Sashe 210
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani abu data lura dashi yana da bala'in son tara yara,Allah ya taimaketa ya dinga bata bibbiyu har sau uku bayan ukun farko da tayi,iffa ce kawai tazo ita daya abinta,shi yasa idan suka tashi tsokanarta suke cemata me baqinjini,ita ba wanda ya rakota,su kuwa saida suka rako juna,duk da cewa a zahiri kusan farinjininta daban yake,kowa yasan wannan,farinjinin diya mace cikin yara maza. Shurun da tayi ya sanyashi satar kallonta kadan sannan ya kauda kai,bayason damuwa a tare da ita sam sam,don ta gama yi masa komai a rayuwa. "Bani labari.....How'd the trip go?". Numfashi ta sauke tana son wadata fuskarta da murmushi,saidai kafin tace komai ya sake magana. "Banga mamana bafa.....a ina kika barta?" "Tana hannun Nan najma(kaman yadda iffa din take kiranta)" Kai ya gyada "I missed her so much......da safen nan abinci sam bayamin dadi idan na kalli gurin xamanta naga bata nan". Baki Sabreen ta tura tana bata fuska. "I don't know me yasa kakeson min kishiya da iffa ne.......zan bayar da ita fa?". Ido ya waro kaman zai saki steering motar yana dubanta. " What?,yarona ko daya bazan iya badawa ba koda cikin gari ne dani......in fact ma ni koda mutuwa nayi ban yarda a rabamin yara ba bare ina raye". "Mu ajiye batun mutuwar nan hamma....." Ta fada tana maida aljihun motar data bude ta dauko mint sweet ta saka a bakinta. "Komai ya tafi daidai hamma......kuma dukka lambobin yabo dana karramawar da suka bayar naka ne....kaine ka cancancesu......ni 'yar tayi ce,Allah yakai kadan kabarin abba.....sun saka kudade masu yawa a asusun gidan,duk da nace bamu da buqatar wannan,amma sunce zasuyi don neman lada,sannan cikin daliban da muke yayewa duk shekara,a dinga ware mutum goma,maza biyar mata biyar yearly zasu dauki nauyin karatunsu har zuwa degree,har masters ma idan suna buqata har sama da hakan". Kai yake jinjinawa,ya jima yana ayyukan lada dana alkhairi kala daban daban,amma wannan din yafi kowanne yi masa dadi da qara masa walwala da nishadi. Uwa uba kuma wani abu daya lura dashi,tun daya sanda gidan ya fara aiki dukiyarsa kaman amai take,wani irin mahaukacin hauhawa takeyi,wani irin bangajejen budi yake qara samu da shi kansa kai tsaye yanzun bazaice ga adadin abinda ya mallaka ba. Ci gaba sukayi da tattaunawa shi da ita da wani irin yanayi da zai gaya maka zallar soyayya da tausasawa da jin qaine ke wanzuwa tsakanin ruhi da zukatan wadannan masoyan. Suna isa ya karbi mamarshi ameenatu iffa,don ta farka a sannan. Ita dinma da gudu ta nufoshi tana fadin. "Miss you abbee...." "Mamana.....My incomparable mother.....a mother without equal" Ya dagata yana juyata abinsa,ba ruwansu shi da ita da al'ummar dake farfajiyar gidan,wadanda kusan dukansu sun fito ne saboda tarbar Sabreen din,wanda wasu lokuta suke mata title da THE MISTRESS OF THE VILLA. K'ananun shekaru gareta amma ta zama babbar qarfi da yaji cikin gidan,duk da ta tasamma shekaru arba'in daidai a duniya......amma tsananin kula da kai da gyara jiki da kuma shan natural abubuwan gyara ga diya mace ya sanya zaka yita daukanta a shakarunta ashirin da biyar ko da takwas take. Bugu da qari idan ka kwatantata da su anni da suka kasance manya a gidan,ba laifi idan ka kirata da yarinya. Kusan duk wani dawainiya da matsaloli da zaa kaiwa annin ta hana isarsu Gareta,ballantana maamah da ba cikakkiyar lafiya gareta ba,yau da lafiya gobe babu. Girman ya karbeta da kyau,yadda