← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 215

Sashe 82

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

sanda take kawo maza gidan abokan kasuwancinta da suke siyan shaddodin da ta soma business dinsu ba,baisan adadin yawan dukan da yasha a kansu ba......saboda muddin zaka sanya qafarka a gidansu,to shi kuwa zai kafe ya cake a qofa ya hanaka qarasawa ciki. "Babanmu baya so......ya hana maza shigar masa gida,ka koma ka aiko qanwarka ko yayarka" Wadannan sune lafuzzansa a yayin da fuskarsa kan cika da wani irin fushi da zafin zuciya. Kusan baki suke sakewa,kusan duka duka shekarunsa a sannan ba zasu wuce goma sha daya ba,amma zuciyar manya gareshi,zuciyar data kubuta daga dukkanin tsoro saboda kare martaba da haqqin mahaifinsa. Wani lokacin idan ta jawoshi ta daka ta daka,abbansa dake daki kwance yana jiyya shi zaita kiransa,shi zai lallasheshi,yakan ce "Komai na duniya me wucewa ne me babban suna.....komai kuma haquri ne yake zama silar cin nasararsa......ka daina bari ana tabamin lafiyarka me tsadar nan kaji?" Sau tari duk kalan dukan da zata masan ba kasafai ya fiya kuka ba,duk da cewa duka ne ba kadan ba,wani lokaci harda abinda bai kamata ayi dukan ba. Idanunsa saidai suyi jajir,yayita hadiyar yawu da wani irin tsauri "Abba......gidanka ne fa,ta yaya kana kwance zasu dinga tsallakowa suna shigo maka?" Murmushi yakan yi,duk da yakan tsinci ciwo cikin murmushin nasa "Watarana sai labari me babban suna". Ire iren wadannan hirarrakin da abbansa har yau ya kasa sabawa da tunasu,har yau ya kasa jin Normal ne a rayuwarsa,har yau kansa baya iya jure tunasu,duk sanda sukazo masa sai yaji kaman kansa zai tarwatse,sai ya sakejin wani abu yana sanya nisa me tarin yawa tsakaninsa da maamah din,yakan ji kaman bazai iya qara idanu ya kalleta ko ya mutuntata ba......amma ta wani fannin.........uwa data cancanci a kirata mahaifiya irin ameenatu anni......itace ke riqo da hannunsu a ko yaushe,ta kuma qarfafesu da yi mata biyayya. Rana daya daya fahimci ta fara sana'ar dalilin aure,adadin maza da matan dake kai kawo a gidan suka dadu,a ranar ya yiwa wani mummunan rotsen da da qyara aka kashe maganar a police station. Ranar nisan kwana ne kadai ya kawoshi yau da ake magana,don ta sakashi a daki ne ta masa wani irin duka da sai da ya daina numfashi,tun abban nasu dake daga kwance ba daman tashi ya ceceshi yana kiran sunanta gami da qoqarin dakatar da ita,har yawun bakinsa ya dauke tsaf,yayi shuru ya zubawa sarautar Allah ido,yana jin sautin dukan da maganganunta,amma baya iya jin koda tarin muhammad. Yasan halinsa.....sha wuya ne dake iya shanye zafi da tsananin duka,yasan kowanne irin nau'in azaba take masa bazaiyi magana ba. "Me shegen baqin hali irin na ubansa.......baka isa ka hanani neman kudi ba wallahi,yadda talauci ke neman kai ubanka ramin qabarinsa tun lokacinsa baiyi ba......ni bazan zauna talaucin yayi ajalina ba". Qarshe dai musaddiq ya aika ya dinga zuba masa ruwa kafin ya farfado. Ta dauka zai rusuna daga ranar,amma sai taga kaman ma bashi ta daka ba,sai ya canza sabon salon kora da hali wajen yayyanka musu takalmi,karta mota da sace tayoyin motar ko na babur.......still marasa haquri a cikinsu police station suka.kaishi da qyar ta karboshi,zuciyarsa kuma na a tsaye bai rusuna ba,dolen dole ta tattara ta canza sana'a,waccan din saidai tayi a wani wajen daban amma ba cikin gidansu ba. Ajiye roban maca root din dana ginseng farouq yayi yana kallonsa. "Amma yallabai......wadannan abubuwan biyu kaman suna enhancing libido fa.....and..... ". Wani kallo fu'ad ya watsa masa da idanunshi da sukayi laushi qwarai,ya miqa hannu yana fusge container din ya ajiye a gabansa "Baka lura kuma yana boosting energy ba?" Ya fada cikin jin haushi. Dariya sosai ya qunshe farouq din yana gyada kai kaman qadangare "Yes.....yes na gani,kaman kai kenan da kayi loosing energy dinka ko?.....wannan bazai boosta maka komai ba dude.......you need a......." "Zip it" Ya katseshi da kakkausan kallon nan nasa. Shikam farouq bai gama maganansa