iya ba....ni yanzu wallahi kafi qarfina" Kai ya jinjina yana shafa sumarsa. Da gaske yasan farouq aure yakeso.....kuma koda shine yake a matsayin farouq din yana sanya auren mace kaman sabreen bayajin zai iya haqurin da yayi ma.......baiga abinda zaiwa farouq ba sama daya tabbatar da aurensu a daidai date din da aka saka.....baya jin zai yarda ya zama silar daga bikin farouq koda na kwana daya ne. "Ka yiwa pilot nassar magana......ayi booking barinmu taiwan zuwa Nigeria.......inaso larabar nan mu koma gida". Waiwayowa farouq yayi yana kallonsa da mamaki. "Ina zakaje kana jinya?,ina zakaje bincike kuma bai kammalu ba?". Murmushi ya saki me taushi yana duban farouq din,duba irin na 'yan uwantaka ta jini me cike da dumbin qauna. "Bincike ya gama kammala farouq......fareeda keda alhakin komai......ta samu nasarar aiwatar da komai dinne ta silar maamah data bata full details din......abu daya da ban sani ba shine.....bata da masaniyar abinda fareeda zatayi dashi?,ko tana da masaniya?,tayi hakanne dukka cikin tsare tsarenta data dauki shekara da shekaru tana gudanarwa?" Ya qarasa maganar duk wata walwala da yake ciki tana sulalewa daga jikinsa. Ba farouq kadai ba,hatta sabreen data dawo da niyyar daukan slipper dinta ta zagaya koda veranda din dakunan saita tsaya tana komawa da baya. Wani irin tausayinsa yana sasuqar zuciyarta. Yadda walwala tayi qaura daga fuskarsa karo daya ya tabbatar mata a yanzu a rayuwarsa bashi da sauran wani ciwo daya wuce MAHAIFIYARSA. A jikinta ta dinga jin cewa......She has to put in effort to help him overcome his past,ya kamata ta sake matsawa sosai cikin rayuwarsa.....yana buqatarta fiye da yadda take hasashen zai kasance. "No dude.....no.....kada kayi wannan tunanin.....ko yaya ne.....ko yaya kuke da maamah uwa ce.....bana tunanin kowanne kalan hali ne da ita zata iya bada qofa ko daman rabaka da rayuwarka". Idanunsa da suka sauya kala ya maida kan farouq yana dubansa. "Farouq.....duk yadda zan gaya maka abinda ke nan gurin..." Yayi nuni da qirjinsa da yatsansa. ".....ba zaka fahimta ba.......mun rasa MAHAIFIYA.....MUN RASATA RASHI NA HAR ABADA......saidai na yadda nayi kuma imani,yana cikin rashin cikar kamalar ni'imar mutum cikin DUNIYARSA......cikakkiyar ni'ima tana lahira". "Duk da haka dude please......ka ajiye wannan a side" "Na ajiye farouq......fareeda zata girbi duk abinda ta jima tana shukawa.....she must pay.....bawai iya kaina kawai ba". Kai farouq ya jinjina,wani aikine daya shirya gudanarwa da kansa,sai gashi fu'ad din ya rigashi. "But dude.....inaga kaman ka qarasa warkewa....." "Noooooo......dole farouq dina ya shiga qwaryar manya as soon as possible.....ta iya yiwuwa ya rage zargina.....ta iya yuwuwa kuma ya daina katsemin muhimman lokuta na da DUNIYATA". fuskewa farouq din yayi yana sosa kanshi "Eh to.....kaman tafiyanma zaifi mana Alkhairi gaba daya.....don bana tunanin idan ka zauna a nan dinma warkewar arziqi zakayi,gadon ya muku kadan gwara a koma gadon gida". Toshe bakinta sabreen tayi,salin alin ta debi kayan kunyarta taja jikinta tana barin gurin tun wani a cikinsu bai ganta ba. Salati drivern ya saki,hannuwansa bisa saman kansa yana sake sakin salatin gami da cewa. "Ku kawo dauki bayin Allah......hajiya ta zube". Dukka hankalin ma'aikatan gidan ya tattaru a kanta,saidai har matan ciki tsoro da shayin dagata suke,basusan haqiqanin abinda zai biyo baya ba idan suka dagata bayan ta farka. "Dole haka za'a ceci ranta,kome zai biyo baya ai ba za'a barta ta mutu ba ko?". Malam sa'adu me gadi ya fada. "Matso ke raliya ki kama musu ita" Ya fadi yana matsawa baya. "Gashi ba kowa gidan Alhaji hamza ballantana muji ina ake kaita" Malam sa'ad ya fada yana duban driver din. "Kowanne