Sashe 169
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga samanta tana iya hangen yadda duk wani shige da fice yake gudana cikin gidan hamza kibiya. Wani ajiyayyen qullutun baqinciki ne yake tsaye a wuyanta,shi bai fita ba shi bai sauka ba. Idan akace mata a baya nasararta zatazo da irin wannan salon tsaf zata qaryata......a irin wannan yanayin zata iya cewa bikin d'anta akeyi.......amma koshi yaron nata bata samu martabar ganinsa ba bare ta shiga lamarin bikin,balle kuma ta samu girma da daraja irin na kowacce uwa. Agogo ta kalla,tana jin ta matsu ta kuma qagu komai ya faru,tana jin a ranta afkuwar komai din shine zai bawa abinda ya tsaya mata a wuyan damar fadawa. Knocking akayi sannan aka turo qofar dakin. Bata damu ta waiwaya kota tambayi waye ba har zuwa sanda ta fara magana. "Maamah ga abincinki fa,tun na safe bakici ba.....na rana ma haka,ga na dare a hanya,kuma likita yace ki dinga kula da abinci ko don yanayin ciwon...." "Ciwon ubanki?.....nace ciwon ubanki?". Ta fadi tana katse laila da dukka tashin hankalinta ya tattaru ga ganin alamun maamah din tana cikin damuwa,tashin hankalin da takeji tana jin yafi wanda maamah dimma ke ciki. "Maamah kiyi a hankali ki daina fushinnan ko don lafiyark......". "Waini sa'arki ce?,to kiji na gaya miki na rantse da Allah kika qara Dangantani da wani cutar hawan jini saikin gwammace uwarki hajja bata haifoki na......idanma qullawa kukayi don ku cuceni ku kasheni saboda ba idon 'ya'yana ko to?,to kunyi qarya kun kwana da yunwa,ni mariya warki ce daidai qugun kowa.....ni mariya kuma ni kad'aice gayya......fita kiban guri" Ta dakawa laila tsawa tsawar da har saidata zabura. "Allah ya baki haquri" Ta fada ta juya tana fita a dakin kaman zata kifa. Fitar laila sai ya zama kamar ta fita da iskar da take shaqa ne,take taji iska tana mata kadan,wuyanta ya soma riqewa iskar bata samun daman isa ga hunhunta. A daddafe ta samu waje ta zauna tana qara gudun fanka da Ac din dakin,wani irin haki yana sarqeta. Likitan ya gaya mata,kada ta yarda ta fadi muddin irin hakan ya sameta tana a tsaye,idan ba haka ba komai zai iya faruwa. Ta kusa mintuna talatin a haka kafin taji a hankali numfashinta yana daidaita har ya koma normal. Wayarta ta jawo,ta kira number wayar da take sanya ran shigowar kiranta tun dazu. "Baki da damuwa.....muna ankare da kowa da kuma komai.....ki jira jin sakamako daga yanzu zuwa gobe da safe".. "Godiya nake" Ta fadi tana ajiye wayar tana kuma sake jin relief sosai a ranta. Cikin wani irin mugun matakan tsaro jirginsu ya sauka,yayin da baqaqen motocin dake dauke da tambarin JADDA kimanin ashirin sukayi convoy cikin wani irin tsari me daukan hankali da kuma matakan tsaro sosai bisa umarnin fu'ad. Lafiya lau suka qaraso unguwar,suka kuma jera kansu zuwa kyakkyawa kuma makadediyar harabar mansion House din alhj hamza kibiya. Duk wani dake da jibi da ahalin alhj hamza kibiyan yayi tattaki ya fito daga cikin gidan,yayi tsaye a farfajiyar saboda girmamawa ga fannah,wadda aka fito da ita nannade cikin wata lafiyayyar Cotton lafaya butter colour da ratsin maroon. Yana daga cikin motar amma yana iya ganin komai,yabi kowa da ido da yadda abun ke kasancewa,sai yaji wani abu yana taso masa,don haka ya maida idanunsa ya lumshe. Lallai babu wani babban arziqi a duniya irin uwa ta gari......babu wani babban jin dadin rayuwa irin samun uwa ta gari.......alhmdlh yana