ba,baiga abinda zai sanya a hanashi fadin abinda yai niyya ba,sai ya janye baya yana daga kafadu. "Duk wani abu da zai maidaka namijin gaske you're Comsumpting......but ka kasa kunna engine din kadan......" Bai qarasa ba ya cire spoon din cikin mug din ya jefeshi dashi,abinda ya sanyashi kasa qarasa maganan......amma kuma ya kece da dariya,wanda shigowar anni parlor din ya dakatar dashi daga dariyar. "Farouqu.....zoka miqawa muhammadu ya dubamin wannan address din.........wata qawata ce muna magana dazu ashe sun shigo suma". Karbar address din yayi ya kalla,bai gane gurin ba don haka ya miqawa fu'ad. "Few kilometers ne tsakaninmu,zaki je ne anni?" Ya tambaya yana dubanta. "Eh amma sai wajen gobe nake tunani.....tunda yau kaman naji amna tana fadan inda zasuje,ba zaa bar gidan ba kowa ba duk da ba wani abu bane". Kai ya jinjina ya ajiye takardar,sannan ya daga mug dinsa yana shanye ginseng tea dinsa abinsa,ba tare da ya maida kai ga kallon da farouq yaketa binsa dashi ba. Dukkaninsu farouq ya xuba a mota suka fice. Sosai suka zaga garin,guraren da sukaje sun kusa biyar,amma duk da haka amna bata gaji ba,fadi takeyi "Ya farouq.....don Allah mu zaga Maldives gaba daya kafin mu tafi,tunda island ne baida girma can can". Dariya musaddiq ya bushe dashi yana kallonta "Kinsan yawan guraren da suke dashi kuwa amnee......a qalla fa gurare dari da tamanin amnee,yaushe zamu iya zagayeshi?" "But......amma please BB,gobe ma ka fita damu,inason naci rihaakuru fish paste.......kifin Maldives please ya musaddiq" Ta fada tana narke murya. "Ki bani cin hanci mana saina roqar mana shi,harda traditional market dinsu.......rannan naga suna saida abubuwan gargajiya sosai.......i assured zakiji dadin gurin" Maganan musaddiq ta sake gigita amnee,ta dinga roqar farouq,har sai data saka sabreen a ciki. "Please BB farouq......a taimaki autan anni mana" Sabreen din ta fada da sassanyar muryarta dake da wani irin nutsuwa. Murmushi farouq ya saki,tana da kima a idanunsa da martaba me yawa,yana ganin mutuncinta sosai saboda yanayin nutsuwarta da kamun kanta. "An gama tunda.matar.oga ta saka baki" Dariya ya basu dukkaninsu har ita sabreen din sai data murmusa kadan. Har yau ya kasa yarda ko sau daya da binciken fu'ad a kanta......baisan meye dalili ba,duk da ya sani shi din mutum ne mara gaggawa akan kowa da komai......amma gaba daya halayensa sun canza a kanta,bazaice kuma ga wani dalili babba guda daya ba. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ Kusan dare ya soma nisa sanda suka isa gida,basu kuma lura da hakan ba sai da suka shiga parlor din gidan suka sameshi zaune saman qananun sofas din dake a falon. Yau idanunsa suna saye cikin farin glass wanda hasken allon system din gabansa ya sake fidda hasken kwalbar glass din. Kallo daya farouq ya masa yasan ta baci,ba kasafai ya fiya amfani da glass din ba sai idan idanunsa suna masa wani iri,don yana zuqe hasken kowanne abun amfani kafin ya samu shiga kai tsaye cikin idanun nasa. Gaba dayansu kowa sum sum ya soma shigewa cikin falon yana dosar qofar dakinsa. Mamaki ya cikata ganin har suka tako veranda din farko na gidan sunata karadi abinsu kuma cike da karsashi......amma da ganin wanzuwarsa kowa ya kama kansa. "Sai da safe" Ta tsinci muryar farouq da shima ya kama kansa zuwa dakinsu,abinda ya sanya jikinta yin laqwas itama ta qara hanzari zuwa nasu dakin ganin kowa ya fashe daga parlor din. A gaggauce ta shige toilet da duka kayan wankanta,tayi wankanta ta kuma shirya a can,tana fitowa kuwa ta nade saman sofa din data kwana jiya akai tana curewa waje daya cikin comforter din data dauke. Bawai sanyi takeji ba ko wani abu,kawai tanason takurawa kanta ne tayi bacci kafin ya shigo. Bata jima da kwanciya ba kuwa taji shigowarsa,ya ajiye komai a muhallinsa ya taka zuwa toilet. Da alwalarsa ya dawo dakin,kamar jiya ya shimfida abun sallah ya fara sallolin da batasan sanda ya gamasu ba,don gajiyar da tayi yau din ya dinga sassauke duk qashin jikinta gajiya tana fita.
Chapter 82 · 0% Book details