← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 205 OF 215

Sashe 205

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Cikin kwanakin kwanciyar hankali da nutsuwa ta samu ga kowa,ci gaba ta fuskokin rayuwa kala daban daban.
Wata irin soyayya ake murmushewa cikin gidan me jadda me license,irin soyayyar da yaran da suka fito ma daga jikinsu saidai a sanmusu. Tsakanin DUNIYOYIN guda biyu wani irin dangantaka ce me qarfin gaske.....wadda ta gwada musu lallai WA YASAN GOBE? banda Allah?. Wata irin DANGANTAKAR ZUCI me tsakanin qarfi da power,wadda take sake basu yaqinin ABADAN ba wanda zai iya rayuwa ba dan uwansa. Sau da dama idan suka zauna labarin rayuwrsu ta baya suna jinjina lamarin ubangiji kan yadda ya tsara KUNDIN QADDARAr junansu,wani ALQAWARIN ALLAH ne wanda baya tashi. Komai na sabreen din tana qoqarin saitashi ya zama daidai da ALQIBLAr fu'ad din,komai nata tana qoqarin ganin bai saba da muradi da abinda me jadda yakeso ba. SIRADIN RAYUWArta kaf akan gidanta ne da yaranta,ta zage sosai wajen koyan abubuwa da dama da zasu maidata cikakkiyar matar gida,irin matar gidan da soyyayarta da kulawarta ke tsayawa a zuciyar mijinta.
Duk wata DABI'AR ZUCIYA da tasan zata kawo rauni a mu'amalarta da fu'ad tayi qoqarin nesanta kanta da ita,ta sake qoqarin zame masa GURBIN IDO ta fannin mahaifiya dama mu'amalarsa tako da yaushe. Kusan duk bayan kwana uku ko zataje ko bazataje ba ta koyawa faud daukan yaran bayan sallar ishai suje su gaida maamah. Hakan yana sanya maamah cikin farincikin da har baya kasa boyuwa saman fuskarta,tana jin yaran a jikinta qwarai,can qasan zuciyarta kuma idan ta kalli mahafinsu takanji kaman ta zama butulu KUFAN WUTA a wani zamani can baya daya wuce. Tun zuciyarta bata gaya mata harta fara gayawa kanta da kanta cewa A RUBUCE TAKE qaddarar kowanne bawa,ba wanda kuma ya isa ya sauya qaddarar wani face marubucin qaddarar.
Sabreen zata iya cewa ita din tana daya daga cikin matan da suka qaryata kalmar nan ta NAMIJI TABARMAR K'ASHI. Mu'amalar fu'ad da komai nasa na musamman ne kuma ya banbanta dana sauran maza. Duk da cewa GUDUN K'ADDARA GUZURIN TARAR DA ITA amma tayi imanin cewa addu'a tana iya sauya qaddarar bawa......tana fatan yadda ko yaushe ta sanya goshinta a qasa take roqar Allah madawwamiyar lafiya da zaman lafiya a gidanta.......ta kasance ita daya a rayuwar fu'ad din a matsayin matar aure,tana da yaqinin Allah bazai juyar da addu'arta ba duk da tabbacin data samu daga bakinsa.

Cikin dim light din dake kai kawo a dakin ta qaraso gabansa,sanye da wata sassalkar rigar bacci data qawata surarta dama fatar jikinsa. Duk da sau daya ya daga kai ya kalleta amma sai data fusgi hankalinsa,ya kalli agogo ya maida dubansa kanta sanda take tsugunne gabansa tana zuba masa hadadden kunun ayar data koya,kunun da tunda ta koyeshi ya zame masa JARRABI kullum sai yasha shi.
Sai data sake masa murmushi sannan ta miqa masa cup din,ya miqa hannu da nufin karba yana cewa.
"Inda malami kika saka yayimiki aiki akan soyayyarki a zuciyata,tabbas dana qara masa kudi ya qara tsananta aikinsa,don nasan babu me mace irin tawa a duniyar nan".
" Hamma....sonkai?" Ta fada da muryarta me sanyi,wadda shi daya take maidawa ita haka a kebantaccen guri irin wannan. Zai bata amsa zafin da bayan hannunta yayi ya dauki hankalinsa.
"Subhanallah.....zazzabin nan wai bai tafi ba?" Ya tambaya cikin tsananin damuwa yana ajiye cup din hannunsa.
Kai ta gyada masa a shagwabe
"Bai tafi ba hamma....."
"Bari na yiwa doctor mubeena waya ta shigo ta dubaki......zazzabin nan ya isa haka nan". Tasan koda tace masa ya bari bazai bari ba,yana damuwa da ciwonta fiye da yadda ita take damuwa da kan nata.
Sannu kawai yake jera mata,tayi tayi ka yasha kunun yace ta maida fridge.
Baa rufa awa ba doctor mubeena ta iso da kayan aikinta,kai tsaye suka wuce dan qaramin dakin daya zuba qananun kayan aiki a ciki saboda lafiyar iyalin gidan.
Shi da ita duka idanu suka zuba mata sanda take duba gwajin data mata saboda ganin murmushi yana fita kan fuskarta.
"Mr and mrs jadda......congratulations,madam nada juna biyu". Banda yasan doctor mubeena na tsananin girmamashi da sai yace tana wasa da hankalinsa ne,saidai duk da haka sai daya ce.
"Say it again please".
"I said madam nada juna biyu......she's pregnant". Suratul ikhlas kawai ya hau karantawa qafa uku,daga nan ya miqe ya sunkuci matarsa,daukan data saka Dr mubeena soma hada ya nata yan nata ta basu waje,saidai tana iya hangen tsoro sosai fuskar sabreen.
Abinda kawai yake yawo a kanta shine watansu fauzan hudu,cikin week dinma duka duka aka fara koya musu zama......likita yace aqalla tayi shekara daya so samu har biyu bata dauki wani cikin ba saboda ta warke yadda ya kamata,yanzu kuma dr mubeena na gaya mata juna biyu ne da ita?.
Cikin qasa da mintuna biyar dukka wannan tsoron yabi ruwa,cikin daqiqa kadan komai ya kwaranye daga zuciyarta. Yadda idanun fu'ad ke fidda qwallar farinciki......yadda bakinsa ya gaza hutawa dayi mata addu'ar
"Ke 'yar aljanna ce in sha Allahu sabrrrr.......ke alkhairi ce sabrrrr......don Alla ki gayamin me kike da burin mallaka a rayuwarki bayan gidan marayu da gajiyayyu da tallafawa marayu?". Kai ta girgiza a hankali,lallai ta jahilci irin tsananin son da fu'ad yakewa haihuwa.
"Babu.....babu muffin,iya wannan qaunar da soyayyar da wadatar......iya wannan shauqin na samun iri daga jikina ya isheni farinciki har qarshen rayuwata". Ta furta maganar da dukka zuciyarta tana tuna wata mata da mijinta yayi mata duka ya watsota waje ya kuma saketa dukka a iqirarinsa na ta fiya haihuwa......da an tabata sai ciki.....dukka ubangiji ita bai jarabceta da wannan ba?.
Wani irin dare ne da bacci ya gagari idanun fu'ad,yayi sallah yayi addu'a har baisan iyaka ba. Itama da take kwance lamo kawai tayi,zuciyarta na sake cika da mamakin yadda yake tsananin son haihuwa,saita samu kanta da maimaita.
"Alhamdulillah......alhamdulillah" Har sau babu adadi.
Chapter 205 · 0% Book details