← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 215

Sashe 84

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gabansa tana qarewa kanta kallo. Ita kanta ta yaba da kanta ballantana wata halittar d'a namiji?. "Yadda bai sassautawa zuciyata ba bazan sassauta masa ba.......sai na tabbatar na zama cikakkiyar matarsa da shaidu na halas sannan zan barshi ya shaqi numfashi me kyau" Ta qarasa maganar tana daukan chewing gum ta jefa a bakinta tana duban qawartata "Sai na dawo?" Ido ta lumshe sannna ta budesu a kanta. "Inajin inama ace nice yau zan samu nasarar kasancewa da namiji irin muhammad jadda......koda bai aureni ba babbar nasara ce wannan a wajena......best wishes" Wani kallo fareeda ta watsa mata "To mayya........wata miyar ai sai a maqota,babban goro sai magogin qarfe kuma" Dariya ta sheqe da ita "Na sani qawata" Itama saita tayata tana ficewa zuciyarta fes yau din. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ Karo na uku ya sake daukan cup din yana kurban tataccen ruwan strawberry din da shine abu na farko daya soma zaba akai masa. Ya maida cup din ya ajiye yana zare belt din suspenders dinsa. Sosai gurin ya masa kyau ya kuma qawatar dashi,banda annin da suka baro a gida ita daya ba shakka ba abinda xai sakashi qin yanke hukuncin kwana a wajen,amma ko iya hakan ma nan da eleven yasan ya samu refreshment din da yakeso ai. Mamaki ya cikashi jin an murda qofar an kuma shigo,ya waiwaya yana tunanin saddiq ne ko musaddiq,saidai kuma fuskar daya gani tasha banban da fuskokinsu gaba daya. Da kanta ta fito don karbawa amna grilled fish dinta don girmamawa ga yarinyar yadda take kimantata da ganin girmanta,amnan tana da wani irin kirki da sauqin kan da yake bawa sabreen mamaki,don haka tace "Zauna addanki ne zata amso kifin nan da kiketa kwadayi". A gurin ta samu musaddiq shima zai karba nasa order din,wani tsari ne dasu akan grilled fish......zaka je wajen da kanka,zasu nuna maka inda kifayen ki ninqayarsu cikin ruwa ba tare da sanin kwanakinsu qayyadaddu bane,zaka nuna irin kifin da kakeso take a ciroshi a gasa maka a baka ka wuce. Kusan tare suka zaba aka kuma musu irin gashin da sukeso,musaddiq din ya miqa mata daya plate din hannunsa "Addanmu......taimaka ki miqawa hamma wannan please.....kunfi kusa da dakinsa....Allah yasa banyi laifi ba" Murmushi kawai tayi ta karba,tana mamakin yadda suke bata girma haka,bayan duk cikinsu idan ka dauke amna bata girmi kowa ba. Ason ranta tace ya taimaka mata ya qarasa masa dashi,to amma tana jin nauyin kasa masa alfarmar ko don yadda suke daukanta. A nutse take takawa tana duba dakin da take tunanin kamar ya shiga ciki. "Na gaya maka.....kana ganin kaman d wasa nake?......zanci gaba da kasancewa a kowanne taku naka......zan kasance cikin kowanne fitar numfashi da daqiqa naka.......makahon so nake maka.......i can't imagining yadda xan iya ci gaba da rayuwa babu kai". Tayi maganar tana karantar qwayar idanunsa. Tanaso ne komai ya kankama a jikinsa kafin takai ga cikar burinta.......tanason kowanne hankali yayi nesa da tunaninsa kafin ta aiwatar da komai. Wani qaqqarfan yanayi dake taso masa ya sanya ya kasa cewa komai. Kokawa kawai yakeyi da abinda yakeji din,yanason tabbatarwa da ba wannan qaqqarfan abun bane ke qoqarin motsawa?. Yana tsaka da wannan kokawar da duk wani control dake aiki a jikinsa ya tsinci fadowarta jikinsa,ta sanya dukka hannayenta ta masa wata irin bahaguwar runguma kaman