Sashe 5
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read
A nutse ta daga kai tana kallon hajjan
"Na tsani matsala ko akasi hajja......musamman a wannan matsayin da nake kai a yanzu......me zanyi da ita ballantana na buqaci sharhi a kanta?,bana buqatar dukkan wani jawabi da zai alamta min FADUWA ko MATSALA akan cikar burina a yanzu.......inaji a jikina da raina cewa......zan iya kauda kowacce matsala da zata tunkaro muddin na samu nasarar tsallake wannan matakin da muke kai a yanzu......da qwanjina....da kuma fikirata". Jinjina kai kawai hajja keyi.......tanason taji wanne tanadi da tsari tayi akan hakan?,amma kuma bataso ta zafafa tambaya akai har maamah ta zargi wani abun,saita tattarewa ranta komai tana jiran lokaci.....domin kuwa ta san cewa qwace goruba a hannun kuturu ba abu bane me wahala ba.
********Abune sananne a wajen kowa......sharar biki da yawan maganarsa a bakunan mutanen mu ya ta'allaqa da suna da sharar iyali dangi ko zuri'ar da za'a gudanar da bikin diyoyinsu. Hakan itace ta kasance akan MUHAMMAD FU'AD JADDA mamallakin JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES.
Daga qishin qishin zuwa samun tabbacin tasowar maganar aurensa,wanda tabbacin ya samu ne daga yadda farouq musaddiq saddiq da uban family alhaji hamza kibiya sukewa bikin shiri na gasken gaske.
Daga abokansu saddiq maganan ya fara yaduwa,kafin kace meye wannan labarin ya fara kewaye kowacce kafar sada zumunta.
Duk da a qurataccen lokaci labarin ya fasu.....to amma labari ne me dumin gaske daya bawa mutane da dama mamaki.......ya girgiza zukata da zuciyoyin 'yammata da dama......musamman yaran masu kudin da suke kwana su tashi da mutuwar sonshi......suke kuma da qaqqarfan hope din samun shiga a wajensa kodon matsayi da mahaifansu ke dashi......walau na dukiya ko na siyasa......ko kuma kasancewarsu abokan kasuwancin gold da diamond dinsa.