godiya ga Allah a bisa dukkan ni'imomin da yayi masa,kuma ya karba cewa tasa qaddarar tana kan MAHAIFIYARSA tasa jarrabawar tana kan UWA da Allah ya bashi. Amna dake nade cikin tata lafayar sai wani irin farinciki taji yana lullubeta,tana jin kamar suna dab da gina wani babban ahali ne,yau BB farouq dinta.....ya saddik,ya musaddiq da hammanta dukkaninsu yana da matar aure,wadannan matan kuma kowacce ana sanya ran zata basu baby,babies din da zasu taru su zame musu wata tawaga kuma family na musamman. Kasa jira tayi a qaraso da fannah,saita taka da dan hanzarinta tana cimmata ta riqe hannunta,abinda yasa matar dake riqe da fannah din sakin hannunta taja baya,wannan ya bawa amna daman magana da ita qasa qasa. "Welcome to alhj hamza family,welcome to jadda family adda fannah......bansan ya kuke cewa adda da kanuri ba.....anyway muna miki maraba". "Na gode" Siririyar muryar fannah ta fita wanda ta tabbatar ita daya ta jita. Cikin girma da martaba dangin anni dana abba suka amshi fannah aka qarasa ciki da ita,bayan anyi addu'a an kuma bawa su anni amanarta,sai annin ta sanya aka ware daki daban aka bawa fannah din ta huta suci abinci sannan sai a wuce da ita gidanta,hakanan danginta suma aka basu wani dakin daban. Sai data tabbatar babu kowa a dakin sannan ta yaye lafayar dake kanta. Amna da huda ke dakin,hudar da sam ta kasa sakewa,ta hana kowa ma ya ganta throughout saboda surukuta da takeyi da dangin anni. Musayar murmushi sukayi,amna ta nuna huda. "Wannan itace huda.....qanwar adda sabreen,matar ya saddiq" Lokaci daya huda ta yiwa fannah,ta miqa mata hannu sukayi musabaha. Ita da amna sai take jinsu karon farko kaman qannenta,don ta tabbatar ta girme musu,saidai ba wani da yawa bane. Qaramar walima akayi cikin gidan,baqi sukaci suka qoshi suka huta,sannan anni ta bawa fannah kyauta irinta surukuwa kaman yadda ta yiwa sabreen. *_ME FARUWA!_* Tun bakwai da rabi aka soma shirye shiryen qarasawa da fannah gidanta. Musaddiq da saddiq ne akan komai na game da shirya motocin da za'a dauketa a qarasa da ita ainihin gidanta dake maqociyar unguwarsu. Tunda aka fara jera motocin daga harabar gidan zuwa qofar gidan amna ta kasa zaune ta kasa tsaye. Tana bala'in son zuwa gidan ya farouq,wannan yana daya daga cikin mafarkanta tun kafin tasan rayuwa zata juya lokutan aurensu guri guda,tun kafin ta taba tunanin zata kasance qarqashin igiyar auren yaa musaddiq a wannan lokacin. Yadda kowa ya shirya haka ta shirya,tanason ta tambayi ya musaddiq ko shi ya dauki mota subi ayarin kai amare,a qalla tana tunanin bazai hanata ba,tunda zai wahala idan ta shiga nata gidan ya barta fita da wurwuri,don musaddiq din wani irin tsaro ne dashi tun wancan lokacin ballantana yanzu data zama mallakinsa. Zaune tayi tana gwada wayarsa,sai data kirashi a qalla sau hudu sannan ya daga. "Ya akayi baby doll?" Cikin shagwabar nan tata ta narkar da kai. "Besty.......gidan amarya please,don Allah muje" Idanunsa ya waro waje kaman tana gabansa. "What?.....aah karmu fara haka dake babe.....zakije amma bayan munyi wasu watanni" . Kukan shagwaba ta sakar masa wadda ta qarasa susutashi,da qyar da ban baki ta shawo kansa. "Amma kinsan anni zatayi fada ko?". "Karka gaya mata please,nayi alqawari muna zuwa zamu dawo". Shuru ya danyi,bayan wasu sakanni yace. "Ban miki alqawari ba gaskiya babe... Kema amaryarce kaman kowa,kodon kinga ban tada rigima a kaiki