zata shige cikinsa tana fadin. Sake kallon number dakin tayi da kyau,ta sake samun tabbacin shine,saita murza handle din tana murmushin hattararta da yadda ta iya gane dakin,ta tura qofan tana sanya qafafunta ciki. "I need you......i need you please jadda......kada ka juyawa zuciyar dake sonka baya.....ka bari na sauke maka abinda kakeji.......kaima kana cikin irin yana yina......na gani a qwayar idanunka" Kalaman da ta fara maraba dasu kenan kafin qwayoyin idanunta su sauka a kansu. Idan idanunta ba qarya sukayi mata ba fareeda khaleed mustapha ce cikin mummunar shiga.......dukka su biyun suna a tsaye,yayin data samu kyakkyawan maxauni a qirjinsa saboda tsahonsa daya shanye nata. "La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimeen" Ta fusga daga qasan zuciyarta zuwa labbanta,saidai sautin baikai ga fita a sarari ba ta samu ta janye qafafunta ta koma da baya. Dukka jikinta bari yakeyi,abinda ya sanya plates din guda biyu duka suka kife ruf a qasa. "Sorry madam" Wata murya ta tsarga saman kanta,kafin ta dago ma har ya tsuguna yana kwashe duka plates din. Baya taja k awai ta tsaya tana qoqarin maida numfashinta daidai,don bata da wani qarfi na kwashe barnar da tayi sam. "Relax Sabreen relax mana.....fareeda dince baki sani ba?,ko fareeda dince bakisan yana bibiya ba?,sau nawa kikaga kiranta a wayarshi da luluqin dare?,me kudi ne fa?,yana da kudin da zai iya gayyatar ko wacce mace ta debe masa kewa......that's why aure baya a gabansa......karki yaudari kanki sama da haka ma zaki iya gani...." "And then waye shi a gurinki da zaki rude har haka?" Wannan gigitacciyar tambayar ta fado mata,abinda ya sanyata gayyato duk wata nutsuwa dake kowacce kafa ta jikinta ta azawa ranta tana duban matashin daya miqe yana dubanta da plates din a hannunsa. Cikin harshen turanci ya fara mata magana "Sannu ko?,muje su canza miki wani kifin" Duk da ba'a hayyacinta take ba amma koda ta dubeshi da kyau sai taji a jikinta mutumim africa ne,duk kuwa da cewa shi din ba baqi bane. Duk wani zaren tunaninta ya gama kwancewa,don haka bata da wani zabi illa binsa ta karbowa Sabreen wani kifin,saboda bata da abinda zatace mata idan ta koma dakin haka. Tana biye dashi yana qoqarin janta da hira da mata tambayoyin da bama iya amsa masa takeyi ba saboda yadda zuciyarta ke tsananin gudu. Hannunsa daya ya sanya ya yakice fareedan gefe zuciyarsa tana wani irin mahaukacin bugu. Fushi da feelings gaba daya sun hadu suna neman sauya tsarin bugun zuciya dana numfashinsa. "Wacce irin dabba ce ke?,a hankalinki kike kuwa?" Ya fada da wata irin tsawa data kusa tarwatsa duk wani plan nata......amma data tuna wannan shine plan dinta na qarshe saita miqe da hanzari tana cewa "Bazan taba iya qyaleka ba,sonka mahadin bugun numfashina ne....ka soni please.....koda na iya yaun....." Bata samu damar qarasawa ba saboda wani bahagon mari daya dauketa dashi yana huci,sai gata qasa warwas ta zube bayan ta tuntsura ta dawo ta zauna. Huci yake fitarwa sosai yana jin yadda jikinsa ke sake rikicewa "Daga yau ya zama na farko kuma na qarshe da kika sake shiga hanyata ta kowacce fuska.....if not.....zan batar dake ne a banza......idiot kawai mara amfani!" Yana kaiwa nan ya miqa hannunsa ya dauki key din motarsa da wayar dake ajiye tare dashi guri daya,bai kuma tsaya sauraron kukan data saki tana kiran sunansa ba ya sanya kai ya fice. Yana ji a jikinsa ba daidai yake ba,hakanan baya jin zai qara koda