Sashe 131
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
alhj muhyidden ya nema inda zasu hadu. A girmame yace zai sameshi a masaukinsa,hakan ya yuwa fu'ad nauyi,don babba ubane a wajensa,don haka duk wanda ya jibanceshi yana masa kallon uba shima. "Ka zabar mana guri,zan iskeka in sha Allah ko a ina ne". Nutsuwar fu'ad da hankalinsa ba wani baqon abu bane a wajensa,don haka cikin masallacin yace su hadu bayan sallah isha'i,ya duba lokaci sai ya yanke daga sallar la'asar din yayi zamansa har isha'i acan yayi jiransa,don yana da tarin addu'o'i daman da zaiyi. "In sha Allah zan zauna ta babus salam". Ya fadawa alhj muhyidden. A nutse ya dauki casbaharsa,ya sake feshi jikinsa da lallausan turarensa sannan ya saka wasu loafers masu taushi marasa nauyi ya fice a dakin. Ita daya cikin dakin tunani kaman zai fasa kwanyarta,tana zaune daga gefan gadon,madarar almara'i ce a gabanta tana tsiyaya da kadan da kadan tana sha,don batajin abinci xai wuce ta cikinta. Kwata kwata jinta take kaman akan qaya,lissafin kwanakin da zasuyi a qasar takejin sun mata yawa sun mata kuma nisan da kamar ba zata iya jira ba. Ganin yaran ya sake gigita tunaninta,tun sanda ta samu ta sabule yaran daga hannunta dama tana tare dasu?,ko wani gurin ta kaisu?,ya akayi suka kasance a nan gurin?. Tunaninta ya katse sanda akayi knocking qofar dakin,idanunta ta daga ta kalli qofar,tasan ba kowa bane sai fu'ad din,murya a cunkushe tace "Shigo" Qofar ya murda ya tura ya shigo,don bayan fitar musaddiq tace yabar masa qofar a bude. Kallo daya yayi mata yasan dai kaman kullum ne,kaman yadda aka saba wani abu da ya shafi buqatar qashin kanta ya sanya ta kirashi,saman dressing mirror ya qaraso,ya dosana kadan ya zauna samansa yana dubanta. "Gani" Ya fada a nutse yana shirya jin komai da zai fita a bakinta. "Muhammadu......wai nikam duniya na haifawa kai ne?,wanne irin wauta da hauka kakewa rayuwarka?,sam ba ruwanka da tattala rayuwarka?,ba ruwanka da sanin ya kamata?,ka zama baitul mali ka maida kanka bayin wasu?". Dukka maganganunta tana yinsu ne cikin fada zafi da kuma daga murya. A nutse ya lumshe idanunsa sannan ya budesu. "Yanzun me akayi?,me ya faru?" Ya tambayeta a nutse yana qare mata kallo. Bayason ranshi ya baci ko kadan,yanayin abubuwan maamah suna neman fara ta'azzara,shi daya yasan me ya adana a zuciyarsa daya shafeta,sirrika masu nauyi da tsanani wanda ita kanta batasan da hakan ba. Ido itama ta zuba masa,saidai nauyin nasa idanun yafi nata,dole ta janye idanun nata. Tanajin zallar rainin hankali da wayo a al'amarinsa......tanajin wani irin ciwo da yadda ya gagara zuwa hannunta tamkar ba ita ta haifeshi ba. "Tuni na dade da sanin ni din marainiyar wayonka ne........wadannan yaran daka debo meye alaqarka dasu da har ka fara barnatar da dukiyarka a kansu?" Ta tambayeshi a zafafe. Idonsa ya dauke yana qoqarin jawo sabuwar iska zuwa hunhunsa,al'amarin maamah yana daure masa kai maqura......tana yin abubuwa da zummar ba wanda yasan kalarta ta badini a nata hangen?. "Maamah......nayi tunanin kece me bawa wani labarin alaqar dake tsakanina dasu ko?,a wajenki na fara sanin dacewar kulawa da qannen matarka,na dauka idan nayi hakan nima wani abune me kyau nayi?" Yadda ya amsa matan ya mata wata bulala data ratsata matuqa,shuru ya gifta tsakaninsu na wani lokaci,wani sashe na zuciyarta yana gargadarta "Ki kula da dukka amsar da zaki bashi.....akwai.magana cikin maganganunsa". Abinda wani sashen yake nanata mata kenan. " Muhammadu.....ka saurara da kyau ka jini,qannen matarka ko wani abu makamancin haka ba damuwata bane......ba ruwana da alaqarka dasu,bana buqatar wata hidima tsakaninka dasu,wannan maganar da gaske nake gaya maka ita,tunda kai ka zama abinda ka zama,bazan sanya ido mata su sakamin yaro a tsakiya sai yadda sukaga damar yi dashi ba......bazan lamunta ba,tun wuri ka saki dui wata hidima tasu,banaso na sake ji ko na sake gani muddin kana neman albarka daga wajena". Wata qaramar dariya ta taso masa amma.ya kwantar da ita ta hanyar lumshe idanunsa,ya jinjina kanshi da kyau mamaki yana sake cikashi. "Kana jina?" Ta fada da mugun zafin da takeji a ranta. "Maamah.....cikin arziqin da Allah yayimin......ina iya daukan dawainiyarsu data danginsuma gaba daya ba tare da komai dana mallaka ya samu matsala ba......dukka mutumin da ka kawoshi nan wajen yayi ibada kana da lada na musamman,duk aikin alkhairin da kayi asalinsa kana da lada daidai da wanda yayi aikin ba tare da an tauye ladan kowa ba.......maamah......tabbas inda albarkar uwa ita ke sawa yaro ya rayu.....ba shakka da tuni mun jima da amsa sunan GAWA,so inaga ba matsala bane ka zama silar sanya farinciki a rayuwar wani......dukiyarmu da kason wasune dole a ciki da ubangiji ya sanyata cikin tamu.....ya zama dole ka raba ka bawa kowa don fita haqqinsu da ubangiji ya dora maka.....ina fatan ba wani magana a ciki daya bata miki" Ya qarasa fada yana miqewa. Mutuwar zaune tayi kalamansa suna bata mamaki me tsanani,kasa ce masa komai tayi har ya fara takawa zuwa qofa. "Muna kusa da masjid nabawi,dukka sallolinku zaku iya qarasawa kuyi a ciki.....ni na wuce sai zuwa dare" Ya qarasa fadi yana ficewa cike da fatan kada ta sake cewa komai din bare ya tsaidashi. A bakin elevator ya samu su musaddiq,sai kawai suka wuce zuwa masallacin. Suna tattaki a qafa yana sauraren hirarrakinsu,yayin da nashi Hankalin yayi nisa zuwa wani guri na daban.