yau ba?" "Am sorry besty....don Allah" "Nace banyi alqawari ba,but ki jirani idan hali ya yiwu zan miki magana saiki fito" A haka suka rabu da musaddiq,duk sai taji ranta ya jagule,tunda taji ya fadi hakan probability na rashin zuwanta yafi na zuwan nata yawa,saita buga tagumi tana zaman jiran tsammani,har sanda aka shigo aka fita da fannah alamun tafiya zasuyi. Kasa zama tayi,ta lafe a farfajiyar gidan tana ganin yadda motocin suke tashi suna ficewa. Ta duba agogo,ta tabbatar tunda har musaddiq yakai wannan lokacin baice ta fito ba to tayi loosing chance dinta,tabbas bazai kaita ba. Hawaye taji ya silmiyo mata,daya daga cikin talalar aure kenan,idan dane anni kawai zata gayawa ta fice abinta. Ko a yanzun ma ji tayi ba zata iya haqura ba,tunda duka motocin gidansu ne zata iya basaja ta bisu,idan an tashi dawowa da dangin amarya ta biyosu ba lallai a gane ta fita harta dawo din,don haka ta silale a hankali tabi ta jikin motar dake fita daga gidan ta saje a jikinta suka fice tare. Sai data fita din tahau raba ido,ba wata mota a wajen duka sun dauki hanya wata nabin wata,caraf idanunta suka sauka kan wata baqa guda daya dake fake a gefe,sauri take kada musaddiq ya cimmata yace ta koma gida,don haka bata lura da number ba irin ta gidansu bane kawai ta doshi motar kai tsaye. Sosai abun ya musu dadi,ya kuma yi musu sauqi na ganin ta kawo kanta da kanta,sai ya bude motar kawai yana jiran isowarta,wanda tana isowar ta bude bakinta da zummar tambaya sai kawai ji tayi luuuu an jata cikin motar an maida qofa an rufe. A gaggauce ta bude idonta tana son gani ko musaddiq ne yake mata wasa?,saidai fuskar data gani din a gabanta ba wata alaqa ta kusa ko ta nesa da imani a tare dashi bare a alaqantashi da sunan musaddiq ma.....kafin kuma ta sake tantance komai,sun badeta da wani abu da ya sanyata atishawa,cikin qasa da second biyu ta daina fahimtar komai. _masu karatu kuyi haquri nayi baqi ne yau din,mu tara gobe in sha Allah......sai ince kowa ya shirya,ranar da kuke jira ce ta tunkaro mu_ Sonso *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ 141 *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET........siya ko saidawa,reposting ko sari_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX Tsararren gida ne da akayi masa wani irin qawataccen gini mai dauka hankali. Tun daga qofar gidan zuwa cikin gidan dole ya burge me kallo saboda yadda komai yake a tsare da wani irin yanayi me jan hankali. Komai favourite na farouq aka saka,fu'ad yayi masa ba zata kaman yadda shima yayi masa. A hankali ta rufe turaren data gama fesa masa tana dubansa,yayi masifar kyau cikin wani lallausan yadin vicuna da aka yiwa riga da wando da wata 'yar sama me kama da alkyabba. Tsadajjen dinkin hannu da aka shiryashi da zare me daraja. "Kayi kyau muffin" Sabreen ta fada tana lumshe idonta gami da budesu akan fuskarsa. Hannunta ya riqo a tausashe yayi kissing dinta "Soyayyarki ce ta saka my world.....but bakisan kin fini kyau ba?" Ido ta zaro waje kana ta saki dariya tana girgiza kai gami da ja baya "Zolayata kake muffin.....ta yaya haka zai kasance?,kar ka tsaida BB hamma......yau ranarsa ce aje a miqawa sister fannah shi" Murmushi ya subuce masa ya soma zura rufaffun takalmansa tana daga tsaye tana morewa kallon abinta. Sai ya fito fes kaman wani shaihin malami. Har bakin mota ta masa tattaki,bayan ta tabbatar an saka komai a motar