ta tafi dashi kuma cikin adalci da mutuntawa ya sanya kowa yake biye da ita da tarin qauna. Ko a wajen bata wuce ba sai data duba lafiyar duka ma'aikatan,fuad na biye da ita dauke iffa yanata shan surutu,daya hannun nasa kuma handbag dinta ce. Wannan dabi'ar tasa kowa dake jadda villa ya santa,tun suna kunya har ya zame musu jiki. Ko zaman kwana uku kawai kayi cikin villa din zakasan cewa akwai wata mahaukiyar soyayya irin ta hanta da jini a tsakaninsu. Tare suka jera cikin gidan bayan gamawa da ma'aikatan yana tsokanarta. "Hajjaju da kanta......yau masu gidan sun dawo kowa ya shiga saitinsa" Yayi maganar yana maqalewa a bayan fuskar iffa yana mata gwalo. Murmushi ta saki tana mintsinar hannunsa. "Ka daina mantawa fa da cewa yanxun baban samari ne kai.....in suka ganka kana tsokanar ummensu tabbas xakaji kunya". "Suma sun jima da sanin cewa ba'a raba hanta da jini......yadda nakeso susan zallar madarar soyayyar dake tsakanin abbeensu da ummeensu alhamdlh sun fahimta" Kai ta gyada,ita kanta tasan da hakan,hakan kuma ya taimaka sosai wajen bawa yaran qwaqwalwa da rayuwa me kyau,hakanan kuma suma sai suka tashi da qaunar junansu sosai. "Banga kowa ba cikin dukka yaran gidan nan ba.....sauban dai ancemin yana gurin anni". "Kin rigani fade ne......duk da kaman su nadra sun tafi siyayya dasu sahl samr suhail duka sun bisu". Murmushi ta danyi tana jinjina kai,tana sake jin rayuwarta tayi mata dadi idan ta tuna yau zata aurar da nadra da haneefa gaba daya,ragowar abinda ya rage mata kenan take addu'ar Allah yakai mata ranta. "Kaman yaushe zaku fara bikin nan?" Fuad ya tambaya sanda suke dab da isa sassan maamah. Umarnin anni ne,duk sanda suka dawo daga wata tafiya ko kuma suka tashi da safe zasu shiga su gaisa ita ta yafe zuwan farko,su fara zuwa wajen maamah tukunna su dubata. "Don itace me lalura,tafi buqatarku a akaina,ni da lafiyata har yanzu da sauran qarfina.....kuma alhamdulillah zan iya yiwa kaina komai" "Hamma abubuwa kadan zasuyi fa......zasuyi the day of qur'an da dalibai da malamansu na mu'assas.......then zasuyi bridal shower.......sai waleema da anni ta shirya shikenan,dukkansu suda mazan basason dogon biki". Kai ya jinjina,yana jinjinawa yaran,suna da wani irin hankali da nutsuwa na daban,komai nasu moderate ne,shi yasa ya yuwa rayuwarsu wani tanadi na musamman da ba wanda ya sani sai ranar da aka daurawa kowaccensu aure. "Ma sha Allah.......Allahumma barik" Ya furta suna sanya qafa makekiyar balcony din da zata sadaka da falon. Idanunta akan tashar saudi sunnah da suke hasko masallacin ma'aiki tare da karanto hadisansa masu tsarki girma da alfarma,zuciyarta takejin tana tsananin kewa da qishirwan gurin,kaman bata taba zuwa ba tunda take a rayuwarta. Sukanje tana bin jama'ar gidan da suke da kebantattun lokuta da jirgin jadda majesty jet yake jigilar kowacce halitta dake birnin jadda villa din bayan kowanne hutun makaranta da za'ayiwa yaran. Wannan damar suke amfani da ita suke ziyartar fauzan fawad da fawwaz dake karatunsu a madeena king Abdul'azee international School wadda suka kammala kuma za'ayi bikin yayesu sati me zuwa. Kaman saukar nannauyan dutse daga qirjinta haka taji sanda sukayi sallama a tare,ta motsa bakinta tana amsa musu da sautin da ba'a fahimtar abinda take fada sosai sai wadanda suke da matuqar ganewa kaman sabreen din,don shi kansa fu'ad din sometimes sabreen ce ke gaya masa abinda tace din. Idanunta ta janye a kansu tana maidawa kan