minti guda cikin island din ba.......kaman yadda bazai iya tsaiwa nemansu farouq ba,haka ya nufi hanyar barin wajen wani irin fushi yana lasar zuciyarsa. Kaman cikin gizo idanunsa suka sauka a kanta. Tana tsaye suna facing juna ita dashi. Ya miqa mata kifin da aka nadeshi cikin aluminum foil yana sakar mata murmushi. Bata da wani zabi da ya wuce maida masa martani duk da irin abinda takeji qasan ranta. "Thank you" Ta fadi tana juyawa. Taku uku kacal tayi ta tsinceshi a gabanta babu zato ba tsammani. Wani irin zazzafan kallo take tsinta cikin idanunsa.....wani kakkaifan kallo da kaifinsa ya zarce na takobi.....kallon da tsananin bacin rai yake da matuqar tasiri a cikinsa. Kallo ne daya tabata har cikin b'argonta ya aika saqo sassan jikinta,saidai girma da nauyin abinda ta gani qasa da minti biyar cikin dakinsa ya dakushe kowacce razana tata. Nata fushin ne yake tasowa wanda a dazu tsananin razana da tayi ya cakude da firgici ta rasa ainihin abinda takeji sai yanzu. Yatsansa ya daga yana nuna fuskarta,sai kuma ya sanya hannusa ya damqi nata hannun ba tare daya damu da plate din dake hannunta ba,ya finciketa da wata irin sauri daya qure yanayin adadin tafiyarta ta kasa daidaita tafiyarta da tasa,sai hadawa da tayi da sassarfa. Qoqari taketa yi ta qwace hannunta amma ko cikakken motsi ta kasa yi a hannunsa,kaman yadda bai saketa ba haka bai waiwayeta ba,har sai daya dangana da motar. Seat din gaba ya bude ya kuma sanyata a ciki ya rufe,sannan ya zagaya seat din driver ya shiga,ya tayar da motar d wani dan irin zafin nama,yayu reverse ya fusgeta da wani irin gudu na tashin hankali. Dimaucewa tayi gaba daya har sai data sanya tafukan hannayenta ta rufe dukka kunnuwanta. Ta kasa kallon titi ko sau daya saboda yadda jikinta yake gaya mata irin gudun da yakeyi da ita. Tsahon tafiyar mintina ashirin da sukayi bakajin komai sai qarar iska dake son kutse ta cikin window din motar. Birkin da yaja da wani irin qarfi shi ya kusa sakata tintsurowa daga nata seat din. Murfin ya bude ya fita.....ta dauka a nan abun zai tsaya amma sai taga yana zagayowa inda take zaune. Sake bude motar yayi,ya kuma cafko hannunta kamar dazu ya fito da ita,ba tare daya tsaya kulle motar ba yaci gaba da janta har zuwa cikin gidan. Suka ratsa veranda suka wuce parlor suka tuqe zuwa ga bedroom dinsu. Sai da sukakai tsakiyar dakin yaja burki yana sakinta da qarfi,ta turje taja ta tsaya tana haki idanunta a kansa. Haki yake yana nunata da yatsa,yana son yayi magana amma yadda zuciyarsa ke bugawa a jejjere cikin son wuce qa'idarsa ya sanya ya gaza fadin komai. Kaman daga sama ya fusgo kalaman "Da kowanne namiji ma tsayawa kikeyi?,kowanne namiji ma fuska kike bashi?,wacce iri ce ke!,nace wacce iri ce ke?". Wani kalan tashin hankali taji yana sauke mata saman kai,ta runtse idanunta ta kuma budesu lokaci guda fushinta na qara hauhawa.....wanne irin dan rainin hankali ne shi haka?,ta gaji!,takai maqura! "Daga rana irin ta yau ba zaki sake fita daga nan ba har sai randa zamu bar qasar nan.......zakita zama a dakin nan naga ta yadda zakiga wani d'a namijin,waishin kowa ma burgeki yakeyi?,kowa ma son kudinsa kike?" "Eh......kaman yadda kowacce mace take burgeka!.....kaman yadda kake shirya plan ka kama masauki kawai don ka hadu da wata!.......idan kaga namiji yana burgeni to tabbas shi din ba ragowar wasu bane.......ba sauran wata 'ya mace bane......isashen namiji
Chapter 84 · 0% Book details