asibiti ma kaita za'a yi tunda abune na gaggawa.....ki shigo mu tafi" Yace da raliya yana shigewa cikin motar. Tuqi yake a gaggauce yana tsoron kada ta mace a hannunsa,babar babban mutum irin me jadda ta mutu a hannunsa tabbas ba qaramin tashin hankali bane. Tafiyar minti shabiyar suka samu wani private suka tsaya a nan,aka dauko wheelchair aka dauketa akai,har a sannan bata dawo daidai ba. Sai da suka kashe minti kusan sha biyar a kanta sannna ta farfado,suka cire mata oxygen suka daura mata ruwa da suke saka ran minti talatin ya qare sannan likitan yace zaije ya dawo kafin ruwan ya qare. Kanta kawai take mirginawa tana jin qirjinta yana mata wani ciwo,duk inda ta juya fuskar raliya data drivernta kadai take gani,har bacci ya saceta. Still data farka din ba wasu sabbin fuskokin saisu din dai. Wani abu ya tsaye mata a wuya,wasa wasa tana shirin kamanceceniya da ts intacciyar magen da bata da wani gata. A hankali ta sauke dubanta kan wata mata dake kusa da gadonta,wanda su biyu ne kacal dama a dakin. Yara hudu ne tsaye a kanta,tana zaune saman gadon,daya a hannun damanta.....daya a hagunta,dayan yana tsaye saman kanta yana bare mata ayaba yana bata tana ci,dayar tana saman kujera gaban gadon nata riqe da robar yoghurt tana jira ya gama bata ta miqa mata. Hira suke a tsakaninsu,kowanne fuskarsa dauke da walwala duk da cewa jinyar mahaifiyarsu sukeyi. Tana gama ci ya karbi bawon ya jefa a Dutsbin,zai karba yogurt din daga hannun ta zaunen ta hanashi. "Saika kwashe ladan duk kai kadai,nima inaso" Ta fada tana kai roban bakin mahaifiyartasu. Idanu maamah ta dauke tana runtse idonta,wani irin bacin rai yana ratsata. Tasan koda kwatar kwatar kwatar kudin fu'ad duka yaran matar basu kai ba.....amma yadda suke tattalinta da nuna mata qauna da kulawa kadai abun kallo ne.....ita gata ta qare da zama 'yar kallo,cikin rayuwar kadaici da rashin wani sashe da zai tallafeka. "Allah ya isa ameenatu.....Allah ya isa" Ta fada a sarari tana ji har zuciyarta anni ta mata cutar da bazata taba iya wankuwa daga ranta ba.....hakanan kowacce kalar fansa data shirya dauka ba zata iya ramawa daidai da abinda tayi mata ba. Daga raliya har driver din da kallo suka bita,saidai babu bakin magana,daidai nan likitan ya shigo. "Ta farka ko?" Ya fada cikin kulawa yana dauko file din gami da sake duba abinda ya rubuta,ya qara wasu rubuce rubucen sannan ya ajiyeshi yana dubanta. "Hajiya ki rage saka bacin rai a zuciyarki.....ki rage saka damuwa a ranki,kina da hawan jini bai kamata ki dinga zama cikin damuwa ba.......irin wannan gaskiya yana iya haifar da matsala kala kala,ba'ason abinda zai dinga sanyawa jinin yana hawa haka ta farat daya....kuyi qoqarin ganin ta kiyaye" Ya qarasa maganar yana dubansu raliya ganin maamah din taja idanunta abinta ta kulle. "Tom.....in sha Allah" Raliya ta fada a sanyaye a ranta tana cewa mu asuwa?,indai taji da kunnenta ai shikenan mun kubuta. "Kuna iya tafiya gida.....amma da zarar taji wani abu daban ayi hanzarin dawowa,saboda yanzun takai matakin da dole a dinga yawa checking up nata". "Mun gode likita" Driver ya fada bayan ya karbi takardar magungunan daya rubuta mata. Yana shirin tada motar ya dan waiwayo "Ya za'a yi da magungunan nan hajjaju?,zamu siya ne a hanya ko za'a kawo?". "Kai sagiru" Maamah dake a qufule da yadda suke jaddada mata cutar hawan jini ta kira sunansa. "Naam hajiya". "Ka fita daga ido na......hawan jinin banza hawan jinin wofi?,maqaryatan banza wanda mutum baya ciwon Allah da annabi?,shekarata nawa a duniya hawan jinin bai sameni ba sai yanxu ina fafutukar cika burikana?,Allah ya tsinewa wanda ya fasa cewa ina da hawan jini.......hawan ruwa ne dani.....bani takardar nan nan" Ta fada cikin