yarinya ta biyu da Allah ya jarabceta da masifar son yarinyar......yarinyar da duk gidan kowa qaunarta yakeyi saboda kasancewarta jika diya mace qwaya daya kaf cikin jikokin gidan ashirin da wani abu. Ameenatu iffa ta sakarwa maamahn murmushi tana zamewa daga jikin fu'ad ta tsallako da gudu tayo wajen maamah. "Har yanzu baki tashi kin fara tafiya ba?,kikace zaki fara tafiya kafin mu dawo?" Ta fadi cike da quruciya cikin maganarta. Murmushi kawai maamah din ta sake,yarinyar ta tattaka qafafun maamahn ta haye cinyarta tayi dare dare tana bata labarin su hamma fauzan suna gaisheta. Tayi kewar 'yan ukun sosai,su na dabanne a zuciyarta,duk da gidan cike yake da tagwaye amma nasu qaunar daban yake. Har yanzu suna iya kira video call su dukka ukun su sakata a gaba da hirarraki har sai sun sakata dariya sanna,har zaman jiran kiransu takeyi kulli yaumin,koda basu kira ba zata sanya a kira mata su. "Barka da warhaka maamah.......ya qarfin jikin?". " Alhamdulillah " Yau sautin amsa gaisuwar sabreen din ya fita da kyau har sai da sabreen ta daga kai ta kalleta a mamakance. "Ya taro?" Ta fada da sarqaqqen harshenta. "Alhamdulillah.....mun kammala cikin nasara" "Allah ya taimaka" Ta sake fada da qyar tana fuffusgo kalmar. "Ameen" Sabreen ta amsa tana sadda kanta tana tattalin hawayen farincikin dake son ballewa cikin idanunta. Kamar yadda maamah ta zata din,sabreen din saidata tabbatar komai yana tafiya daidai a sashen,daga masu kula da ita har kalar abincin da ake bata sannan suka wuce sassan anni. Suna zaune da mutuminta sauban a courtyard din da ya zamana shuru saboda fitar duka yaran da rashin motsinsu wanda anni batasan me ya kawo hakan ba. Murmushi ya sakarwa ummeen nasa da abbeen nasa,ya zare headphones din ya ajiye ya tako da nutsuwar nan tasa yana fadin. "Sannu ummee.....abbee sannu" Ya fada yana kamo iffa wadda tayi tsalle ta daneshi. Akwai sabo sosai tsakaninsu,don wani irin sassanyan kulawa yake bata ta hankali. "Anata karatun sauban?" Sabreen ta fadi bayan ya gama gaidasu,fu'ad ya dora hannunsa saman kansa. Yana jin yaron sosai a jininsa saboda yadda yake da maitar karatu,yana da buri sosai akanshi,kowanne yaro nashi yana bashi karatu daidai da abinda ya fuskanci yafi karkata akai.....kaman yadda ta fannin neman kudi ma yayi alqawarin zaibar kowa yayi kalar neman kudin da yafi sha'awa muddin bai sabawa addini ba. Da wani irin alfahari qauna da soyayya anni ke kallonsu a gabanta,har suka gama gaisawa suka fara taba hira "Kije ki huta takwara,anjima akwai general dinner a babban dining room na gidan nan,sai a qarasa hirar a can" Murmushi tayi a kunyace sannan ta miqe,fu'ad ya tayata da jakar suka rankaya dukkaninsu wannan karon har sauban suka fice. Tun kafin sukai ga bude qofar sassan taga kaman parlor din farko yayi duhu da yawa,bangaren sitting room ba ba wani wadataccen haske. Tanata so tayi magana amma kuma Allah bai bata iko ba har sai da suka shiga parlor din. Duduun ba wani haske,abun da ya basu mamaki kenan daga ita har fu'ad din,ta bude baki zatayi magana fitilan farko ta kama. Harafin H ne tafkeke,mamaki ya cikata,zatayi magana A ta bayyana,da wani irin sauri P ta bayyana a jejjere ragowar suka kama suka bada cikakken sunan HAPPY WEDDING ANNIVERSARY. Baki sake take kallon harufan,ta juya a hankali da zummar yiwa fu'ad magana ko yaga abinda take gani,sai gaba daya wutar falon ta kunnu hade da wasu abubuwa masu walwali da suka soma bude kansu da kansu daga jikin